Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kofin Duniya: Yadda Croatia ta doke Najeriya

Najeriya ta sha kashi a fafatawarta da Croatia a rukuninsu na D a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Yanzu kalubale ya fi yawa kan Najeriya, Croatia 1-0 Najeriya

    Idan Najeriya ta bari aka tashi a haka, za ta kasance ta karshe a rukunin D, bayan Iceland ta rike Argentina 1-1

  2. Moses ya nemi fanareti, Croatia 1-0 Najeriya

    Moses ya fadi a gidan Croatia bayan ya samu kwallo a kafar Mikel amma alkali ya hana fanareti

  3. Najeriya ta yi canji, Croatia 1-0 Najeriya

    Musa ya karbi Iwobi

  4. Croatia ta yi canji, Croatia 1-0 Najeriya

    Brozovic ya karbi Kramaric

  5. Ighalo ya yi yunkuri, Croatia 1-0 Najeriya

    Ya sa kai amma golan Croatia ya kama

  6. Najeriya ta fi kai hari bayan hutun rabin lokaci, Croatia 1-0 Najeriya

  7. Najeriya na shirin canji, Croatia 1-0 Najeriya

    An tayar da Kelechi Iheanacho da Ahmed Musa suna motsa jiki

  8. Saura kiris Croatia ta kara, Croatia 1-0 Najeriya

  9. Rakitic ya nemi raga daga nesa, Croatia 1-0 Najeriya

    Amma kwallon ta bi saman ragar Najeriya

  10. Super Eagles sai sun yi da gaske, Croatia 1-0 Najeriya

    Sai Najeriya ta yi da gaske kafin haduwarta da Iceland da ta yi kunnen doki da Argentina.

  11. Moses ya kai kora, Croatia 1-0 Najeriya

    Amma ya buga kwallon ta fita

  12. Najeriya sun samu kwana, Croatia 1-0 Najeriya

    Najeriya ta samu kwana uku

  13. An dawo, Croatia 1-0 Najeriya

    Croatia ta fi Najeriya taba kwallo

  14. Ko kun san cewa?, Croatia 1-0 Najeriya

    Nasarori biyar da Najeriya ta samu a wasanni 18 da ta buga a gasar cin kofin duniya, kasashen Turai ne ta doke. Najeriya ta doke Bulgaria 3-0, Girka 2-0 a 1994, Spain 3-2 da Bulgaria 1-0 a 1998, Sai Bosnia Herzegovina 1-0 a 2014. Ko a bana Super Eagles za su gagari Croatia?

  15. Yadda aka fafata a kafin rabin lokaci, Croatia 1-0 Najeriya

  16. An tafi hutun rabin lokaci, Croatia 1-0 Najeriya

  17. Mandzukic ya kai wa Najeriya hari, Croatia 1-0 Najeriya

    Kwallo ta taba Etebo ne ta shiga raga.

  18. Saura kiris Croatia ta kara, Croatia 1-0 Najeriya

    Kramaric ya nemi karawa Najeriya amma kwallon ta bi saman raga

  19. Yadda Najeriya ta ci kanta, Croatia 1-0 Najeriya

    Oghenekaro Etebo ya ci wa Croatia kwallo a ragar Najeriya.

  20. Etebo ya ci kansu, Croatia 1-0 Najeriya

    Dan wasan Najeriya Etebo ne ya ci kansu