Liverpool ta yi kaca-kaca da Barcelona

Labarai da sharhi game da yadda Liverpool da Barcelona ke karawa a wasan kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai a filin wasa na Anfield.

Rahoto kai-tsaye

  1. Kocin Barcelona, Liverpool 4 - 0 Barcelona

    Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce "Ni ban san ta yadda wannan wasan zai shafi aikina ba, amma dole koci ya dauki alhalkin duk abin da ya faru.

    "Abin takaici ne a wurinmu, karo na biyu kenan da haka take faruwa da su".

  2. Sergio Busquets ya nemi afuwa, Liverpool 4 - 0 Barcelona

    dan wasan tsakiyar Barcelona Sergio Busquets ya nemi afuwar magoya bayansu.

    Ya ce: "Bayan abin da ya faru a Rome shekarar da ta gabata ta kuma faruwa. Abu ne mawuyaci a cinye ka bayan kana da nasarar 3-0. Muna bayar da hakuri."

  3. Rio Ferdinand ya ce, Liverpool 4 - 0 Barcelona

    Rio Ferdinand ya ce ba za ka taba samun irin wannan ba sai a kwallon kafa.

    Ya ce: "Ni dan wasan kungiyar adawa ne amma wajibi ne ka jinjina wa Liverpool da magoya bayansu a wannnan dare. Mun zo kallon Messi ne don ya yi nasara".

  4. Ta leko ta koma wa Barcelona, Liverpool 4 - 0 Barcelona

    Liverpool ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Barcelona 4-0 ranar Talata a Anfield.

    Liverpool ta ci kwallaye biyu ta hannun Divock Origi, sannan shima Georginio Wijnaldum ya ci biyu a karawar.

    Barcelona ce ta ci 3-0 a makon jiya a Nou Camp, amma Liverpool ta zare su sannan ta kara daya a raga, inda ta kai wasan karshe da kwallo 4-3.

    Liverpool tana ta biyu a teburin Premier, za ta buga wasan karshe da Wolverhampton ranar Lahadi.

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Barcelona ta leko ta koma, Liverpool 4 - 0 Barcelona

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  6. Liverpool kai wasan karshe, Liverpool 4-0 Barcelona

    Wayyo Allahna!!!!

    Wannan wane irin dare ne. Duniyar kwallon kafa na cikin wani yanayi na karya tarihi.

    Stats

    Asalin hoton, Rawar da kowacce kungiya ta taka

  7. An tashi wasa, Liverpool 4-0 Barcelona

    Yayin da ka tabbatar kana da lasisin zuwa birnin Madrid😛😝🕺🕺🕺

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Liverpool, Liverpool 4-0 Barcelona

    Liverpool na kan hanyarsu ta zuwa wasan karshe a karo na biyu a jere

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

  9. An kara minti biyar, Liverpool 4-0 Barcelona

    Alkalin wasa ya kara minti biyar kafin a tashi wasan. Idan aka tashi wasan a haka Liverpool ta yi nasara ke nan.

  10. Canji, Liverpool 4-0 Barcelona

    Daniel Sturidge ya shigo cikin fili, inda ya canji Shaqiri a minti na 90

  11. Barcelona sun matsa kora, Liverpool 4-0 Barcelona

    Barcelona sun matsa kora, amma masu tsaron bayan Liverpool sun kare gidansu.

  12. Van Dijk, Liverpool 4-0 Barcelona

    Van Dijk ya tare kwallo mai hadari a cikin yadi na 18 dinsu

  13. Saura minti hudu a tashi wasa, Liverpool 4-0 Barcelona

  14. Canji, Liverpool 4-0 Barcelona

    Gomez ya karbi Origi

    Wannan wani salo ne daga Klopp don tabbatar da nasarar da suke da ita a yanzu.

    Gomez dan wasan baya ne kuma ya canji na gaba, wanda shi ne ma ya ci kwallo 2 daga ciki

  15. Origi, Liverpool 4-0 Barcelona

    Origi ya fadi a tsakiyar fili yana karbar kulkawa.

    Saura minti 6 a tashi daga wasa.

  16. Goooo! Origiiiiiiiiiiiii

    Origi ya cilla kwallo ta 4 a ragar Barcelona.

    Dama taken Liverpool shi ne "ba za mu bar ka kai kadai ba"

  17. , Liverpool 3-0 Barcelona

    An bai wa Samedo katin gargadi

  18. , Liverpool 3-0 Barcelona

    Arthur ya canji Vidal a minti na 74.

    Vidal ya yi kokari sosai ganin yadda ya rika kaiwa da komowa a tsakiyar fili.

  19. , Liverpool 3-0 Barcelona

    Minti 73, kuma komai na tafiya yadda Liverpool ke bukatarsa.

  20. Liverpool, Liverpool 3-0 Barcelona

    Liverpool na kokarin zama kungiya ta 3 da ta ci wasa bayan an ci ta 3-0 a wasan farko a matakin kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Chamapions Leahgue da kum Europa.

    Muna jiran ganin karshen wannan dare mai cike da tarihi