Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa a nan muke muku sallama tare da fatan haduwa gobe don ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a duniya, kai tsaye.

    Mu kwan lafiya.

  2. Ƴan bindiga sun sako mutum 200 da suka sace a Zamfara

    bandits

    Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun sako sama da mutum 200 bayan sun yi garkuwa da su kwana 20 da suka gabata.

    Sai dai kuma masu garkuwar sun kashe kimanin mutum 28 daga cikin 262 da suka yi garkuwar da su.

    Mutanen da aka sako ɗin yawancin su mazauna ƙauyen garin Randa da ke cikin karamar hukumar mulki ta Maru ce.

    Sun biya kudi naira miliyan shida daga cikin naira milyan 30 da masu garkuwar suka nema su biya.

    Sai dai wadanda aka sako din sun ce ƴan bindigar sun sha alwashin sake sace su idan har ba su biya ragowar miliyan 24 ɗin.

  3. INEC ta gargaɗi masu son sayen ƙuri'u a zaɓukan Najeriya na 2023

    vote buying

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ja kunnen ƴan ƙsar da su guji saye da sayar da ƙuri'a a yayin zaɓukan da ke tafe a farkon shekarar 2023.

    Jaridar Daily Post ta intanet da ta ruwaito INEC a yau, ta ce duk wanda aka kama da laifin zai fuskanci ɗaurin shekara guda a gidan yari da kuma biyan tarar naira 500,000.

    Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan koke-koken da jama'a suka yi na zargin cewa ƴan siyasa na son sayen ƙuri'u a zaɓukan da ke tafe.

    INEC na cikin matsin lambar ganin ta gudanar da sahihin zaɓe marar maguɗi da hana sayen ƙuri'un mutane - wanda yana cikin dalilan da suka sa babban bankin ƙsar ya ce ya ɗauki matakin sauya kuɗaden naira da rage yaɗuwar sabbin kudin don hana wannan ta'asa.

  4. Amurka ta ce ta damu da atisayen da sojojin China ke yi a kusa da Taiwan

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Fadar White House ta ce ta damu da atisayen da sojojin China ke yi a kusa da Taiwan.

    Hukumomin Tsibirin sun ce ce jiragen sama da 70 da marasa matuka na China ne sun ratsa sararin samaniyar Taiwan cikin sa'o'i ashirin da hudu.

    Sanarwar da Amurka ta fitar ta bayyana ayyukan sojin na China a matsayin takalar fada. Washington ta ce za ta ci gaba da taimakawa Taiwan ta fanin tsaronta.

    Beijing ta fusata ne sakamakon amincewar da Shugaba Biden ya yi da wani ƙunshin tallafin tsaro na biliyoyin daloli ga Taiwan.

  5. An gano gawar mutum 25 da matsanancin sanyi ya kashe a New York din Amurka

    Sanyi a Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Tawagar agajin gaggawa a yammacin jihar New York a Amurka sun gano gawarwakin mutum 25 da suka mutu sakamakon mummunan matsanancin sanyi da dusar ƙanƙara a ƙarshen makon nan.

    Galibinsu sun sun mutu ne a cikin a birnin Buffalo da kewayensa.

    An sake yin hasashen samun ƙarin dusar ƙanƙara a can, yayin da dokar hana tuƙi ke ci gaba da aiki.

    Shugaban yankin Erie -- wanda ya hada da Buffalo -- ya ce watakila wannan ne yanayi mafi muni da aka fuskanta a tarihin birnin.

    Jami'an tsaron ƙasar sun kuɓutar da ɗaruruwan mutanen da suka maƙale a cikin motoci da a gidajen da ba su da wutar lantarki.

    Matsanancin sanyin da dusar ƙanƙara da aka gani ya yi sanadin mutuwar mutum kusan 50 a arewa maso gabashin Amurka.

  6. Masu garkuwa sun kashe wasu 'yan gida ɗaya bayan sun karɓi fansar naira miliyan 60

    'yan bindiga

    Asalin hoton, others

    Bayanan hoto, 'Yan bindiga

    Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu 'yan uwan juna su uku tare da wani mai babur bayan da suka karɓi fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Jaridar daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da dajin Garin Dogo a yankin ƙaramar hukumar Lau ranar Lahadi.

    Rahotonni sun ruwaito cewa masu garkuwar sun kama mutanen uku - waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya - inda kuma suka buƙaci naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

    Mahaifin yaran uku wanda mai sana'ar safarar shanu ne ya daidaita da masu garkuwar - waɗanda suka amince zai biya su naira miliyan 60 domin sakin 'ya'yan nasa uku.

