Sai da safenku
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don kawo muku sabbin rahotannin.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.
Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe don kawo muku sabbin rahotannin.

Asalin hoton, BAT
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci hukumar tsaro ta DSS su fice daga ofishin hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da ke Ikoyi a jihar Legas.
Dakarun DSS sun yi wa ofisshin EFCC dirar mikiya tare da hana ma'aikatan shiga ofishin a yau Talata. Wasu rahotanni na cewa har an ji karar harbin bindiga a yankin.
Sai dai a wata sanarwa daga mai taimaka wa shugaban ta fannin yada labarai, Tunde Rahman, ya yi kira ga jami'an DSS da su gaggauta barin ofishin.
Sanarwar ta ce: "Shugaban kasa ya ce idan akwai wata matsala tsakanin hukumonin biyu ya kamata a sasanta cikin ruwan sanyi."
Jami'an DSS sun afka ofishin ne suna masu ikirarin cewa su suka mallaki ginin.

Asalin hoton, NNPCL
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL na bin gwamnatin ƙasar bashin naira tiriliyan biyu da biliyan 800 na tallafin man, a cewar shugaban kamfanin Mele Kyari.
Da yake magana a fadar shugaban ƙasa bayan kammala ganawa da Shugaba Bola Tinubu, Kyari ya ce sun yi maraba da jawabin shugaban na cewa tallafin mai ya ƙare.
"Dogayen layuka da aka fara yi a faɗin ƙasa ba abin mamaki ba ne, saboda 'yan kasuwa na son su fahimci ma'anar maganar Tinubu cewa 'tallafin mai ya ƙare'," a cewarsa.
Ya ƙara da cewa biyan kuɗin tallafin, wanda NNPCL ke samarwa, ya hana kamfanin samun ribar da zai zuba a wasu harkokin kasuwancinsa.

Asalin hoton, House
'Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun yaba wa yunƙurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da janye tallafin man fetur.
Sun ɗauki matakin ne bayan gabatar da ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa Jimoh Olajide ya yi a zamanta na yau Talata.
Sakamakon haka ne Majalisar ta nemi 'yan Najeriya da su yi haƙuri tare da yi wa gwamnati addu'a game da matakin.
A ranar Litinin ne - a jawabinsa na rantsuwar kama aiki - Shugaba Tinubu ya ce "tallafin man fetur ya ƙare", yana mai cewa babu tanadin kuɗin a kasafin kuɗi na wata shidan ƙarshe na 2023.
Tuni jawabin nasa ya janyo dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar, inda mutane ke rige-rigen sayen man.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Italiya ta sanar da cimma yarjejeniya da Juventus don kawo karshen zargin badakalar da ta shafi biyan 'yan wasa albashi.
Juventus ta tsaya tsayin daka domin kamo bakin zare kan takaddamar da ke tsakaninta da hukumar, domin ta samu damar fuskantar kakar badi cikin shiri.
Cikin yarjejeniyar da aka kulla, Juventus ta amince za ta biya tarar dala 790,000, kuma babu batun daukaka kara a kotun kararrakin wasanni.
Haka kuma ba za a kara kwashe wa Juventus maki ba bayan da aka karbe maki 10 har karo biyu kan zargin badakalar cinikayyar 'yan wasa.
Saura wasa daya a karkare kakar Serie A ta bana, kuma da wannan hukuncin Juventus tana ta bakwai a teburi da maki 59. Watakila ta samu gurbin Europa Conference League a badi.

