Kofin Duniya: Nigeria ta sake haduwa da Argentina

Ku biyo domin samun bayanai da sharhi kan jadawalin kasashen da za su fafata a Gasar cin Kofin Duniya a Russia a shekarar 2018.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahya

  1. Labarai da dumi-dumi, Brazil na cikin Rukunin E

  2. Putin ya hadu da Infantino

    Shugaban kasar Russia Vladimir Putin da shugaban hukumar kwallon kafar Duniya, FIFA, Gianni Infantino yayin da suke gaisawa a wurin rabon jadawalin gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya.

    Mr Putin na shan caccaka a wasu kasashen

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Labarai da dumi-dumi, Argentina ta fada Rukunin D

  4. Labarai da dumi-dumi, Faransa tana Rukunin C

  5. Labarai da dumi-dumi, An sanya Portugal a Rukunin B

  6. Akwai baraka a tawagar Senegal?

    Wannan ne karo na biyu da Senegal ke halartar gasar cin Kofin kwallon kafar Duniya, inda fitaccen dan wasan da aka buga gasar 2002 da shi, Aliou Cisse ke jagorantar tawagar kasar.

    Ya zabi 'yan wasa masu kwazo cikinsu har da Kalidou Koulibaly da ke buga tamaula a Napoli, da Idrissa Gana Gueye da ke buga wa Everton da kuma Sadio Mane da ke fafatawa a Liverpool.

    Sai dai ana rade-radin cewa akwai baraka a tsakanin 'yan wasan, sannan ana tababar salon horaswar da Cisseke amfani da shi.

    'Yan wasan bana sun fi wadanda suka yi wasa 2002 kwazo bayan da suka bai wa duniya mamaki inda suka doke Faransa.

    Ana tababar salon horaswar Cisse

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Maradona ya isa wajen rabon jadawalin

    Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona da mai dakinsa yayin da ya isa zauren rabon jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya na 2018.

    Maradona ya yi shaharar da ba kowanne dan wasa ne ya yi ba

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Wanne hali Brazil ke ciki?

    Brazil ce kasar da ta fi yawan daukar Kofin Duniya, inda ta lashe shi sau biyar - a shekarar 1958, 1962, 1970, 1994 da kuma 2002.

    Sai dai Jamus ta doke ta da ci 7-1 a matakin kusa da na karshe a gasar da ta karbi bakunci shekara hudu da suka wuce.

    Babban dan wasanta: Neymar. Dan wasan na gaba da aka saya kan £200m shi ne babbar kadarar Brazil, a cewar tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Pele, wanda ya goyi bayansa domin lashe kyautar Ballon d'Or.

    Neymar ne babbar kadarar Brazil, in ji Pele.

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Samuel Eto'o ya halarci wajen rabon jadawalin

    Tsohon dan wasan Kamaru Samuel Eto'o yayin da ya isa zauren jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya na 2018.

    Samuel Eto'o ya taka rawa sosai a Gasar cin Kofin Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Muhawarar da kuke tafka wa a BBC Hausa Facebook

    Mika'ilu Ahmad Usman: Mu 'yan Najeriya Allah ya sa a ba mu rukuni mai sauki amma fa ba tsoron kowacce kasa muke ba.

    Sama'ila Ala Kwankwason Fulatan:To hukumar Fifa muna fatan za ki tsara jadawalin gasar cin Kofin Duniya da zai gudana a kasar Rasha 2018 a kan tsari mai kyau da adalci.

    Ashiru Lawal Nagoma: Muna yi wa gwarzayen 'yan kwallon kafarmu na Super Eagles fatan zuwa Rasha da kafar dama domin samun tabuka abun a zo a gani.

  11. Anya ba za a samu matsala a tawagar Nigeria ba?

    Tawagar Nigeria ita ce za ta je Russia da 'yan wasa mafi jini a jika, kuma wadannan matasan 'yan wasa sun sanya wa 'yan kasar kwarin gwiwar ganin sun fitar da kitse daga wuta.

    'Yan wasan na rige-rigen ganin sun samu gurbi a bangaren kai hari, inda 'yan wasa irinsu Kelechi Iheanacho, Alex Iwobi, Odion Ighalo da kuma Victor Moses ke son ganin sun bai wa mara da kunya.

    Kyaftin John Mikel Obi da Wilfried Ndidi za su kare tsakiya.

    Sai dai ana tababa kan ingancin 'yan wasan da ke tsaron gida da kuma mai tsaron raga ko da yake nasarar da Nigeria ta yi kan Argentina da ci 4-2 a watan jiya ta sa kasar ta ja hankalin duniya.

    Tawagar Najeriya na cike da matasa

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Mai rike da kambu

    Jamus ke ke rike da Kofin Duniya a yanzu haka bayan ta lashe shi a gasar da aka yi a shekarar 2014 a kasar Brazil. Ta soma shiga gasar ne a 1908 kuma wannan shi ne karo na hudu da ta dauki kofin, wato a 1954, 1974, 1990 da kuma 2014.

    Sau hudu Jamus na daukar Kofin

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Wanne rukuni ne zai fi yi wa Nigeria dadi?

    'Yan Najeriya sun soma tofa albarkacin bakinsu kan rukunin da suke so kasar ta fada a ciki.

    Bayanan sautiMene ne ra'ayin 'yan Nigeria?
  14. An raba kasashe tukunya-tukunya

    Tukunya 1: Russia, Germany, Brazil, Portugal, Argentina, Belgium, Poland, France

    Tunkunya 2: Spain, Peru, Switzerland, England, Colombia, Mexico, Uruguay, Croatia

    Tunkunya3: Denmark, Iceland, Costa Rica, Sweden, Tunisia, Egypt, Senegal, Iran

    Tunkunya 4: Serbia, Nigeria, Australia, Japan, Morocco, Panama, South Korea, Saudi Arabia

    An raba kasashe tukunya-tunkunya

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Takaitaccen tarihin Gasar Kwallon kafar Duniya

    An soma Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ne a shekarar 1930, kuma tun daga wancan lokacin ake fafatawa duk bayan shekara hudu domin lashe Kofin in ban da a shekarar 1942 da 1946 da ba a yi ba saboda Yakin Duniya na Biyu.

    An soma gasar a  1930

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Jama'a barkanmu da saduwa a wannan shiri da zai kawo muku bayanai da sharhi kai-tsaye kan jadawalin kasashen da za su fafata a Gasar cin Kofin Duniya a Russia a shekarar 2018, tare da Nasidi Adamu Yahaya. Za ku iya bayar da gudunmawa ko tafka muhawa a BBC Hausa Facebook.