Tinubu ya umurci DSS su fice daga ofishin EFCC

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Umar Mikail

Buɗewa

Assalamu alaikum jama'a barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na BBC da muke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

Ni ne Muhammad Annur Muhammad, zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a wannan rana ta Talata.

Mu fara da wannan karin maganar da ke cewa ; "Komai nisan dare gari zai waye''