NDLEA ta gano wajen da ake sarrafa muggan ƙwayoyi a Legas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Mamakon ruwan sama ya kashe mutum 28 a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, EPA

    Ruwan sama kamar da bakin-kwarya gami da tsawa ya ɗaiɗaita al'umma a Pakistan, inda ya kashe mutum 28 zuwa yanzu.

    Aksarin waɗanda suka mutu mazauna Lardin Khyber Pakhtunkhwa ne.

    Mamakon ruwan ya haddasa ambaliyar ruwa da lalata gwamman gidaje, an dinga nuna hotuna da ke nuna rufin gidaje fayau da faɗuwar gine-gine.

    Sama da mutum 140 aka kƙiyasata kawo yanzu sun jikkata.

    An kuma samu wasu da suka rasa rayukansu a yankin Punjab.

    Masu aikin ceto sun bazama yankunan da ambaliyar ta afka wa domin taimaka wa mutane.

  2. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi na Lahadi.

    Ku biyo mu don sanin halin da duniyar ke ciki har zuwa daren yau.