    Sai kuma ya ɗauki ɗan achaba tare da bashi kuɗin domin kai wa masu garkuwar a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen nasu, dan sakin 'ya'yan nasa .

    To sai dai bayan kai kuɗin fansar da mai babur ɗin ya yi sai suka kashe shi tare da sauran yaran uku, bayan sun karɓi kudin fansar.

  7. Boko Haram ta kashe makiyaya 17 tare da sace dabbobinsu a Borno

    Boko Haram

    Asalin hoton, Getty Images

    Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe wasu makiyaya 17 tare da sace musu dabbobinsu bayan wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda wata ƙungiyar tsaro ta sa kai ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Rahotonni sun ce mayaƙan Boko Haram ɗin ne suka kai hari kan makiyayan waɗanda ke kiwon dabbobinsu a kusa da ƙauyen Airamne a yankin ƙaramar hukumar Mafa, kamar yadda ƙungiyar tsaro ta sa-kan ta bayyana.

    “17 daga cikin makiyayan ne aka kashe a lokacin artabun, tare da sace duka dabbobinsu'' Kamar yadda shugaban ƙungiyar tsaro ta sa-kai Babakura Kolo ya bayyana.

    “Da fari makiyayan sun turje to amma kasancewa yawan 'yan Boko Haram din - waɗanda ke ɗauke da muggan makamai - ya ninka nasu ya sa suka juya da baya'', in ji Kolo.

    Wani ma'aikacin ƙungiyar tsaro ta sa-kai ya ce mayaƙan na Boko Haram suna ƙaddamar da hare-haren ne daga kusa da dajin Gajiganna, inda suka koma bayan da ƙungiyar ISWAP tare da sojojin Najeriya sun fatattake su daga dajin Sambisa da a baya suka mayar babbar maɓoyarsu.

    ƙungiyar ISWAP ta ɓalle daga cikin ƙungiyar Boko Haram ne a shekarar 2016, inda kuma ta zama babbar ƙungiyar 'yan tayar da ƙayar baya a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

  8. Amurka za ta taimaka wa NDLEA wajen bankaɗo masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi

    Miyagun ƙwayoyi

    Asalin hoton, NDLEA

    Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta na yin wani shiri domin ƙarfafa wa hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta hanyar inganta binciken kimiyya da na sinadarai da kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri.

    A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Femi Baba Femi ya fitar ranar Litinin ya ce taimakon na Amurka na zuwa ne bayan da shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya buƙaci hakan daga hukumomin na Amurka bayan jerin ganawa da ya yi da manyan jami'an Najeriya da na Amurka.

    Baya ga taimako a ɓangaren binciken kimiyya da na sinadaran, gwamnatin ta Amurka ta ce shirin zai taimaka wa hukumar wajen samun hanyoyin tattara bayanan sirri ta hanyar na'urori na zamani.

    Matakin na zuwa ne bayan da wata ƙungiya mai suna Abdul Samad Rabiu Initiative (ASR Africa) ta bayar da kyautar naira miliyan 500 ga hukumar ta NDLEA domin ɗaukar nauyin wasu manyan ayyukan hukumar.

  9. Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, others

    A jamhuriyar Nijar wani jirgin sojin kasar ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka bayan da ya dawo daga wani atisayen soji, lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar sojoji uku.

    Rundunar sojin Nijar ɗin ta tabbatar da mutuwar sojin ƙasar biyu da na Ukraine ɗaya - waɗanda duka ma'aikatan jirgin ne - a lamarin da ya faru a filin jirgin saman birnin Yamai.

    Rahotonni sun ce Jirgin ya dawo daga wani atisayen da ya saba yi a lokacin da ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin na Yamai.

    Kawo yanzu dai hukumomin sojin na Nijar ba su bayyana musabbabin tashin wutar a cikin jirgin ba, sai dai sun ce suna kan gudanar da bincike domin gano musabbabin hakan.

    A cikin wata sanarwa da ministan tsaron ƙasar ya sanya wa hannu a madadin shugaban ƙasar ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan mamatan

  10. Kane ya ci ƙwallo a wasan Premier na farko bayan hutun Kofin Duniya

    Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Kaftin ɗin Ingila Harry Kane ya ci kwallo ɗaya a wasan Premier League na farko tun bayan hutun gasar Kofin Duniya, bayan da ƙungiyarsa ta Tottenham ta tashi wasa 2-2 tsakaninta Brentford.

    Tun da farko dai ƙungiyar ta Brentford ce ta fara cin ƙwallayenta biyu, kafin Tottenham ