NDLEA ta gano wajen da ake sarrafa muggan ƙwayoyi a Legas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Saudiyya na son haɗa hannu da China

    Ministan Makamashi na Saudiyya ya ce yana son haɗa hannu da China amma ba gogayya ba.

    A baya-bayan nan alaƙa tsakanin ƙasashen biyu na ƙara yauƙaƙa.

    Da yake magana a yayin wani taron kasuwanci da ya gudana tsakanin ƙasashen biyu a Riyad, Yarima Abdulaziz Bin Salman ya ce bai damu da maganganun da ake yi ba a Amurka na nuna damuwa kan ingantuwar alaƙa tsakanin Saudiyya da Chinan.

    A watannin da suka gabata ne, Bejeing ta ja ragamar daidaita alaƙar tsakanin Saudiyya da Iran, waɗanda suka daɗe ba sa ga miciji.

    Wani mataki da masu sharhi ke kallo a matsayin faɗaɗa ikon China a yankin ƙasashen Larabawa, inda Amurka ta daɗe tana shimfiɗa ikonta.

  3. Betara da Gagdi sun janye wa Tajudeen Abbas takarar kakakin majalisar wakilai

    a

    Asalin hoton, Tajedeen Abbas/Twitter

    Masu neman kujerar kakakin majalisar wakilan Najeriya guda biyu Hon. Aliyu Betara da Hon. Yusuf Gagdi sun janye wa Tajudeen Abbas don zama kakakin majalisar wakilan kasar ta 10.

    Betara da Gagdi sun bayyana janye takarar tasu ne jim kaɗan bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, ranar Lahadi.

    A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna mataimakin shugaban kasar Sanata Kashim Shettima na tabbatar da batun janyewar Betara da Gagdi.

    Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar dai na mara wa Hon. Tajuden Abbas da Benjamin Kalu don zama kakakin majalisar da mataimakinsa, a ƙunshin majalisar wakilan ƙasar ta 10.

    A ranar Talata 13 ga watan Yuni ne za a ƙaddamar da sabuwar majalisa ta 10 a ƙasar, bayan babban zaɓen ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata

  4. Djokovic ya zama kan gaba a yawan lashe kofunan Tennis bayan cin na 23

  5. Gwamnatin Kwara za ta samar da motoci don taimaka wa ɗalibai da ma'aikata

    kwara

    Asalin hoton, Kwara State Govt/facebook

    Gwamnan jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya AbdulRahman AbdulRazaqAbdulRahman AbdulRazaq ya amince da samar da manyan motoci domin taimakawa wajen jigilar ɗaliban manyan makaratun jihar da ma'aikatan gwamnnatin a birnin Ilorin da kewaye.

    A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Rafiu Ajakaye ya sanya wa hannu, aka kuma wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ta ce an samar da manyan motocin ne domin taimaka wa dalibai wajen rage musu raɗadin da cire tallafin man fetur ya haifar.

    Matakin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin rage wa al'ummar jihar raɗadin cire tallafin man fetur, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce ''daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin da muke ciki za a samar da manyan motoci da za su riƙa jigilar ɗaliba manyan makarantun gaba da sakandire a birnin Ilorin da kewayensa, ciki har da masu zuwa jami'a jiha da ke Malete''.

    ''Gwamnatin jiha za ta ci gaba da samar da tallafi ga al'ummar jihar Kwara, yayin da najeriya ke tunkarar rayuwa ba tare da tallafin mai ba'', in ji sanarwar.

    Tun da farko da gwamnatin jihar ta rage kwanakin aikin gwamnati zuwa wuni uku a faɗi jihar.

  6. Yadda take kayawa a kasuwar sayen 'yan ƙwallo ta nahiyar Turai

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Yayin da ake tunkarar kakar saye da sayar da 'yan wasa ta nahiyar Turai, tuni manyan ƙungiyoyi suka fara cefanen 'yan wasa.

    Manyan 'yan wasa irin su Messi da Benzema tuni suka koma wasu ungiyoyin da ke wajen Turai.

    Ko wanne hali ake ciki yanzu game da cinikin 'yan wasan?

  7. Na ji raɗaɗin ciwon kafa a wasan Inter - De Bruyne

  8. NDLEA ta gano wajen da ake sarrafa muggan ƙwayoyi a Legas

    NDLEA

    Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta gano wani ɗakin gwaji da ake haɗa miyagun ƙwayoyi a asirce.

    A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta ce jami'an hukumar ne suka gano ɗakin gwajin wanda ake sarrafa miyagun ƙwayoyin a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Sanarwar ta ce an samu wasu ƙwayoyi da aka sarrafa a ɗakin a lokacin da jami'an hukumar suka kai samamen.

