Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Kepa Arrizabalaga na daf da zuwa aro Real Madrid
Shugaba Bazoum ya gana da likitansa
Asalin hoton, PRESIDENCE DE LA REPUBLIQUE DU NIGER
Bayanan hoto, Shugaban Nijar da sojoji suka hamɓarar
Magoya bayan hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum sun ce likitansa ya kai masa ziyara domin duba lafiyarsa.Kamfanin dillancin labaran Faransa ya kuma bayyana cewa likitan ya yi wa Mista Bazoum da matarsa da ɗansa guzirin abincin gargajiya da shugaban ya fi so a inda suke tsare.
Baya ga abinci da suka kunshi gayyaki da likitan ya kai wa hambararren shugaban na Nijar, ya kuma kai masa magungunna.
Likitan ya kuma nuna damuwa kan yanayin wurin da ake tsare da Bazoum a wani ɗakin ƙarƙashin ƙasa da ke fadar shubaban ƙasar a birnin Yamai inda ko lantarki babu.
Sojojin dai na tsare ne da Bazoum da iyalinsa da kuma dansa mai shekara 20, kuma tun bayan da suka ƙwaci mulki a hannunsa a ranar 26 ga watan Yuli suke tsare da shi.
Kasashen duniya, ciki har da Amurka, da Tarayyar Turai da Majalisar
Dinkin Duniya na ci gaba da nuna damuwa game da lafiyar
zaɓaɓɓen shugaban da kuma lafiyar iyalinsa.
Tuni dai hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rahotannin da ake ruwaitowa kan yanayin da ake tsare da Bazoum sun saɓa wa dokokinta na kare hakkin dan adam.
Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbatar ba, sun ce sojojin da suka hambarar da Bazoum suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.
Masharhanta dai na ganin matsin lamba ga sojojin na Nijar ne ya sa suka ba Bazoum damar ganawa da likitan nasa.
Ronaldo ya ɗauki kofin Zakarun ƙasashen Larabawa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A watan Janairu Ronaldo ya koma taka-leda a Saudiyya, bayan raba gari da Manchester United.
Cristiano Ronaldo ya ɗauki kofin Zakarun ƙasashen Larabawa bayan da ƙungiyarsa ta Al-Nassr ta doke Al-Hilal da ci 2-1.
Dan wasan na ƙasar Portugal ne ya zura duka ƙwallo biyun da ƙungiyar ta ci a ƙarawar.
Wannan shi ne kofi na farko da Ronaldo ya ci tun bayan komawa ƙungiyar a watanni takwas da suka gabata.
Bayan kammala gasar Kofin Duniya ne, Ronaldo ya koma taka-leda a Saudiyya, bayan raba gari da ƙungiyarsa ta Manchester United.
Komawar tsohon ɗan wasan Real Madrid ɗin zuwa Saudiyya ta buɗe ƙofa ga sauran fitattun 'yan wasan Turai wajen komawa buga gasar ta Saudiyya.
Cikin wannan shekara fitattun 'yan wasa irin su Karim Benzema da Ngolo Kante da Riyad Mahrez da sauran 'yan wasan Turai da dama ne suka koma buga gasar ta Saudiyya.
Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta ce ta kai harin makamai mai linzami kan gadar da ta haɗe yankin Crimea
Asalin hoton, Reuters
Rasha ta ce jami'anta sun kai hari da makamai biyu masu linzami kan gadar da ta haɗe yankin Crimea.
Wasu bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ke tashi a saman gadar.
Ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta ce makaman biyu ƙirar S-200 da aka harba kan gadar, sun haddasa mummunar ɓarna.
Kawo yanzu Ukraine ba ta ce komai ba game da harin.
Sau biyu ana kai wa gadar hari a cikin watannin da suka gabata.
An buɗe gadar a shekarar 2018 domin bayar da damar harkokin sufurin mota da na jiragen ƙasa tsakanin yankin Cremea - da Rasha da ƙwace a shekarar 2014 - da Ukraine
Gadar na da matuƙa muhimmanci da dakarun Rasha da ke riƙe da wasu yankunan kudancin Ukraine.
