Shugaba Bazoum ya gana da likitansa

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Hafsoshin tsaron Ecowas sun ɗage zaman da za su yi kan Nijar

    Ecowas

    Asalin hoton, REX/Shutterstock

    An dage taron da manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma suka shirya yi don tattauna batun juyin mulkin Nijar.

    Tun farko an sa ran taron, wanda kungiyar Ecowas mai raya tattalin arzikin ƙasashen na Afirka ta Yamma ta kira, za a yi shi ne a Accra, babban birnin kasar Ghana a yau Asabar.

    Babu wani dalili da aka bayar game da daga taron.

    A ranar Alhamis Ecowas ta bayar da umarnin cewa dakarun kungiyar su kasance cikin shiri don dawo da mulkin farar hula a Nijar.

    Shugaban mulkin soja Abdourahmane Tchiani, wanda ya ƙwace mulki ranar 26 ga watan Yuli, ya kafe cewa duk ƙasar da ta kai musu hari za su kare kansu

  2. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya.

    Sunana Umar Mikail kuma ni ne zan kasance da ku a wannan hantsi na Asabar.

    Ku biyo mu.