Shefield United 0-0 Man United, Shefield United 0-0 Man United

Asalin hoton, BBC Sport
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

Asalin hoton, BBC Sport
Abokan aikinmu barkanku da yammacin Lahadi, barka da zuwa Shefield United vs Manchester United.
Shi ne wasa daya tilo da za a buga a yau na Premier mako na 13.
Buhari Muhammad Fagge ne da Umar Mikail ke cewa ku biyo mu.
Masu kallo da bibiyarmu nan muka kawo karshen sharhi da rahotannin na wasannin Asabar.
Mu hadu gobe domin kammala sauran wasannin mako na 13.
A duk kungiyoyin da suka buga wasa a gida a yau babu wadda ta ci wasa sai Manchester City kuma a gaban wadannan magoya bayan nata ta samu nasarar

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, ge
Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester City karon farko cikin wasa shida da ta buga a Premier ba tare da rashin nasara ba.
Man City ba ta yi kama da kungiyar da Pep Guadiola yake jagoranta ba a daren yau ganin irin yadda ta kasa shafa kwallo kamar yadda aka saba.
Kashi 46.74% da Man City ta samu na rike kwallo a yau shi ne mafi karanci da Guadiola ya taba samu a matsyain koci. Hakan yana nufin Chelsea ta nuna bajinta duk da cewa tawagar Lampard din ba ta iya farke kwallo ta biyu da Mahrez ya ci a minti na 37 ba.
Amma dai ko ba komai City ta farfado daga kashin da ta sha a hannun Liverpool mako biyu da suka gabata da ci 3-1.
Ngolo kante ne ya fara bude wasan da kwallonsa mai matukar kyau minti 21 da take wasa, kafin daga baya De Bruyne ya farke ta a minti na 29.
Raheem Sterling ya ci ta uku a minti na 93 amma na'urar VAR ta ce an yi satar gida kafin a saka kwallo a raga.
Sakamakon bai zo wa Chelsea da dadi ba domin kuwa ta koma matsayi na 4 a kasan City maimakon na uku da take kafin take wasan.
Ita kuwa Man City ta koma ta ukun da maki 28, maki tara kenan tsakaninta da Liverpool wadda ke saman teburi.
Maki uku masu mahimmanci ga City, nasara ce mai cike da alfahari.
Duk da Chelsea ta yi rashin nasara amma ta nuna jajurcewa da kuma kwarewa, shi yasa magoya bayan kungiyar ke murna da koci Frank Lampard
Wannan ita ce nitsattsiyar ramuwa da Manchester City ke dauka a kan Chelsea bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Liverpool kafin tafiya hutun wasanni.
City na nuna zafin rashin nasarar da ta yi tare da daukar matakin hucewa a kan Chelsea
Sai dai na'urar VAR ta ce an yi satar gida kafin a ci kwallon
Anya akwai Sterling a wannan wasan? minti 80 har yanzu banji an kira sunan shi ba.
Gabriel Jesus ya shigo a madadin Agüero
Jorginho ya fita Mount ya shiga Abraham ya fita Batshuayi ya shiga.
Chelsea na rike da ragamar wasan. amma ta kasa farke kwallonta.
Yau masu ci wa Chelsea kwallon sun buya daga Tammy Abraham har Pulisic.
da alamun Chelsea sai ta yi da gaske.
Silva ya fita yayin da Foden ya shigo don nuna bajintarsa.
David Silva a kasa da alama ba zai iya karasa wannan wasan ba saboda raunin da ya ji.
City na neman kari ido rufe. Riyad Mahrez ya kusa kara kwallo ta biyu a wasan.
Jorginho ya bige De Bruyne an bashi kati. amma ta wata fuskar ya yi abin da ya dace.
Emerson ya fita James ya shigo shima ya gwada sa'arsa.
Dama na ci gaba da zuwa a wasan, sai dai ba a san maci tuwo ba....