    Hukumar ta ce ta samu nasarar ƙaddamar da samamen ne bayan da ta samu bayanan sirri game cewa ana sarrafa miyagun ƙwayoyi a wurin.

    Haka kuma NDLEA ta ce tana ƙoƙari wajen ganin ta kama mutumin da ya mallaki wurin.

  9. An hana direbobin haya ɗaukar sojoji a Somaliya

    Moghadishu

    Hukumomin soji a gundumar Banadir da ke Somaliya sun fitar da wani gargaɗi ga direbobin haya a yankin da su guji ɗaukar sojoji a ababen hawansu.

    Sanarwar ta haramta wa direbobin motocin haya da babura masu ƙafa uku da kuma babura ɗaukar sojojin ƙasar a ababen hawansu.

    Hukumomin sun ce an tanadi doka mai tsanani kan direbobin da suka ƙi bin wannan umarni.

    Wannan sabuwar doka na zuwa ne bayan da mayaƙan ƙungiyar al-Shabab sanye da kayan sojoji suka ƙaddamar da hari kan wani gidan cin abinci ranar Juma'a da dadare tare da kashe mutum 16.

  10. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. Laimer ya koma Bayern Munich kan kwantiragin kaka huɗu

  12. Shugaba Tinubu zai yi jawabin Ranar Dimokuraɗiyya karon farko

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, @officialABAT

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi wa 'yan ƙasar jawabin Ranar Dimokuraɗiyya karon farko bayan hawansa mulki.

    Zai yi jawabin da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar Litinin, 12 ga watan Yuni, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.

    "Ana umartar gidajen rediyo da talabijin da sauran kafofin labarai na intanet su jona daga Gidan Rediyon Najeriya da kuma NTA," in ji sanarwar da Abiodun Oladunjoye ya sanya wa hannu.

    A baya dai, ana yin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ne a ranar 29 ga watan Mayu, kafin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya zuwa 12 ga Yuni a 2018.

  13. Wata matashiyar a Najeriya na yunƙurin yin girkin awa 120

    Damilola Adeparusi

    Asalin hoton, @lolaAdeparusi

    Wata matashiya 'yar Jihar Ekiti a kudancin Najeriya mai suna Damilola Adeparusi na can tana yunƙurin kafa tarihi na mafi daɗewa tana yin girki a duniya, inda take son cimma awa 120.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Adeparusi, wadda ɗalibar Jami'ar Tarayya ta Oye-Ekiti ce, tuni ta yi girki na awa 56 ya zuwa safiyar Lahadi a Ilupeju-Ekiti.

    Tana girka sanwar ce a wani gida a Ƙaramar Hukumar Oye, kuma ta fara ne da ƙarfe 12:00 na dare a ranar Alhamis (Juma'a 9 ga watan Yuni), amma a wani ƙaramin wuri da babu iska sosai.

    Matashiyar na ƙoƙarin zarta Hilda Baci ne, wadda ta ce ta yi girkin awa 100 a Jihar Legas da zimmar shiga kundin tarihi na Guinness World Record. Sai dai Guinness sun ce suna aikin tantance gaskiyar iƙirarin nata tukunna.

    Baya ga kasancewarta mai girki, Adeparusi marubuciyar waƙar zube ce, a cewar NAN.

  14. 'Da an ga baƙar fata sai a ce wannan ba ɗan Tunisiya ba ne'

  15. Mun karɓi ƙorafi 705 daga 'yan Najeriya a Majalisa ta Tara - Ahmad Lawan

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Facebook/Ahmad Lawan

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya mai barin gado, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce Majalisa ta Tara da ya jagoranta ta karɓi ƙorafi 705 daga ɗiɗaikun 'yan ƙasar cikin shekara huɗu.

    Da yake jawabin bankwana a ranar Asabar a zauren Majalisar, Ahmad Lawan ya ce sun samu ƙorafi 146 a shekarar farko, 239 a shekara ta biyu, 232 a shekara ta uku, da kuma 88 a ta uku.

    "Dukkansu suna matakai daban-daban na samun biyan buƙata," in ji shi.

    Kazalika, 'yan Majalisa ta Tara sun gabatar da ƙudiri 361 (motion) sannan kuma suka ɗauki matsaya (resolution) 488 a kan batutuwa daban-daban da suka ja hankalin gwamnati a kansu, a cewarsa.

    "Kwamatocin sa-ido na Majalisa ta Tara sun kai ziyarar aiki 371 zuwa ma'aikatu da sashe-sashe da hukumomi da kuma wuraren gudanar da ayyuka a faɗin ƙasa," kamar yadda ya bayyana.

