Obasanjo ya buƙaci a soke zaɓen shugaban ƙasa a yankunan da aka yi tashin hankali

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan abubuwan da ke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen 2023 da kuma wasu abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bola Tinubu ya buƙaci magoya bayansa a Legas su kwantar da hankalinsu

    Tinubu

    Asalin hoton, BOLA AHMED TINUBU/FACEBOOK

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al'ummar jihar Legas da su kwantar da hankalinsu sannan su guji duk wani abu da zai iya kaiwa ga karya doka da oda.

    Tinubu ya ce bai kamata mutane su tayar da hankalinsu ba, bayan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Legas ya nuna Jam'iyyar Labour ce ta yi nasara, inda ya ce tsarin dumukuraɗiyya ya bai wa kowa ikon zaɓar abin da yake so.

    Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da Bayo Onanuga, jami'in yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya fitar yau Litinin.

    Tinubu ya kuma bayyana damuwa game da rahotannin tashin hankalin da aka samu a wasu sassan jihar.

    Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce: "Bai kamata a samu tashin hankali ba kasancewar APC ta sha kaye a Legas da tazarar ƙuri'un da ba su taka kara sun karya ba."

    "Dama a tsarin dumukuraɗiyya, za ka yi nasara a wani wajen, ka sha kaye a wasu wuraren. Bai kamata mu kawo naƙasu ga tsarin sanar da sakamakon zaɓen ba," in ji sanarwar.

    A sakamakon wucin-gadi da aka fitar a matakin jiha, INEC ta ce dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya ta LP ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar a Legas ɗin - birni mafi girma a Najeriya.

    Shi ma Gwamnan jihar ta Legas, Babajide Sanwo Olu ya buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu su kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci ba tare da wata fargaba ba.

    Cikin sanarwar da ya fitar yau Litinin, Gwamna Sanwo-Olu ya ce ya umarci hukumomin tabbatar da doka su sa ido domin hana afkuwar rikici a sassan jihar.

    "Na kasance gwamnanku kusan shekara huɗu inda nake fifita zaman lafiya da son juna a tsakanin ƙabilu da mabiya addinai daban-daban ba tare da nuna wani banbanci ba."

    "Mu kwantar da hankalinmu, komai zai tafi lafiya lau. Mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma hakan za mu ci gaba da kasancewa." in ji Babajide Sanwo-Olu.

  2. Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Kaduna

    Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shuagaban ƙasa na jihar Kaduna.

    Ya zuwa yanzu an sanar da sakamako a kananan hukumomi 16 cikin 23 na jihar.

    Wakilin BBC a jihar Yusuf Tijjani ya ruwaito cewa mutane da dama na cikin zaƙuwa na jiran jin sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

    Ya kuma ce an tsaurara matakan tsaro a harabar wajen da ake sanar da sakamakon zaɓen don tabbatar da cewa komai ya tafi lami lafiya.

  3. Atiku ya ci zaɓen shugaban ƙasa a Adamawa

    Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a jiharsa ta Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar ce ta sanar da sakamakon a Yola, babban birnin jihar.

    INEC ɗin ta bayyana cewa Atiku ya ci zaɓe a jihar ne bayan samun kuri'u 417, 611, inda ya buge abokin takararsa na APC wanda ya zo na biyu da kuri'u 182, 881.

    Peter Obi na jam'iyyar Labour ne ya zo na uku da kuri'a 105, 648.

  4. Me ya sa ake samun jinkiri wajen sanar da sakamakon zaɓen Najeriya?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A zaɓukan Najeriya biyu da suka gabata, lokacin da aka fi yin hanzari wajen bayyana wanda ya yi nasara shi ne a rana ta uku bayan zaɓe.

    To amma sakamakon amfani da na'urar aikewa da sakamakon zaɓe da INEC ta ɓullo da ita a zaɓen bana, mutane da dama sun yi tsammanin samun sakamakon da wuri fiye da yadda ake samun sa a baya.

    INEC ta ce ta ɓullo da na'urar ne domin yin abubuwa a fayyace, haka kuma hukumar ta buɗe shafin yanar gizo don karɓar sakamakon domin tabbatar da cewa ba a sauya sakamakon ba.

    To sai dai masu zaɓe da dama sun zargi jami'an INEC da ƙin aika sakamakon rumfunan zaɓe zuwa shafin hukumar na yanar gizo kamar yadda aka tsara.

    Jami'an INEC ɗin dai na ƙorafin cewa rashin intanet ne ya hana su aikawa da sakamakon zaɓen zuwa rumbun adana sakamakon da INEC ɗin ta tanadar.

    Masu zaɓe na ta yaɗa bidiyo da hotunan ma'aikatan INEC da suka ƙi aikawa da sakamakon zaɓen zuwa shafin na INEC.

    Haka kuma an samu rahotonnin hatsaniya a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen a wasu jihohi, inda a ranar Lahadi wasu jam'iyyu suka riƙa kira ga magoya bayansu da su je cibiyoyin domin kare ƙuri'unsu.

