Obasanjo ya buƙaci a soke zaɓen shugaban ƙasa a yankunan da aka yi tashin hankali

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen 2023 da kuma wasu abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da yunkurin ƙona ofishin INEC a Kano

    Zaɓen Najeriya

    Rundunar ƴan sanda a Kano ta ce ta kama mutum huɗu da ake zargi da yunkurin ƙona ofishin hukumar zaɓe a karamar hukumar Takai na jihar.

    A cewar sanarwar da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ta ce ana zargin mutanen huɗu da yunkurin ƙona ofishin na INEC a daidai lokacin da ake sanar da sakamakon zaɓe.

    Sanarwar ta ce ƴan sandan sun samu nasarar kama mutanen ne bayan kai samamen gaggawa tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro.

    Haka ma, ƴan sanda sun ce wasu ƴan bangar siyasa sun kai hari kan ofishin yakin neman zaɓe na jam'iyyar NNPP a karamar hukumar Tudun Wada, inda aka kashe mutum biyu.

  2. Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen jihar Legas

    Ƴan takarar shugaban Najeriya
    Bayanan hoto, Ƴan takarar shugaban Najeriya

    Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a jihar Legas inda hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC take bayyana sakamakon ɗaya bayan ɗaya.

    Legas ce jihar da ta fi kowace a Najeriya yawan waɗanda suka yi rajistar zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a babban zaɓe na shekara ta 2023.

    Saboda haka na ganin sakamakon da zai fito daga jihar zai iya yin tasiri sosai a zaɓen.

    Ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na wasu ƙananan hukumomin jihar Legas da aka bayyana kawo yanzu.

    Karamar hukumar Surulere

    APC 39002

    LP 36923

    NNPP 442

    PDP 2651

    Karamar hukumar Etiosa

    APC 15317

    LP 42388

    NNPP 381

    PDP 3369

    Karamar hukumar Apapa

    APC 15471

    LP 7566

    NNPP 338

    PDP 2997

    Karamar hukumar Ifako Ijaye

    APC 30756

    LP 25437

    NNPP 232

    PDP 3258

    Karamar hukumar Ajeromi Ifelodun

    APC 25938

    LP 35663

    NNPP 436

    PDP 4680

    Karamar hukumar Oshodi - Isolo

    APC 27181

    LP 51020

    NNPP 414

    PDP 3139

    Karamar hukumar Mushin

    APC 40876

    LP 23066

    NNPP 397

    PDP 3403

    Karamar hukumar Amuwo Odofin

    APC 13318

    LP 55547

    NNPP 330

    PDP 2383

    Karamar hukumar Kosofe

    APC 36883

    LP 46554

    NNPP 902

    PDP 4058

    Karamar hukumar Shomolu

    APC 27879

    LP 28936

    NNPP 476

    PDP 3449

  3. Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kwara - INEC

    Bola Ahmed Tinubu
    Bayanan hoto, Bola Ahmed Tinubu

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce jam'iyyar APC ce ta lashe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kwara.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon da ke Ilori.

    Ga kuri'un da manyan jam'iyyu hudu suka samu:

    APC - 263,572

    LP - 31,166

    PDP - 136,909

    NNPP - 3,141

  4. Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Gombe - INEC

    Atiku Abubakar
    Bayanan hoto, Atiku Abubakar

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce jam'iyyar PDP ce ta lashe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Gombe.

    Jami'ar tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar ta Gombe, farfesa Maimuna Waziri ta bayyana sakamakon kamar haka:

    PDP - 319,123

    APC - 146,977

    NNPP - 10,520

    LP - 26,160

    Sauran jam'iyyu - 7,263

    Masu zaɓe da aka yi wa rajista - 1,549,243

    Masu zaɓen da aka tantance - 542,997

    Ƙuri'un da aka kaɗa da kyau - 510,043

    Ƙuri'un da suka lalace - 23,735

    Yawan waɗanda suka kaɗa ƙuri'a - 533,778

  5. Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya na ci gaba da shigowa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakamako na ci gaba da fitowa a zaɓen da ake ganin shi ne mafi zafi a Najeriya tun bayan kawo karshen mulkin soji shekaru 24 da suka wuce.

    A hukumance an sanar da sakamakon jihar Ekiti da ke kudu-maso-yammacin ƙasar, yayin da ake jiran sauran jihohi jihohi 36 da yankin babban birnin tarayyar kasar.

    Dan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ne aka sanar ya samu kuri'u mafi yawa a sakamakon zaben jihar wato Ekiti.

    Amma ya yi wuri sosai a yi hasashen wanda zai lashe zaben na shugaban kasa.

    Kusan masu zabe miliyan 90 suka yanki katin jefa kuri'a a zaben na shekaran-jiya Assabar wanda galibi aka yi cikin tsanaki illa tsaikon da aka samu nan da can.

    Sai dai tsaikon da ake samu wajen sanar da sakamakon ya jawo jita-jita cewa an shirin tafka magudi a zaben kasar wadda a baya ta yi kaurin suna wajen samun magudin zabe da sayen kuri'a.

  6. Barkan mu da warhaka!

    Masu bibiyar mu a wannans shafi na BBC Hausa barka da safiya. Wannan shafi namu zai ci gaba da kawo muku sakamakon zaɓen shugaban Najeriya da na majalisar dokokin tarayya.

    Da fatan za ku kasance da mu a shafin namu tsawon wannan wuni domin kada a bar ku a baya kan abubuwan da suke faruwa.

    Kuma ku je shafukanmu na facebook da tuwita da instagram domin bayyana ra'ayoyinku.