Me zai hana sojojin Nijar su miƙa mulki a wata 9? - Tinubu
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umaymah Sani Abdulmumin and Abdullahi Bello Diginza
Yara bakwai na cikin wadanda suka mutu a gobarar Afrika ta kudu
Cikin waɗanda suka mutu a gobarar Afirka ta kudu akwai yara bakwai, ciki harda jariri mai shekara ɗaya.
Rahoton da jaridun Afirka ta kudu suka wallafa ke tabbatar da hakan bayan tattaunawa da kakakin hukumar agajin gaggawa Robert Mulaudzi.
Ya kuma shaida cewa akwai mutum 52 da ke samun kulawa a asibiti.
Ma'aikatan kwana-kwana na ci gaba da aikin ceto. Sannan an kaddamar da bincike domin gano musababbin gobarar.
An buƙaci kotu ta soke naɗin da aka yi wa Hannatu Musawa
Asalin hoton, Hannymusawa
Wata ƙungiyar farar-hula da ake kira 'Incorporated Trustees of Concerned Nigerians' ta kai sabuwar ministar raya al'adu, Hannatu Musa Musawa Kotu inda ta buƙaci a soke naɗin da aka yi mata.
Ƙungiyar ta kare manufofinta kan bukatar hakan, saboda korafe-korafen da suka biyo bayan gane cewa ministar ba ta kammala aikin yi wa ƙasa hidima ba wato NYSC.
Masu shigar da karar karkashin jagorancin Deji Adeyanju sun buƙaci kotu ta duba kundin tsarin mulkin ƙasa ta fayyace musu idan mutum na iya haɗa aikin hidimar ƙasa ta NYSC da kuma muƙamin minista a lokaci guda.
Sannan sun buƙaci a ci tarar ministar naira miliyan 100 da kuma naira miliyan ɗaya kuɗin ɓata lokaci a kai ta kotu.
Takardun da suka miƙawa kotu mai shafi 13 sun kuma bayyana cewa, Hannatu Musawa ta amsa cewa yanzu take NYSC ɗinta, kuma an tura ta Abuja domin hidimtawa ƙasa.
Korafin nasu na jadadda cewa babu dokar NYSC da ta amince mai hidimatawa ƙasa ya karɓi wani aiki na gwamnati ko muƙamin siyasa.
Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi a yi adalci wajen wannan shari'a.
Yanayin da ake ciki a gaban ginin da ya ƙone a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga PDP - Nyesom Wike
Asalin hoton, NYESOMWIKE
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙalubalanci jam'iyyarsa ta PDP kan barazanar korarsa, yana mai cewa babu wanda ya isa.
A lokacin wata tattaunawa da ya yi da kafar Talabijin Channels, ministan ya ce, ba ya tsoron kowa kuma abin da ya ke yi babu batun saɓa ƙa'idar jam'iyya ko kuma zagon-ƙasa.
Wike wanda tsohon gwamnan Ribas ne, ya ce shi dai a iya saninsa bai ga wani shugaba a PDP da ya ke da ikon iya korarsa ba, ko yi masa barazana.
Ministan ya kuma jadadda cewa shi shugaba Tinubu ya ke yiwa aiki, ba wai APC ba don haka babu wanda ya ke bin sa bashi ko ya wajaba ya nemi afuwa daga gareshi.
Sabon ministan na Abuja ya kuma shaida cewa nan da watanni takwas za a ga canji sosai a birni, saboda jirgin ƙasan da zai ke yawo a cikin gari zai soma aiki, sannan mulkinsa zai dawo da abubuwa sosai musamman ainihin tsarin Abuja.
Yana mai shaida cewa dama masu arzikin Abuja ke karya dokoki birnin, don haka za su ɗau duk wani mataki na laɗabtarwa da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa.
Gawarwaki da dama sun ƙone ƙurmus a Afrika ta Kudu
Asalin hoton, Reuters
Wani rahoto da kafar yaɗa labaran Afirka ta Kudu ya fitar na cewa da wuya a iya gano wasu gawarwaki, saboda konewar da suka yi kurumus.
"Zai yi wahala a iya tantace gawarwakin mutanen da ke cikin ginin da ya kone. Gawarwakin mutanen da wutar ya kona ba za a iya gane su ba.
"Galibin 'yan uwa da iyalai sai dai su yi hakuri saboda a irin wannan yanayi ba a iya tantace gawarwaki", a cewar Ayanda Nyathi da ke aiki da kafar talabijin din Newzroom Afrika.