  5. Peter Obi ya lashe zaɓe a jihohi 11 da Abuja

  6. Binos Yaroe ya sake lashe kujerar majalisar dattawa ta kudancin Adamawa

    Sakamakn zaɓe

    Asalin hoton, Binos Yaroe/Facebook

    Sanata Binos Dauda Yaroe na jam'iyyar PDP, ya sake lashe kujerar sanata da ke wakiltar kudancin jihar Adamawa a karo na biyu.

    Da ake sanar da sakamakon zaɓen a ofishin tattara sakamakon zaɓen mazaɓar, INEC ta ce Binos ya samu ƙuri'u 146, 407, inda ya buge sauran 'yan takara da ya fafata da su.

    A cewar hukumar zaɓen, ɗan takarar APC Adamu Samaila Numan, shi ne ya zo na biyu da ƙuri'u 94, 828 yayin da ɗan takarar jam'iyyar Labour ya zo na uku da ƙuri'u 9, 444.

  7. Yadda ma'aikatan BBC Hausa ke gudanar da aikin zaɓe a ofishinmu na Abuja

  8. An karɓi sakamakon jihohi huɗu

    zauren tattara sakamakon zaɓen

    A hukumance kawo yanzu, shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihohi huɗu.

    Jihohi huɗun da aka gabatar da sakamakonsu a zauren taron sun haɗar da Ekiti da Kwara da Osun da kuma Ondo.

    Sakamakon dai ya nuna dan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a jihohi uku watau Ekiti da Kwara da kuma Ondo.

    A yayin da shi kuma dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe a jihar Osun.

    An samu hayaniya a cikin zauren tattara sakamakon zaben bayan da wadansu jam'iyyu suka ki amincewa da sakamakon zaben na jihar Ekiti.

    Hukumar INEC ta tafi gajeren hutu sai bayan sa'a daya za ta dawo.

  9. Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Ondo

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana sakamakon zaɓen shuagaban ƙasa na jihar Ondo.

    An bayyana sakamakon ne a ɗakin tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Sakamakon ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu ne ya lashe zaben na Ondo.

    Ga kuri'un da manyan jam'iyyu huɗu suka samu;

    Yawan masu zaɓe da aka tanatance: 571,002

    APC - 369, 924

    LP - 47, 350

    NNPP - 930

    PDP - 115,483

  10. Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na jihar Osun

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar Osun.

    An bayyana sakamakon ne dakin tattara sakamakon zabe da ke Abuja.

    Yawan waɗanda aka tantance don kaɗa kuri'a: 759, 362

    Ga kuri'un da mayan jam'iyyu huɗu suka samu;

    APC 343, 945

    LP - 23, 283

    NNPP - 713

    PDP - 354, 366

  11. Ɗan Ganduje ya faɗi zaɓen ɗan majalisar tarayya

    Umar Abdullahi Ganduje

    Asalin hoton, Gandujiya Online

    Bayanan hoto, Umar Abdullahi Ganduje

    Dan gidan gwamnan jihar Kano Umar Abdullahi Umar, ya faɗi zaɓen dan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Tofa da Rimin Gado.

    Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ce ta bayyana sakamakon ranar Lahadi.

    Dan takarar jam'iyyar NNPP Tijjani Jobe ne ya samu nasara da ƙuri'u 52,456, inda shi kuma Umar ganduje ya samu ƙuri'u 44,809.

  12. PDP ta yi ƙorafi kan sakamakon zaɓen Ekiti

    Senator Dino Melaye

    Asalin hoton, OTHER

    Bayanan hoto, Waklilin PDP a zauren bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Najeriya Senator Dino Melaye

    Wakilin jam'iyyar PDP a dakin tattara sakamakon zaben shugaban ƙasa, Sanata Dino Melaye ya yi ƙorafin cewa an tafka maguɗi a sakamakon zaɓen shuagaban ƙasa na jihar Ekiti.

    Dino Melaye ya yi ƙorafin a gaban shugaban hukumar zaɓe farfesa Mahmood Yakubu, inda ya ce INEC ta sake duba batun kuri'un jihar.

    Melaye ya kuma yi korafin cewa INEC ba ta saka sakamakon zaɓe a cikin rumbun bayananta na intanet.

    Sai dai, farfesa Yakubu ya mayar da martanin cewa alkaluma da wakilin na PDP ya bayyana hukumar bata san da su ba saboda waɗanda ke hannunta sahihahi ne.

    Jam'iyyar PDP ta ce hukumar INEC ta saba wa doka wajen rashin sanya sakamakon zaben shugaban kasa a manhajarta ta intanet.

