West Ham United 0-0 Tottenham
Kwana ta Farko ga Tottenham, sai dai bata shiga ba, gashi nan za a dauko ta biyu.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Kwana ta Farko ga Tottenham, sai dai bata shiga ba, gashi nan za a dauko ta biyu.
Duk da cewa ita ke waje, Amma Tottenham ta rike wasan kamar ita ce a gida.
Duka kungiyoyin na bukatar nasara a wasan, West Ham United da ke karbar bakunci wasanta 6 babu nasara.
Tottenham ta buga biyar babu nasara.
Idanu na kan sabon koci Jose Mourinho.
Alamu ba su nuna wani sauyi ba a wannan wasa duk da cewa Tottenham a waje take wasan.
Da alama Mourinho ya tsuma su domin ba zai so ya fara da rashin nasara ba.
Issa Diop ya doke Harry Kane kuma an ba shi katin gargadi, kuma shi ne na farko a wasan.
Tun a minti na uku da take wasa ne Harry Kane ya cilla kwallo a raga amma amma lafari ya ce an yi satar gida.
Da tuni Mourinho ya ci wasa a minti uku da fara wasa a cikin kusan shekara guda kenan.

Asalin hoton, Getty Images
Al’amura sun tabarbare wa Spurs, ta buga wasa biyar ba tare da nasara ba a Premier, wanda wannnan shi ne lokaci mafi muni da kungiyar ta shiga tun bayan wanda ta shiga a Disambar 2008 da kuma Junairun 2009.
Haka zalika ba ta samu nasara ba a wasanni 12 da ta buga a waje tun daga watan Junairun, kuma wasa 13 ta buga a waje kowanne ana sa mata kwallo a raga.
Ita ma West Ham ta yi wasa shida a Premier ba tare da nasara ba, an ci ta hudu ta yi canjaras biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Masu bibiyarmu barkanku da makon wasan Premier na 13.
Yau Mourinho ne ke jan ragamar Tottenham, saboda haka wasan na musamman ne.
Ku biyo mu.