    A ranar Talata mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Majalisa ta 10, yayin da ake ci gaba da tafka siyasa game da wanda zai maye gurbin Ahmad Lawan a matsayin shugaba.

    Jam'iyyar APC mai mulki dai na son 'yan majalisar su zaɓi Godswill Akpabio daga Jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya, a matsayin shugaba, da kuma Barau Jibrin daga Kano a arewacin ƙasar a matsayin mataimakinsa.

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Facebook/Ahmad Lawan

  16. Romaniya ta nemi afuwa bayan jakadanta ya kwatanta 'yan Afirka da birai

    Dragos Tigau

    Asalin hoton, AFP

    Romaniya ta kira jakadanta gida daga Kenya kuma ta nemi afuwa bayan ya kwatanta 'yan Afirka da birai.

    Dragos Tigau ya yi kalaman ne yayin wata ganawa a wani ginin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Nairobi ranar 26 ga watan Afrilu.

    A cewar kamfanin labarai na AFP, Mista Tigau ya ce "tawagar Afirka ta shigo cikinmu" lokacin da ya hango wani biri ta taga.

    Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Kenya, Kamau Macharia, shi ne ya fara fito da kalaman na Tigau a ranar Alhamis.

    A ranar Asabar Romaniya ta sanar cewa sai a wannan makon aka sanar da ita abin da ya faru kuma "ta fara shirin kiran jakadan nata zuwa gida".

  17. Muna kan hanyar kamo Real Madrid - Guardiola

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya gargaɗi Real Madrid cikin raha cewa ƙungiyar tasa na kan hanyar kamo ta a yawan kofunan Zakarun Turai na Champions League.

    Real ta jinjina kofin na Champions League har sau 14, City kuwa sai a jiya Asabar ta ɗauki na farko a tarihinta.

    "Muna kan hanyarmu," kamar yadda ya faɗa cikin barkwanci bayan an tashi daga wasan.

    "Idan suka yi barci, kamo su za mu yi."

    Man City ta ci kofin ne bayan doke Inter Milan 1-0 a birnin Istanbul na Turkiyya a gaban 'yan kallo fiye da 74,000.

  18. Me ake nufi da sarkin Katsinan Gusau, me ke haifar da wutar daji?

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku:

    Filin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi biyu kan abin da ake nufui idan aka ce sarkin Katsinan Gusau da abin da haifar da wutar daji a wasu ƙasashen duniya.

  19. Masar ta daina barin 'yan Sudan shiga ƙasarta ba tare da biza ba

    'Yan Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Masar sun fito da sabbin tsare-tsare a kan iyaka da ke bukatar dole duk mutumin da ya taso daga Sudan ya gabatar da biza kafin ya shiga kasar.

    Matakin sabon sauyi da ya sha bamban da tsare-tsaren baya da ke barin mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi maza da ke tsare wa yakin Sudan su tsallaka iyaka zuwa cikin Masar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon yadda ake samun damfara da masu aikata miyagun laifuka.

    Sama da mutum 200,000 aka kiyasta sun tsallake iyakar zuwa cikin Masar a wata kusan biyu da aka kwashe ana gwabza yaki a Sudan.

  20. Tallafin mai: Jihar Edo ta mayar da ranakun zuwa makaranta sau uku a sati

    Ɗaliban firamare a Jihar Edo

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A makon da ya gabata jihar ta Edo ta rage ranakun aiki zuwa uku a mako

    Gwamnatin Jihar Edo a kudancin Najeriya ta mayar da ranakun zuwa makaranta sau uku a sati da zimmar rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

    Shugabar hukumar ilimin bai-ɗaya ta Edo State Universal Basic Education Board (SUBEB), Ozavize Salami ce ta bayyana hakan a Birnin Benin ranar Juma'a, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.

    An ɗauki matakin ne bayan ganawar da ta yi da sauran hukumomin gwamnatin jihar domin fara aiki da umarnin gwamnati na rage yawan ranakun aiki daga biyar zuwa uku a makon da ya gabata.

    "Game da matakin rage ranakun aiki zuwa uku a sati, mun yi ƙoƙarin mayar da ranakun zuwa makaranta cikin kwana ukun farko na kowane mako," in ji ta.

    Ta ƙara da cewa: "Ba ma son a samu wani tazgaro game da tsarin tafiyarwa. Saboda haka yara za su je makaranta a ranakun Litinin, da Talata, da kuma Laraba a dukkan makarantun firamare.

    "Abin da muka yi shi ne, mun tsawaita lokacin koyarwa da awa ɗaya a firamare da kuma awa biyu a sakandare don tabbatar da cewa an cimma manhajar karatu da aka tsara."