Messi ya kai mummunan hari, Liverpool 3-0 Barcelona
Messi ya kai mummunan hari, amma golan ya cire kwallon.
Labarai da sharhi game da yadda Liverpool da Barcelona ke karawa a wasan kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai a filin wasa na Anfield.
Messi ya kai mummunan hari, amma golan ya cire kwallon.
Messi ya buga kwallon amma ta daki bango kuma ta tafi kwana
Yanzu haka ana kunen doki tsakanin kungiyoyin biyu 3-3.
An bai wa Matip katingargadi bayan ya bige Messi a bakin ragarsu
Liverpool sun tasa Barcelona a gaba kuma komai yana taffiya a yadda suke sonsa.
Ana kan-kan-kan a yanzu
Wasa ya sake daukar sabon salo, inda Liverpool take ci gaba da danna Barcelona.

Asalin hoton, Getty Images
Wijnaldum ne ya yi tsallen gaske a tsakiyar yadi na 18 din Barcelona kuma kunduma ta cikin ragarsu.
Ya sake jefa kwallon ne a minti na 56.

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta sake jefa kwallo a ragar Barcelona a minti na 54.
Wijnaldum ne ya shauda ta ga Stegen, inda shi kuma ya kasa tare ta kuma afka cikin raga.
Van Dijk ya kai mumunan hari inda Stegen ya kama ta da kyar.
Sadio Mane ne ya take kwallon bayan an bugo masa ita. Sagio Roberto ne ya cilla kwallon bugun kwana
Liverpool ta samu bugun kwana, amma 'yan wasan bayan Barcelona sun cire kwallon.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, BBC Sport
Jordi Alba ya buga kwallo ga Alisson kuma ta tsallake shi, amma ya rarrafa ya kamo ta. Mummunan hari ne domin kuwa daga shi sai gola. Allah ya kare Liverpool kawai
Messi ya kusa cilla kwallo ragar Liverpool amma ta yi fadi ta kuma fita bugun gida ga Liverpool
An kara minti 4 a kan minti 45 na farkon wasa. Nan gaba kadsan kuma za tafi hutun rabin lokaci
Yadda wasan ke gudana cikin hotuna.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Shaqiri ya nemi Mane a cikin yadi na 18 din Barcelona amma mai same shi ba
Wannan yakin fa ba na wasa ba ne😲💪

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images