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Afirka ta Kudu ta samar da kariya ga jami'an kasashen da za su halarci taron kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke habbaka na BRICKS a birnin Durban, domin shugaba Putin ya samu nutsuwar halartar taron.
A farkon wannan shekarar ne aka gayyaci Shugaban na Rasha domin halartar taron.
To amma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da damar kama shugaban wanda hakan ke nufin ake ganin ya kamata Afirka ta Kudu ta kama shi idan har ya halarci taron.
Ana zargin shugaban na Rasha da laifukan take hakkin dan'Adam a yakin da yake yi da Ukhraine.
Kakakin gwamnatin ya ce, ''za mu canza doka don mu ba kanmu damar hakan kuma babu abin da zai hana mu canza duka dokar a Afirka ta Kudu.''
Afirka ta Kudu dai ba ta soki matakin da Rashar ta dauka ba na mamayar Ukriane tana mai cewa ba za ta mara wa kowane bangare baya ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ce akwai bukatar a kara saka ido domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta yi tasiri saboda yakin yana rutsawa da masu aikin raba abincin.
Hukumar ta ce ta yi nasarar kai tallafi ga wasu mazauna Khartoum da Umm-Durmān a yan kwanakin nan, tun bayan fara yakin, sai dai har yanzu shirin bai kai wasu wuraren ba.
Amurka da Saudiya da suka assasa yarjejeniyar sun ce suna maraba da kara tsawaita yarjeniyar tsagaita wutar ta kwana biyar.
Sai dai sun bayar da tabbacin dokar ba ta yi aiki yadda ya kamata ba.
Bangarori biyu da suke rikici a Sudan din na zargin juna da fara karya yarjejeniyar musamman a yankin Dafur.

Ƴan majalisar dokokin Rasha biyu sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kai wasu hare-hare a kasarsu, bayan harin jirgi marar matuki mafi girma da aka kai wa kasar tun bayan da ta yi wa Ukraine kutse.
An kai harin ne a yanki mafi yawan masu arziki a birnin Moscow, inda aka jikkata mutum biyu.
Daya daga cikin ƴan majalisar ya ce, '' Wannan harin ya nuna karara ramuwar gayyace daga Kyiv ta hare-hare masu tasiri da muka kai masu.''
''Har ila yau hakan ya ba mu tabbacin ci gaba da daukar matakai na musamman da muke dauka domin cimma burin da ke gabanmu,'' in ji shi.
Ukhraine ta ce ba ta da hannu cikin kai harin, amma kuma mai magana da yawun Shugaba Zelensky ya ce sun ji dadin faruwar hakan.

Asalin hoton, SCREEN SHOT/BREKETE FAMILY YOUTUBE VIDEO
Kotun kwadago ta Najeriya ta zartar da hukuncin cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka kan kungiyar Malaman Jami’a na kin biyan mambobinta da suka shiga yajin aiki albashi yana kan doka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban kotun mai shari’a Benedict Kanyip, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da hukuncin, inda ya ce gwamnatin tarayyar tana da ikon rike albashin ma'aikatan da suka shiga yajin aiki.
Sai dai kuma a bangaren tsarin biyan albashi kotun ta zartar da cewa, ya saba wa tsarin ƴancin cin gashin kai na jami'a a tilasta wa malaman shiga tsarin nan na biyan labashi na, IPPIS, saboda malaman suna da ƴancin zabar yadda za a biya su albashinsu.
A ranar 14 ga watan Fabarairu ne ASUU ta shiga yajin aiki, wanda ya kai wata takwas a kan neman kyautata yanayin albashi da inganta tsarin ilimin jami'a da sauran bukatu.
Yajin aikin ya sa daliban kasar da dama zaman gadi yayin da gwamnati ta kafe cewa ba za ta biya malaman albashi ba tsawon lokacin da suka yi yajin aikin.

Asalin hoton, AFP
Dogayen layukan mai sun dawo a gidajen sayar da mai a fadin biranen Najeriya tun bayan da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man.
A jiya Litinin ne Tinubun ya sanar da cire tallafin a jawabinsa na farko bayan rantsuwar kama iaki inda ya ce kasafin ba ya cikin kasafin kudin da ya gada daga gwamnatin Buhari.
Wasu rahotanni na cewa a birane irin su Lagos da Abuja ana sayar da man a wasu wuraren a kan kusan naira 600 a kan lita daya kari daga daga 185 a kan lita a yau Litinin.
Sai dai kuma kamfanin mai na kasar NNPC ya sanar cewa akwai wadataccen mai a kasar saboda haka babu dalilin da zai sa mutane su shiga fargabar sayen man.
Ƴan kasar da dama na kokawa kan yadda suke shafe tsawon lokaci a kan layi domin sayen man.
Tinubu ya ce za a yi amfani da kudin tallafi wanda ya ce a yanzu wasu attajirai ne kawai suke cin moriyarsa, wajen bunkasa wasu fannonin da jama'a za su fi amfana.
Ba a san ko tun daga jawabin nasa gwamnati ta dakatar da tallafin ba kenan.
Masana harkokin tattalin arziki na nuna cewa tasirin cire tallafin zai haddasa tsadar sufuri da kayayyaki.