'Ban sani ba ko 'yata na da rai'
Cike da hawaye wata uwa mai suna, Treasurelee Shuping, wadda ke tsaye a ƙofar ginin da ke ci da wuta banga-banga, tana neman 'yarta mai shekara 24.
Ta shaidawa manema labarai cewa, "Tun lokacin da labarin gobarar ya same ni, na san ban ga ta zama ba. cikin gaggawa na iso nan domin in ga ko zan dace in gan ta"
Yanzu dai ga shi na zo, amma ban san me zan yi ba, domin ban san halin da ake ciki ba. Ban san inda na dosa ba - gaba ɗaya na ƙagara. Ba ni da tabbaci idan har 'yata na da rai."
Da aka tamabaye ta game da yanayin da ginin, wanda ke cike da ɗimbin jama'a, sai ta ce,"Ai lamarin babu kyau - wuri ne da ba za ka a yi tsammanin ɗan adam na iya rayuwa cikin sa a ba, shi ya sa ma da farko na yi ƙoƙari mayar da ita gida.
Gobarar Afirka ta kudu ta yi muni
Kawo yanzu dai an kai ga gano kimanin gawarwakin mutane 73 da suka mutu da kuma wasu 43 suka samu munanan raunuka sakamakon gobarar da tatashi a ƙasar Afirka ta Kudu.
Jami'in hukumar da ke bayar da agajin gaggawa na kasar, Robert Mulaudzi, ya shaidawa wata kafar watsa labaran ƙasar ta ENCA, cewa akwai fargabar adadin na iya ƙaruwa.
"Muna bi ɗaki-ɗaki domin gano waɗannan gawarwaki." in ji shi.
Amma a wani rahoton da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Johannesburg ta fitar ya bayyana cewa yawan waɗanda suka mutu ya kai mutum 73.
Kazalika ana kan ci gaba da gudanar da aikin neman waɗansu da ake kyautata zaton sun hallaka.
Wasu rahotanni na cewa galibin mutanen da ke cikin ginin da gobarar ta rutsa da su baƙin haure ne, da kuma ke zaune a ginin ba bisa ƙa'ida ba.
'Yan Afirka ta Kudu da dama ne ke Alla-wadai da kalaman wariya da wasu 'yan ƙasar ke yi a shafukan sada zumunta inda suke famar sukar waɗanda gobarar ta rutsa da su.
Yadda ake aikin ceto a gobarar Afirka Ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Gobara ta hallaka sama da mutum 60 a Afirka Ta Kudu
Ma'aikatan agajin gaggawa da 'yan kwana-kwana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, sun ce sama da mutane 60 sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a wani rukunin gidaje.
Jami'an sun ce mutane da dama sun ji mummunan rauni, kuma hukumomi sun ce ba a kai ga gane musabbabin tashin gobarar a ginin mai hawa biyar da ke wata unguwa a tsakiyar birnin ba.
Mai magana da yawun hukumar gaggawa Robert Mulaudzi ya shaidawa BBC 'yan kwana-kwana sun yi nasarar fito da wasu mutane daga ginin.
Ya kuma ce wutar ta mamaye daukacin ginin, hakan ya zama abu mai matukar wuya ga ma'aikatansu, amma duk da hakan za a ci gaba da neman wadanda watakil suka maƙale a ginin.
Sojojin da suka yi juyin-mulki a Gabon sun jadadda manufofinsu
Janar din sojin da ya jagoranci juyin mulki a Gabon kuma shugaban gwamnatin riƙo, ya kare matakin da sojoji suka ɗauka na kawo karshen mulkin shugaba Ali Bongo.
Janar Oligi Ngwema, ya shaidawa jaridar Le Monde ta Faransa cewa Mista Bongo ba shi da damar yin mulki a wa'adi na uku, sannan zaɓen da aka gudanar a makon da ya wuce cike ya ke da kura-kurai.
Man Foumbi shi ne kakakin shugaban riƙon wanda ya shaidawa BBC cewa Janar Oligi Ngwema ya umarci a mayar da layukan intanet da gidajen Talbijin na gida da ƙasashen waje.
A wannan Alhamis din 'yan Gabon za su iya fita harkokinsu daga karfe 6 na safiya zuwa 6 na yamma.
Mista Bongo da mahaifinsa dai sun jagoranci ƙasar Gabon na tsawon shekaru 53.
Maraba
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Bisimillahku!
Masu bibbiyar mu a wannan shafi Barka da wannan lokaci da fatan kun wayi gari lafiya. A wannan rana ni Umaymah Sani Abdulmumin tare da Zubairu Ahmad Kasarawa za mu kasance da ku.
Za mu rinka kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.