Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai

Real Madrid ta yi nasarar lashe kofin Zakarun Turai karo na uku a jere bayan ta doke Liverpool ci 3-1 a wasan karshe da suka fafata a birnin Kiev na Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Ko ficewar Salah baraka ce ga Liverpool?, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Liverpool

    Asalin hoton, @Championsleague

    Liverpool

    Asalin hoton, @Championsleague

    Liverpool

    Asalin hoton, @Championsleague

  2. An sako Lallana, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Lallana ya canji Salah

  3. Salah ya ji rauni an fitar da shi, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Ya fita fili yana kuka

  4. Sau biyar Klopp na shan kashi a wasannin karshe

    Jurgen Klopp

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya sha kashi a wasannin karshe na muhimman gasa shida ciki har da wasan karshe na zakarun Turai biyu.

    A karon farko dai Klopp yana tare ne da Borussia Dortmund, a lokacin da suka sha kaye a hannun Bayern Munich a wasan karshe na gasar zakarun Turai ta shekarar 2013 da aka buga a filin wasa na Wembley, yayin da na biyun ya zo a lokacin da Liverpool ta sha kaye a hannun Sevilla a wasan karshe na gasar Europa.

    Idan Liverpool ta sha kaye a yau, Klopp zai zama koci na hudu - bayan Max Allegri (a shekarar 2015 da 2017), Diego Simeone (shekarar 2014 da 2016) da kuma Hector Cuper (shekarar 2000 da 2001) - da suka fuskanci irin wannan rashin nasarar a wasanni karshe na gasar zakarun Turai.

    Sai dai kuma kungiysar ba ta da irin wannan mummunar tarihin. Babu wani dan wasan da ya buga wa Liverpool a wannan kakar da ya taba buga wasan karshe a gasar zakarun Turai, sabanin 'yan kungiyar Real Madrid, inda takwas daga cikinsu ke fatan cin kofin a karo na hudu.

  5. Ramos ya yi wa Salah keta, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Salah ya fadi ana duba lafiyarsa bayan Ramos ya ma sa mugunyar keta

  6. Liverpool na taba Madrid, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Liverpool sun fara da karfinsu. Ko za su daure a haka?

  7. Liverpool ta kai hari amma golan Madrid ya kame kwallon, Real Madrid 0-0 Liverpool

  8. Kofin Zakarun Turai na biyar Ronaldo ke hari, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Ronaldo na harin lashe kofin zakarun Turai na biyar, tarihin da ‘yan wasa hudu kawai suka taba kafawa

    Dan wasan ne kuma ya fi yawan cin kallaye a gasar a bana inda ya ci 15.

    Sau shida a jere ke nan Ronaldo ya fi kowa cin kwallo a raga a gasar Zakarun Turai.

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Ronaldo ya sauya wuri, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Ronaldo ya koma gefen dama bayan ya fara a gefen hagu

  10. Ronaldo ya kai hari, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Amma ya dirka kwallon saman ragar Liverpool

  11. Haduwa ta biyu tun 1981, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Karo na biyu ke nan da Real Madrid ta hadu da Liverpool tun 1981 a Paris da Madrid ta yi nasara da ci 1-0

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Real Madrid ta koma tsaron gida, Real Madrid 0-0 Liverpool

  13. ‘Kwarewar Madrid a gasar ba komi ba ne’, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce lashe kofin zakarun Turai abu ne da ke jinin Liverpool. A cewarsa, duk da Madrid ta goge a gasar, hakan ba zai razana ‘yan wasan shi ba.

    Klopp ya taba jagorantar Borussia Dortmund wasan karshe a gasar zakarun Turai a 2013 amma ya sha kashi a hannun Bayern Munich.

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Liverpool ta matsawa Real Madrid, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Liverpool na son ta yi gaggawar zura kwallo

  15. Modric ya tare kwallon da Salah ya buga a gidan Madrid

  16. Ramos ya yi wa Salah keta, Real Madrid 0-0 Liverpool

  17. An fara wasa da zafi, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Liverpool ta kai kora biyu a gidan Madrid.

  18. Real ta kai hari, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Ronaldo ya kai kora amma Isco ya yi satar gida

  19. Andriy Shevchenko ne ya gabatar da kofi a fili kafin soma wasan

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. An fara wasa, Real Madrid 0-0 Liverpool