Asalin hoton, DSS
Jami'an hukumar ƴan sandan ciki ta Najeriya DSS sun yi wa ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa a Lagos dirar-mikiya inda suka hana jami'an na EFCC shiga ofishin a Ikoyi.
Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa daman akwai sabani a tsakanin hukumomin biyu a kan wadda a tsakaninsu ta mallaki ginin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani jami'in DSS ya fada mata bisa sharadin boye sunansa cewa daman sun dade suna takaddama da EFCC a kan wadda ta mallaki ginin, wanda su DSS ne suke amfani da shi tun ma kafin a kirkiri EFCC kuma ya ce an mallaka wa DSS din.
Jami'in ya kara da cewa batu ne da yake a tsakanin hukumomin biyu, kuma bai je gaban shari'a ba sannan ba su taba rikici a kai ba kafin yanzu.
''To amma yanzu ba mu san dalilin da suka zo suka hana jami'anmu shiga ofishin ba, duk da cewa ga sabuwar gwamnati ta zo,'' in ji shi.
Jaridar ta ce duk kokarin ji daga bakin masu magana da yawun hukumomin biyu Wilson Uwujaren na EFCC, da kuma Dr Peter Afunaya na DSS a kan batun bai yi nasara ba.

Asalin hoton, EPA
Rasha ta sake kaddamar da wasu hare-hare da makamai masu linzami a babban birnin Ukraine Kyiv.
An ruwaito cewa an ji karar jiniya da kuma fashewar abubuwa a kusa da birnin da sanyin safiyar yau.
Jami'ai sun ce sojojinsu da ke kare hare haren da ake kai musu ta sama sun mayar da martani.
Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko, ya bayyana hare haren a matsayin munana tare da bukatar mazauna wuraren da su tsaya a wuraren mafaka.

Asalin hoton, Reuters
Wani masanin kimiyya a China ya shaida wa BBC cewa bai kamata a yi watsi da batun asalin inda cutar korona ta bullo ba.
George Gao, ya ce har yanzu ba a yi komai a game da matakin gwamnatin China na watsi da batun cewa daga dakin gwaje-gwajen cutukan kasar ta bullo ba.
Ya ce, ''a kimiyyance dole ka zamo mai karbar shawarwari.''
''Ka kasance kana karbar shawara saboda komai zai iya faruwa. Kada ka dauka komai ba zai iya faruwa ba.''
Masanin kimiyyar shi ne shugaban cibiyar kula da cutuka masu yaduwa na China a lokacin annobar korona.
Har yanzu hukumar lafiya ta duniya ta ce ba ta gano ainihin daga ina cutar ta balla ba.
Yawancin masana kimiyya sun ce akwai yiwuwar cutar ta yadu ne daga wajen dabbobi zuwa mutane a birnin Wuhan na China.
Kididdiga dai ta nuna cewa kusan mutum miliyan bakwai ne suka rasa ransu sakamakon cutar korona, ko da yake ana ganin adadin ya iya zarta hakan.

