'52, Barcelona 0-0 Real Madrid
Madrid ta yi kokari ta kulle Messi a minti 45 na farko amma babu tabbas za ta ci gaba da garkame shi har karshen wasan.
Muna kawo maku wasan La Liga tsakanin Barcelona da Real Madrid kai-tsaye.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Madrid ta yi kokari ta kulle Messi a minti 45 na farko amma babu tabbas za ta ci gaba da garkame shi har karshen wasan.
Isco ya yi satar gida.
Ruwan shuta-shutai da Madrid ta yi wa Barcelona a minti 45 din farko, shi ne hari mafi yawa da Madrid ta kai a Camp Nou a kowacce gasa tun 2003/04
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Casemero ya bige Messi a tsakiyar fili bayan ya yanke shi. Wannan ba sabon abu ba ne indai Messi ne.
Madrid ta bugo kwanar farko a falle na biyu na wasan. Sai dai babu wani hadari ga Barca.
Lionel Messi Barcelona 26
Alfredo Di Stefano Real Madrid 18
Cristiano Ronaldo Real Madrid 18
Raul Real Madrid 15
Cesar Rodriguez Barcelona 14
Francisco Gento Real Madrid 14
Ferenc Puskas Real Madrid 14

Asalin hoton, BBC Sport
An fafata da kyau a wannan wasa kuma Real ta fi taka rawa - kamar a Bernebeu ake buga wasan.

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Barcelona Messi ne ya fi kowa cin kwallo a wasan El Clasico a La Liga, inda ya ci kwallo 18, ya kuma ci 26 a kowacce gasa.
Dan wasan Argentinan ya fi kafatanin 'yan wasan Madrid na yanzu cin kwallo a El Clasico da bal 26, sun ci guda 24.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Valverde ya sake dada kwallo kuma da kyar Stegen ya rarumo ta.
Me ya hana Alba cin wannan kwallon ne haka! Lionel Messi ya coga wata kwallo a sama amma Alba ya kasa amfana da ita - ya buga ta waje.
An bi wa Suarez katin gargadi bayan take kafar Casemiro ta baya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Barcelona ta buga kwana ta farko a wasan amma babu hadari ga 'yan bayan Madrid.
Akwai sababbin fuskoki a wannan karon da ake ganin hankali zai karkata a kansu kamar Frankie De Jong da Ansu Fati daga Barcelona.
Valverde da Rodrygo da suma za su fara buga wasan a yau.
Sabon yaro sabon hari Valverde, Madrid na da sabbin fiskoki a wasan.
Messi ya buga kwallo ta-ci a ragar Madrid, ba don Ramos ba da tuni 1-0.
Shi ne shot na farko ga Barca a wasan kuma na-ci.
Ya zuwa yanzu a Barcelona Ter Stegen da Piqué sun fi kowa kokari, daga ji ba sai an ce komi ba ga ma'abota kallon kwallo.
Madrid ta samu bugun kwana kuma ta bugo babu hadari ga Stegen.
Kwana ta hudu kenan da ta buga.