Rukunin G
Manchester City
RB Leipzig
FC Crvena Zvezda
FC Young Boys
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umaymah Sani Abdulmumin and Abdullahi Bello Diginza
Manchester City
RB Leipzig
FC Crvena Zvezda
FC Young Boys
Barcelona
FC Porto
Shakhtar Donestk
FC Royal Antwerp

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai na gudanar da taro domin raba jadawalin gasar zakarun Turai ta Champions League.
A bara Manchester City ce ta lashe gasar bayan doke Inter Milan da ci 1- 0.
Ana gudanar da taron fitar da jadawalin ne a birnin Monaco.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin da suka yi juyin mulki a Gabon sun ce ranar Litinin za a rantsar da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya na ƙasar, Janar Brice Oligui Nguema.
Sun kuma buƙaci kwantar da hankulan al'ummar duniya ta hanyar yi musu alƙawarin cewa za su mutunta dukkan alƙawurran da Gabon ta ɗauka ciki har da biyan basukan da ke kanta.
Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar tabbatar da Tsaro da Zaman Lafiya na Tarayyar Afirka ke gudanar da taro a yau Alhamis, don tattauna batun juyin mulkin Gabon na ranar Laraba.
Shugabannin juyin mulkin sun ce za a rantsar da Janar Nguema ne a gaban Kotun Tsarin Mulki ta Gabon ranar Litinin.
Wani magana da yawun sojojin juyin mulkin ya faɗa a tashar talbijin ta ƙasar cewa sannu a hankali za su kafa cibiyoyin gwamnati za su gudanar da harkokin mulki.
Ƙungiyoyin ƙasashen duniya kamar Tarayyar Afirka na dako su ji tsawon lokacin da shugabannin sojin ke da niyyar kwashewa a kan karagar mulki, kafin su damƙa al'amura a hannun fararen hula.
Yayin sanar da juyin mulkin a jiya Laraba, sojojin sun kuma soke sakamakon zaɓen da ya bai wa Ali Bongo nasara.
A yanzu, ƙawancen 'yan adawa na kira da a kammala ƙidaya ƙuri'un da aka kaɗa, don ayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara. Yiwuwar ganin hakan ta tabbata dai a Gabon yanzu, ƙalilan ce.

Asalin hoton, AFP
Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya sauya wa wasu manyan hafsoshin rundunar sojin ƙasar wuraren aiki.
Manyan hafsaoshin sojin da sauyin wurin aikin ya shafa ba su wuce muƙaman Kanal ba.
Za su kula ne da wasu muhimman wurare a yankin rainon Ingila mai fama da rikicin 'yan a-ware da ke rajin kafa ƙasar Ambazoniya, da kuma ta arewacin ƙasa inda rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita jama’a.
A makon jiya ne Ministan tsaro ya shugabanci wani taro na musamman domin tattauna lamarin taɓarɓarewar tsaron da ƙasar take fama da shi.
Ga rahoton Mohaman Babalala daga Yaounde.

Asalin hoton, Twitter/Nig.Police
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun ya ce rashin isassun 'yan sanda, na kawo wa rundunarsu tarnaƙi wajen daƙile aikata laifuka a faɗin ƙasar.
Da yake gabatar muƙala - ga manyan jami'ai masu halartar kwas na 45 a cibiyar tsara manufofi da dabarun shugabanci ta Kuru a jihar Filato - Mista Egbetokun ya ce rundunar na buƙatar ƙarin 'yan sanda 190,000 domin tabbatar da ayyukanta na tsaron rayuka da dukiyar al'umma a cikin gida.
Ya ce a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta tanadi cewa kamata ya yi ɗan sanda ɗaya ya kula da mutum 460, a Najeriya ɗan sanda ɗaya na kula da mutum 650 ne.
“Don haka rundunar 'yan sanda na buƙatar ƙarin jami'ai 190,000 domin kai wa ga mizanin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tanada,'' in ji shi.
Babban Sufeton 'yan sandan ya ce idan 'yan sanda ba su wadaci ƙasa ba, ba za a iya cimma burin manufofin gwamnati ba.
“Don haka, rashin wadatattun jami'ai, zai iya kawo cikas ga tabbatawar manufofin gwamnati,'' in ji shi.