Gwamnar jihar Borno, Babagana Zulum ya ce za a dauki malamai 5,000 aiki don fara karatun firamare da sakandare da rana domin magance matsololin cunkoso da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Maiduguri yayin jawabinsa na farko bayan rantsar da shi karo na biyu.
Ya ce : "Duk da cewa mun gina sabbin makarantu masu girman gaske tare da fadada makarantun da ake da su da sabbin ajujuwa kusan 1,000, amma har yanzu muna fuskantar matsalar cunkoso a ajujuwa, kuma muna fama da matsalar da dubban yara da ba sa zuwa makaranta"
“Ina mai farin cikin sanar da cewa nan ba da jimawa ba jihar Borno za ta fara tsarin makarantun firamare da sakandare na rana. Na nada kwamitin aiwatarwa da zai tsara hanyoyin da za a fara karatun makarantun la’asar, kuma zai tantance makarantun gwajin da za a zabo daga wasu manyan makarantunmu na Maiduguri da ke da lantarki.”
Zulum ya bayyana cewa bullo da tsarin karatun na yamma zai bukaci karin ma’aikata, don haka ya umurci ofishin shugaban ma’aikata da ya zakulo wasu kwararrun ma’aikatan da a halin yanzu ba sa aiki a sakatariyar gwamnati, wadanda za a horar da su kan sanin makamar aikin.
Gwamnan ya kuma ce za a dauki matakan tsaro domin tabbatar da samun nasarar makarantun na yamma, yana mai cewa a wasu lokutan ana iya daukar darasi har zuwa farkon dare.
Zulum ya ce za a sake bullo da wasu matakai kamar jarrabawar gwaji da ake kira ''Mock'' da Ingilishi a makarantun sakandare tare da kafa cibiyoyi daukar jarrabawa masu inganci ta yadda gwamnati za ta iya gano baiwa da fasihar yaran.

Asalin hoton, Reuters
Amurka da Saudiyya sun yi maraba da tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da dakarun kar-ta-kwana na RSF da kwana biyar.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen biyu masu shiga tsakani a rikicin sun amince cewa yarjejeniyar farko da aka cimma ta kasance ta je-ka-na-yi-ka, to amma duk da haka ta bayar da damar shigar da kayan agaji ga miliyoyin mutane a Sudan din.
Shirin samar da abinci na duniya, ya ce a karon farko ya samu damar aikewa da abinci ga mutanen da suka makale a babban birnin kasar, Khartoum, tun bayan fara yaki a Sudan din.
Rikicin da aka fara tsakanin bangarorin biyu a kan gwagwarmayar kama iko tun wajen mako shida ya tilasta wa jama'a da dama ficewa daga kasar musamman babban birnin sannan ya jefa da dama cikin mawuyacin hali.

Asalin hoton, FACEBOOK
Gwamnatin Bauchi ta ce za ta dauki matasa akalla dubu 20,000 aiki domin yakar matsalar tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, karkashin wata rundunar tsaro da za ta kirkiro ta musamman a jihar.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa rundunar tsaron za ta kasance ne kamar wadda jihohin kudu maso yammacin kasar suka kirkiro wadda ake kira Amotekum.
Gwamnan jihar Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ne ya bayyana matakin jim kadan da sake rantsar da shi a wa'adi na biyu a matsayin gwamnan a jiya Litinin.
Mai sharia Rabi Talatu ce ta rantsar da shi tare da mataimakinsa Mohammed Auwal Jatau a lokacin.
Gwamnan ya ce rundunar wadda za ta taimaka gaya ga tsarin tsaron da tuni ake da shi a kananan hukumomin jihar za ta kunshi matasa 20,000 da za a fara dauka a kashin farko.

Asalin hoton, OTHERS
Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya fara daukar matakan binciken tsohuwar gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje, inda hawansa mulki ke da wuya ya bayar da umarni kan wasu tsauraran matakai.
Daga cikin matakan da ya fara dauka gwamnan ya soke dukkanin cinikin da aka yi na sayar da wasu wurare na gwamnatin jihar
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na bayan rantsuwa gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro a jihar da su je su karbe iko da wadannan wurare da gwamnatin ganduje ta sayar.
Wasu daga cikin wuraren da aka sayar sun hada da filayen makarantu da na masallatai da makabarta da jikin badala da sauransu.
Matakin ba ya tsaya ga kadarorin gwamnati da ke cikin jihar ba ne har ma wadanda suke waje dokar soke cikin ta shafa.
Gwamnan wanda ya kuma sauke dukkanin shugabannin ma'aikatu da hukumomi da kamfanoni na gwamnati nadin siyasa har ma da hukumomin daraktoci na gudanarwa, da ma'aikatu da hukumomi da kamfanoni har da da manyan makarantun jihar ya kara da cewa dukkanin matakan da zai dauka a kwankin da ke tafe zai yi ne da nufin dawo da kima da martabar jihar.