Jam'iyyar LP ta yi watsi da yadda ake tattara sakamakon zaben shugaban ƙasa

Asalin hoton, LP
Jami'iyyar Labour Party, ɗaya daga jam'iyyun hamayya a Najeriya a zaben 2023 ta yi watsi da yadda ake tatttara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ake yi a Abuja.
Jam'iyyar ta ce ta yi watsi da sakamakon ne saboda INEC ta gaza wallafa sakamakon mazabu a shafinta na intanet a manhajar iREV kamar yadda ta yi alƙawari.
LP ta sa ayar tambaya kan sahihancin yadda ake karɓar sakamakon zaɓen da cibiyar tattara sakamako ta ƙasa da ke Abuja ke yi.
Ɗan takarar jam'iyyar LP Peter Obi na ɗaya daga ƴan takarar shugaban ƙasa huɗu da ke kan gaba a zaɓen na shugaban ƙasa, kuma tuni ya samu nasara a wasu jihohi, ciki har da Legas, jihar da ɗan takarar APC Bola Tinubu ya fito.










