Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Chelsea ta doke Manchester City

Chelsea ta doke Manchester City 2-0 a fafatawar da suka yi a gasar Firimiya mako na 16. Mun kawo Labarai da sharhi kai-tsaye game da dukkanin wasannin da aka fafata a ranar Asabar.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau

  1. Cystal Palace ta ci a London

    Crystal Palace kuwa tana kan gaba a wasan da kungiyar ta London ke yi da takwararta James Mcathur ne ya ci kwallon.

  2. Palace ta ci West Ham, West Ham 0-1 Crystal Palace

  3. GOAL, '13 Manchester United 1-0 Fulham

    Ashley Young ya ci wa Manchester United.

  4. Liverpool ta lallasa Bournemouth 4-0 a gida

    Wasa ya kare! Liverpool ta lallasa Bournemouth a gidanta da ci hudu da ba ko daya.

  5. Lallana ya ji ciwo, '92 Bournamouth 0-4 Liverpool

    Fuskar dan wasan Liverpool Adam Lallana yana cike da jini. Wani naushi ya samu bisa tsautsayi. An dan dakatar da wasa. Amma yanzu wasan ya cigaba.

  6. GOAL, '77 Bournamouth 0-4 Liverpool

    Salah ya ci wa Liverpool kwallo na uku a wannan wasan.

    Ya yi abin da turawan Ingilishi ke ce wa hat-trick (zura kwallaye uku a raga).

    Wasa kawai dan wasan Masar din yake yi da Bournemouth a yau. Ya yanke Steve Cook sannan ya kewaye Asmir Begovic, ya dawo sake yanke golwan Bournemoutha karo na biyu kuma zura kwallon a raga yayin da Nathan Ake ke kan layi ba tare da ya iya tare kwallon ba.

  7. GOAL, '68 Bournamouth 0-3 Liverpool

    Dan Bournemouth ( Steve Cook) ne ya ci kungiyarsa.

  8. Bournemouth ta sake dabara, '65 Bournamouth 0-2 Liverpool

    Ryan Fraser dai ya fara wasa ne daga baya a tsakiya. Amma yanzu ya koma ta hagu domin kai farmaki ta wurin James Milner wanda ke buga wasansa na 500, Junior Stanislas kuma ya koma dama daga hagu, yayin da David Brooks tsakiya ta gaba

  9. Salah bai murnar ba

    Mohammed Salah bai bayyana murnar cin kwaloo na biyun ba. Amma kwallayen nasa ka iya sa kungiyarsa ta yi nasara a wasan.

  10. Fulham ta isa Old Trafford

    A halin yanzu dai 'yan wasan Fulham sun isa Old Trafford don karawa da kungiyar Manchester United a wasan da za a fara karfe hudu agogon Najeriya da Nijar.

  11. GOAL, '48 Bournamouth 0-2 Liverpool

    A halin yanzu an dawo daga hutun rabin lokaci. Mohamed Salah Kuma ya kara wa Bournemouth.

  12. Ina jin dadin aiki a Man U - Mourinho

    Manajan Manchester United Jose Mourinho ya ce yana jin dadi kuma zai ci gaba da aikinsa, kamar yadda wakilinsa ya tabbatar.

    Mourinho na fuskantar barazanar kora daga aikin horar da Man U yayin da kulub din ke matsayi na takwas kuma tazarar maki takwas tsakani da matsayi na hudu a teburin Premier League.

    A watan Janairu Mourinho ya sabunta kwangilarsa a Old Trafford amma ana rade radin zai koma Real Madrid.

  13. An tafi hutun rabin lokaci, HT Bournamouth 0-1 Liverpool

    A halin yaznu dai an tafi hutun rabin lokaci kuma Liverpool tana gaba da Bournemouth da kwallo daya.

    Idanh aka tashi haka, Liverpool za ta haye saman teburin gasar Firimiya.

  14. Sala ya ci kwallye 40 a gasar Firimiya

    A halin yanzu kwallayen da Mohamed Salah ya ci a gasar Firimiya sun kai 40.

  15. Liverpool ta haye teburi, '31 Bournamouth 0-1 Liverpool

    A halin da ake ciki yanzu dai Liverpool ta haye saman teburin gasar Firimiya.

  16. Man City za ta ci gaba da buga Champions League

    Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ya samu tabbaci daga shugabbin kulub din cewa ba za a haramta masu buga gasar zakarun turai ba saboda saba dokar takaita sayen yan wasa.

  17. GOAL, '25 Bournamouth 0-1 Liverpool

    Mohamed Salah ne ya ci wa Liverpool!

  18. Bournemouth ta fara mayar da martani, '22 Bournamouth 0-0 Liverpool

    Liverpool ta dai kai wasu hare-hare daga farko, amma Bournemouth ma ta fara mayar da martani lamarin da ya sa wasan ke zafi.

    Liverpool za ta iya dare wa tebur idan ta yi nasara kafin Man City ta fafata da Chelsea a Stamford Bridge

  19. Bournemouth ta sami katin gargadi biyu, '18 Bournamouth 0-0 Liverpool

    Kungiyar Bournemouth ta sami katin gargadi biyu minti 16 da fara wasa.

  20. Ga 'yan wasan Bournemouth

    Kalli 'yan wasan da ke yi wa Bournemouth wasa a yau.