Arsenal ta fara kakar Premier ta bana da kafar dama
Ranar Matasa ta Duniya: Tinubu ya taya matasan Najeriya murna
Asalin hoton, Tinubu/Twitter
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya matasan ƙasar murnar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musu.
Cikin wani saƙo da ya wallafa shafinsa na Tuwita, shugaba Tinubu ya ce ''A yayin da kuke bikin ranar Matasa ta Duniya, ku sani cewa ilahirin ƙasarmu na tare da ku, domin taimaka muku cimma burinku''.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Tinubu ya kuma yi kira ga matasan da su yi ƙoƙari wajen fuskantar ƙalubalen da ke gabansu, domin cimma burikansu.
''Ku ci gaba da zama jakadun ƙasarmu na gari, kasancewar makomar ƙasarmu na hannunku'', in ji Tinubu.
Ra'ayi Riga: Tasirin takunkuman da Ecowas ta sanya wa Nijar
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon - wanda Imam Saleh ya gabatar - ya duba batun tasirin takunkuman da Ecowas ta sanya wa Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.
Tuni dai ƙungiyar Ecowas ta rufe kan iyakokinta da Nijar, lamarin da ya haifar da tashin farashin kayan abinci a Jamhuriyar Nijar ɗin.
Haka kuma Najeriya ta sanar da katse wutar lantarkin da take bai wa Nijar ɗin.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Bayern Munich ta kammala daukar Kane daga Tottenham
Malaman Addinin Musulunci sun isa Nijar don ganawa da sojojin ƙasar
Asalin hoton, Niger Media
Bayanan hoto, Malaman Addinin sun sauka a filin jirgin saman Yaman da tsakar ranar Asabar
Kungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Najeriya ta isa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarinta na shiga tsakanin sojojin da suka kifar da gwamnatin ƙasar da kuma ƙungiyar Ecowas.
Tawagar malaman ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta ƙunshi manyan malamai irin su Sheikh Kabiru Gombe, da Farfesa Mansur Sokoto da sauran malamai.
A taron da ƙungiyar Ecowas ta gudanar ranar Alhamis a Abuja ta sake jaddada matakain ƙaƙaba wa Nijar takunkumai, tare da umartar dakarun kungiyar su kasance cikin shirin ko-ta-ƙwata.
Gabanin taron na Ecowas, tawagar malaman sun gana da shugaban Najeriya, kuma shugaban kungiyar Ecowas a fadar gwamnatinsa da ke Abuja.
Malaman sun shawarci shugaba Tinubu da kada Ecowas ta yi amfani da ƙarfin soji kan Nijar ɗin.
Asalin hoton, Niger Media
Bayanan hoto, Tawagar malaman sun sauka a filin jirgin sama da ke birnin Yamai da tsakar ranar Asabar
Ranar Matasa ta Duniya: Abubuwan da ke damun matasan Najeriya
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Albarkacin Ranar Matasa ta Duniya, mun tattauna da wasu matasa a Najeriya don jin ƙalubalen da suke fama da shi.
Mufida Sani, da Zainab Aliyu, da Abdallah Ibrahim ne sun amince cewa akwai buƙatar matasa su rage dogaro da gwamnati.
Ba za mu taɓa yin juyin mulki ba a Najeriya - Rundunar soji
Asalin hoton, Defense Headquaters
Bayanan hoto, Shugaba Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa a matsayin hafsan hafsoshin Najeriya a watan Yuni
Rundunar Sojin Najeriya ta ce kiran da wasu 'yan ƙasar ke yi mata da ta yi juyin mulki "tsananin rashin kishin ƙasa ne da kuma mugunta".
Cikin wani saƙo da sojojin suka wallafa a shafinsu na Tuwita, sun ce suna mayar da martani ne sakamakon kiraye-kirayen da wasu ke yi suna fakewa da rashin kula da walwalar dakarunta.
"Hedikwatar tsaro ba ta jin daɗin kiraye-kirayen da ake yaɗawa a intanet game da walwalar dakarunta," in ji Birgediya Janar Tukur Gusau cikin wata sanarwa a ranar Juma'a.
"Yayin da muke ɗaukar walwalar dakarunmu da muhimmanci, muna kuma yin tir da yunƙurin wasu na neman Rundunar Sojin Najeriya mai bin doka ta sauya gwamnati a ƙasarmu ba ta hanyar da tsarin mulki ya tanada ba.
"Muna tabbatarwa ƙarara cewa rundunar ta gamsu kuma ta fi son zama a ƙarƙashin mulkin dimokuraɗiyya, kuma ba za ta yi wani abu da zai kawo wa dimokuraɗiyya cikas ba."
Juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar ya kasance na tara (har da yunƙurin da bai yi nasara ba) da aka yi a yankin Afirka ta Yamma tun daga 2020, inda ya shafi ƙasashen Mali, da Guinea, da Burkina, da Nijar - idan aka haɗa da Chadi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas), shi ne ke jagorantar yunƙurin tilasta wa sojoji su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki da ƙarfin tsiya.
'Labarin ƙona ofishin jakadancin Najeriya a Nijar na ƙarya ne'
Asalin hoton, Federal Ministry of Foreign Affairs
Ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ya musanta rahotannin da ke cewa masu zanga-zanga sun ƙona ofishin.
Tun a tsakiyar mako aka fara yaɗa wani bidiyo a shafukan sada zumunta da iƙirarin cewa masu goyon bayan sojojin mulki a Nijar ɗin ne suka cinna wa ofishin wuta.
"Duk da cewa masu zanga-zanga sun so kutsawa cikinsa a ranar 30 ga watan Yuli, sojojin Nijar da 'yan sanda sun daƙile yunƙurinsu," a cewar wata sanarwa da ofishin ya fitar ranar Juma'a.
"Har yanzu sojojin Nijar da sauran jami'n tsaro na ci gaba gadin sa."
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas), shi ne ke jagorantar yunƙurin matsa wa sojoji su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki.
Gwamnatin Burkina Faso ta ce za ta aika wa maƙwabciyarta Nijar hatsi, kamar yadda rahoton Radio Omega ya bayyana.
Wata sanarwa da ma'aikatar cigaban kasuwanci ta ƙasar ta fitar ranar Juma'a ta ce za a aika wa Nijar ɗin gero da masara da dawa, da dai sauransu.
Yunƙurin na zuwa ne yayin da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkuman kasuwanci da na tattalin arziki sakamakon juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a ƙarshen watan Yuli.
Duk da cewa Burkina Faso mamba ce a Ecowas, ba ta bi umarnin ƙungiyar ba ta raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma saboda ita ma tana cikin takunkumai na juyin mulki.
Sanarwar ta kuma yi kira ga 'yan kasuwar da ke da sha'awar safarar kayan su tuntuɓi hukumomin da suka dace don isar da kayan zuwa Nijar.
Burkina Faso, da Mali, da Guinea dukkansu mambobin Ecowas da aka dakatar saboda juyin mulki, sun sanar da cewa za su goya wa sojojin mulkin Nijar baya idan ƙungiyar ko kuma dakarun ƙasar waje suka kai musu hari.
Takunkumin da Ecowas ta saka wa Nijar ya fara haifar da tsadar rayuwa
Ana kukan tsadar kaya a Ghana da Najeriya saboda rufe iyakokin Nijar
Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar
Jihar Kano za ta kafa dokar kula da kuma inganta wuraren tarihi
Asalin hoton, Getty Images
Babban sakataren hukumar kula da tarihi da al’adu ta jihar Kano, Ahmad A. Yusuf, ya faɗa wa BBC Hausa cewa gwamnatin jihar na shirin kafa dokar da za ta kare tare da kula da wuraren tarihi.
Sakataren ya ce tuni aka ware kuɗaɗen da za a gudanar da aikin sake gina wasu ƙofofin shiga birnin da aka gina shekaru aru-aru.
Kazalika, ya ce za a yi wa Gidan Makama kwaskwarima, wanda aka gina fiye da shekara 500 da suka wuce.
Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar a cikin shirin Gane Mini Hanya:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mini Hanya:
Harry Kane ya koma Bayern Munich daga Tottenham
Asalin hoton, @FCBayernEN
Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Harry Kane ya koma ƙungiyar Bayern Munich kan yarjejeniyar shekara huɗu.
Tafiyar tasa ta kawo ƙarshen taka leda na shekara kusan 20 da ya yi a Tottenham.
Bayern ta ɗauki ɗan wasan gaban kan yuro miliyan 100 haɗi da tsarabe-tsarabe, kuma akwai yiwuwar zai buga wasan ƙarshe da za ta buga da RB Leipzig a gasar German Super Cup a yau Asabar.
Kane mai shekara 30 ya bar Tottenham a matsayin ɗan wasan da ya fi ci mata ƙwallaye - 280 cikin wasa 435.
Cikin wani saƙo a shafukansa na zumunta, Kane ya ce "na ji a raina cewa lokacin barin Spurs ya yi".
Sojin Najeriya sun kashe 'yan fashi uku da ceto mutum 10 a Kaduna
Asalin hoton, Nigeria Army
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan fashin daji uku tare da ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa ta ce dakarun sun yi nasarar kashe 'yan bindigar ne a dajin Kabode da ke ƙaramar hukumar Chikun ranar Juma'a bayan sun yi musu kwanton-ɓauna.
Kafin haka, a ranar Alhamis kuma dakarun suka bi sawun wasu mutane da aka ce an sace a ƙauyen Danbaba na ƙaramar hukumar Igabi.
"Da ganin dakarun a Birnin Yero, sai 'yan fashin suka gudu suka bar dukkan mutum 10 da suka yi garkuwa da su," a cewar sanarwar da aka fitar a yau Asabar.
Ta ƙara da cewa an haɗa mutanen da iyalansu bayan likitoci sun duba lafiyarsu.
Ciwon siga da illarsa ga mata masu ciki
Filin Lafiya Zinariya na wannan makon ya tattauna kan ciwon siga da kuma illar da yakan haifar wa mata masu ciki.
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Lafiya Zinariya
Hukumomin Hawaii na bincke game da wutar da ta kashe mutum 67
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Babban mai shari'a a Hawaii ya bayar da umarnin a gudanar da binicke kan yadda ake aikin kashe wutar dajin birnin da kawo yanzu ta kashe mutum akalla 67.
Ana ta tuhumar mahukunta a kan ko za su iya yin wani abu wajen gargaɗin mazauna tsibirin Maui kafin lamarin ya yi ƙamari.
Wakilin BBC ya ce Gwamnan Hawaii Josh Green ya ce ya bayar da umarnin a duba yadda aikin ceto da shawo kan wutar ke gudana, kuma iska mai karfin da ake yi na kara rura wutar dajin da ke ci.
Yawancin garin Lahaina duk ya zama toka, amma an ba wa wasu daga cikin mazauna garin damar zuwa su ga yadda wutar ta lalata musu gidaje.
Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki bayan kwana 17
Asalin hoton, Science Photo Library
Ƙungiyar lokitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta janye yajin aikin da ta shiga bayan kwana 17, inda likitocin za su ci gaba da aiki daga yau Asabar.
Shugaban ƙungiyar National Association of Resident Doctors (NARD), Dr. Emeka Orji, ya faɗa wa BBC cewa sun jingine yajin ne bayan gwamnatin tarayya ta amince da kafa gidauniyar horaswa ta Medical Residency Training Fund.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta fara shirin biyan su alawus na rage wahalar aikin da suke sha a asibitocin gwamnati sakamakon ficewar likitoci zuwa ƙasashen waje, kamar yadda suka nema.
A cewar Dr. Orji, waɗannan ne manya daga cikin buƙatun nasu kuma za su zauna don duba cigaban da aka samu nan da mako biyu.
Likitocin waɗanda su ne kashi 60 cikin 100 na kafatanin likitocin gwamnati a Najeriya, sun ƙaurace wa ayyuka ranar 26 ga watan Yuli, suna masu neman ƙarin kulawa da kuma inganta yanayin aikin nasu.