  13. Sakamakon wasu ƙananan hukumomi a jihar Adamawa

    Yola

    Maiha:

    APC - 7335

    LP - 440

    NNPP - 146

    PDP - 14088

    Gombi:

    APC - 8341

    LP - 2628

    NNPP - 541

    PDP - 21744

    Mubi ta arewa

    APC - 10078

    LP - 12261

    NNPP 1253

    PDP 21528

    Madagali:

    APC - 4935

    LP - 4034

    NNPP-201

    PDP- 18,077

    Michika:

    APC 7062

    LP 6047

    NNPP 177

    PDP 28328

    Jada:

    APC 8479

    LP 984

    NNPP 186

    PDP 28561

    Hong:

    APC 11489

    LP 9532

    NNPP 790

    PDP 24569

    Yola ta arewa

    APC - 15885

    LP - 9925

    NNPP - 584

    PDP - 32136

  14. Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Kaduna

    A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da ke faɗin jihar a cibiyar karɓar sakamakon.

    Ga sakamakon wasu ƙananan hukumomin kamar haka:

    Jaba:

    APC - 3131

    LP - 9,967

    PDP - 8,798

    NNPP - 335

    Kaduna ta Kudu:

    APC - 29596

    LP - 22577

    PDP - 42996

    NNPP - 9124

    Kauru:

    APC - 15,870

    LP - 11,293

    PDP - 19,018

    NNPP - 3,128

    Lere:

    APC - 24695

    LP - 15,568

    PDP - 34,149

    NNPP - 7,264

  15. Peter Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Legas

    Peter Obi
    Bayanan hoto, Peter Obi

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da sakamakon wucin-gadi na zaɓen shugaban ƙasa a jihar Legas, inda ta nuna cewa jam'iyyar Labour, wadda Peter Obi ke yi wa takara ce a kan gaba.

    To amma akwai buƙatar sai hukumar zaɓe ta ƙasa a matakin tarayya ta tabbatar da sakamakon kafin ayyana wanda ya yi nasara.

    Ga yadda hukumar INEC ɗin ta bayyana sakamakon a birnin Legas:

    Masu kaɗa ƙuri'a da aka tantance: 1347152

    APC: 572,606

    LP: 582,454

    NNPP: 8,442

    PDP: 75,750

    Wannan ne sakamakon da INEC za ta kai cibiyar bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Abuja.

  16. Kawu Sumaila ya doke Kabiru Gaya a zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu

    Sakamakon zaɓe

    Asalin hoton, Kawu Sumaila/Facebook

    Hon Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu a majalisar wakilai.

    Da ake sanar da sakamon zaɓen a ofishin tatttara sakamakon zaɓen mazaɓar, INEC ta ce Kawu Sumaila ya yi nasara ne bayan samun kuri'u 319, 857.

    Hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar APC Kabiru Gaya, shi ne ya zo na biyu da kuri'u 192, 518, inda ɗan takarar PDP kuma ya zo na uku da kuri'u 14,880.

  17. Ƴan sanda sun ja hankalin ƴan takarar shugaban ƙasa kan kalaman tayar da hankali

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a Najeriya sun buƙaci ƴan takarar kujerar shugaban ƙasa da su gargaɗi magoya bayansu kan yin kalaman da za su tayar da hankali a daidai lokacin da ƙasar ke jiran sakamakon zaɓe da aka gudanar wanda ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru.

    Ƴan sandan sun kuma gargaɗi 'yan siyasa kan matsa wa hukumar zaɓe kan fitar da sakamakon zaɓe.

    An kuma buƙaci 'yan siyasa da su yi amfani da wannan damar na jiran sakamakon zaɓe da ake yi, wajen bin doka da oda da kuma mutunta kundin tsarin mulki, a cewar sanarwar 'yan sanda.

    Ya zuwa yanzu an sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jiha ɗaya tilo cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Ana ci gaba da tattara sakamako a Akwa Ibom

    Akwa Ibom

    An ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Uyo babban birnin jihar Akwa-Ibom.

    Akwai kananan hukumomi 31 a jihar ta Akwa Ibom kuma jiya Lahadi an sanar da sakamako na kananan hukumomi 23.

    Karamar hukumar Eket:

    APC 4675

    LP 13238

    PDP 9757

    NNPP 315

  19. Sadiq Ango Abdullahi ya lashe zaɓen majalisar wakilai

    Sadiq Ango Abdullahi

    Asalin hoton, Twitter/@sadiqango

    Bayanan hoto, Sadiq Ango Abdullahi

    Sadiq Ango Abdullahi, ɗaya daga cikin mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su bayan kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, ya lashe zaɓen ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

    Tun farko, takarar Sadiq Ango ta ja hankalin al'umma ne bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani a lokacin da yake hannun ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.

    Ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da ƴan bindiga suka sace a lokacin da suka kai wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna hari a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

    Sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa Sadiq, wanda ya yi takara a jam'iyyar PDP, ya samu ƙuri’a 33,616, wanda ke biye masa na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 31,737, sai kuma jam’iyyar NNPP mai ƙuri’a 2,368.

    Ya wallafa a shafinsa na tuwita, lokacin da jami'in hukumar zaɓe ke sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X