, Barcelona 0-0 Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Wasan hamayyar El Clasico ya tashi babu ci a filin wasa na Camp Nou a wasan La Liga mako na 10.
Wannan ne wasan Clasico na 90 da aka buga a Camp Nou kuma har yanzu kungiyoyin na kankankan a wurin nasara, inda kowaccensu ta ci wasa 72 a dukkanin wasannin Clasico na La Liga.
Real Madrid ce ta kankane minti 45 na farko sakamakon kokarin da 'yan wasan tsakiyarta Tony Kroos da Valverde suka yi.
Amma Barcelona ma ta kankane falle na biyu na wasan kafin Gareth Bale ya zira mata kwallo a raga, sai dai na'urar VAR ta ce Mendy ya yi satar gida, wanda shi ne ya bai wa Bale kwallon.
An bai wa Barcelona katin gargadi sau uku a minti 45 na farko, abin da ke nuna cewa ba ta ji dadin zagayen ba.
Ita kuwa Madrid an ba ta guda biyar kuma duka a minti 45 na biyu, abin da ke nuna ita ma ba ta ji dadin zagayen ba.
Da ma dai tun kafin wannan wasan kungiyoyin ne a saman teburi da maki 35 kowaccensu, amma Barca tana saman Madrid da tazarar kwallo biyu.
Haka abin zai ci gaba da kasancewa yayin da Barca za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ranar Asabar, Madrid kuma ta karbi bakuncin Athletic Club.
Sevilla ce ke biye masu a mataki na uku da maki 31, yayin da babbar abokiyar hamayyarsu Atletico Madrid ke mataki na biyar da maki 29.