Asalin hoton, others
Aƙalla fiye da fasinjoji shida ne aka bayyana cewa sun ɓace bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a kogin Zamre a ƙaramar hukumar mulki ta Agwara da ke jahar Naija.
Jaridar Daily Trusta ta ruwaito cewa lamarin ya faru a ranar Litinin lokacin da matafiyan waɗanda galibinsu manoma ne ke kan hanyar tafiya daga Naija zuwa jahar Kebbi.
A halin yanzu an gano gawar mutum ɗaya daga cikin su, sannan ana ci gaba da neman sauran da suka ɓacen.
Rahotan ya ce kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji 20 da suka haɗa da mata da ƙananan yara, inda ya kife sakamakon tsayawar injin daidai lokacin suka kai tsakiyar kogin.
Jaridar ta ruwaito cewa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jahar Naija ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai babban daraktanta, Garba Salihu, ya ce kawo yanzu ba a kai ga samun cikakkun alƙalumman waɗanda suka mutu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Mai kamfanin sada zumunta na X da a baya aka fi sani da Twitter Elon Musk ya ce nan ba da jimawa ba shafin zai bai wa ma'abotansa damar fara kiran waya da na bidiyo.
Cikin wani saƙon X da ya wallafa Mista Musk ya ce hakan na daga cikin matakan mayar da shafin na komai-da -ruwanka.
“Kiran waya da na bidiyo na nan tafe a shafin X'', kamar yadda ya rubuta ba tare da cikakkken bayani kan lokacin da za a fara amfani da su a shafin ba..
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mista Musk ya ce za a iya samun duka kiraye-kirayen biyu a wayoyin IPhone da na Android da kamfutoci.
Ya ci gaba da cewa ba a buƙatar lambar waya domin morar waɗannan sabbin tsare-tsaren da ya ɓullo da su.

Asalin hoton, Getty Images
A na ci gaba da nuna fargaba game da matakin Kamfanin Haƙar Mai na Najeriya, NNPC Limited, na nemo rancen dala biliyan 3 daga Bankin Afirka domin taimakawa wajen farfaɗo da kasuwar musayar kuɗaɗen waje da ke ci gaba da durƙushewa.
Ana dai yi wa wannan matakin kallon mayar da hannun agogo baya kasancewar samun ƙaruwar faɗuwar darajar naira da ake samu da kuma tashin farashin dala a kasuwa.
Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Kuɗaɗen ajiyar Najeriya na ƙetare na ci gaba da raguwa kashi 0.2 zuwa dala biliyan 33.68, hakan ya faru bayan da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fitar da sanarwar matakin a ranar 16 ga watan Agusta.
A baya dai an ɗauka cewa matakin nemo rancen dala biliyan 3 zai taka rawar a za gani wajen farfaɗo da darajar naira, da kuma saukar farashin dala a kasuwannin musayar kuɗi, wanda ta hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa farashin abubuwa a ƙasa.
Daga cikin abubuwan da ke ƙara karya farashin naira har da tsananin buƙatar dala da jama'a ke yi, inda yanzu haka a kasuwar bayan fage a kan sayi dala ɗaya kan naira 920 zuwa 925.
A shekara ta 2021, Wani mai ɗaukar hoto Shiraaz Mohamed ya kai wata ziyara wannan yanki rukunnin gidaje da ke birnin Johannesburg, domin ganewa idonsa irin rayuwar da ake yi a ginin da ya tara masu aikata muggan laifuka da shaye-shaye da karuwai.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Twitter/Itte
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayar da umurnin fitar da jakadan Faransa da ke ƙasar, inda ta ce a yanzu ya rasa kariyarsa ta diflomasiyya.
Mista Sylvain Itte ya ci gaba da zama a Nijar duk da cikar wa'adin sa'o'i 48 da aka ba shi na ya fice daga cikin ƙasar a ranar Juma'ar da ta gabata.
Sai dai gwamnatin Faransa ta bayyana cewa jakadanta a Nijar ba zai fice daga ƙasar ba saboda gwamnatin sojojin ba ta da halarci.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar na cewa "muna nazari a kan tsaron lafiya da kuma kariya a ofishin jakadancinmu."
Sojojin dai sun ce sun tuɓe wa jakadan na Faransa rigar kariyar diflomasiyya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Nijar na cewa jakadan "a yanzu ba zai ci moriyar alfarmomi da rigar kariyar da ake bai wa jami'an diflomasiyya masu matsayi irin nasa a ofishin jakadancin Faransa ba".
"Duk takardun(sa) na diflomasiyya da biza har ma da na iyalansa, an soke su.
A ranar Juma'a cikin makon jiya ne, hukumomin sojin suka bai wa jakadan Faransa wa'adin sa'a 48 don ya bar Nijar.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan layin dogo biyar sun mutu, bayan wani jirgin kasa mai karfin gaske ya banke su a kasar Italiya.
Ma'aikatan dai na ɗauke ne da kayan aikin da za su yi amfani da su wajen gyaran wani layin dogo a lokacin da jirgin ya banke su, a kusa tashar jirgi da ke Turin.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ma'aikatan biyu da ke tare da 5 din da iftila'in ya ritsa da su, sun tsallake rijhiya da baya.
A ɓangare guda kuma 'yan sanda sun ce suna gudanar da bincike a kan lamarin.

Asalin hoton, HOUSEOFREP
Hukumar kula da shirin dashen itatuwa wanda aka fi sani da Great Green Wall Project na fuskantar bincike kan yadda ake zargin ta kashe naira biliyan 81 domin dashen bishiyoyi miliyan ashirin da ɗaya a jihohin arewa da ke kan iyakar Najeriya.
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya ne ke gudanar da binciken, a kan yadda aka yi amfani da asusun raya muhalli da alkinta yanayi da wasu kuɗaɗen asusun.
Jihohin sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauci da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno.
Daraktan Hukumar ta NAGWW, Yusuf Maina Bukar, ya shaida wa kwamitin cewa hukumar ta kashe naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishinta da kuma naira biliyan 11.28 don gudanar da manyan ayyuka.
Ya ƙara da cewa galibin kuɗaɗen da hukumar ke samu, sun fito ne daga kashi 15 cikin ɗari na kuɗaɗen asusun alkinta yanayi da muhalli da kuma waɗanda gwamnatin tarayya ke samarwa.
Baya ga wannan ma, kwamitin ya kuma binciki Babban Bankin Najeriya game da wasu asusun ajiya fiye da bakwai da bankin ya san da su.
Wasu takardun bayanai masu shafuka shida ɗauke da kwanan watan 22 ga Agustan 2023 da bankin na CBN ya miƙa wa kwamitin sun nuna cewa an sakawa asusun hukumar kusan naira biliyan 9 da rabi, tun daga 2015 zuwa wannan ranar.
Babban akantan Najeriya, Oluwatoyin Madein ya bayyana cewa Hukumar kula da shirin dashen itatuwa da alkinta yanayi ta NAGWW ɗin ta ƙarbi kuɗin da yawansu ya zarce naira biliyan 19 tun daga watan Fabrairun 2019 kawo yanzu.
Shugaban kwamitin binciken na majalisar wakilai ta ƙasa, Isma’ila Haruna Dabo tare da sauran mambobin kwamitin sun nuna damuwa kan yadda aka kashe kuɗaɗen babu kan gado.
Kwamitin ya bayyana cewa ya zama wajibi su gudanar da cikakken bincike kan wannan batu duba da irin maƙudan kuɗaɗe da hukumar ke samu daga gwamnatin tarayyar Najeriya da ma sauran ƙasashen waje amma ta sauka daga kan turbar da aka ɗora ta a kai.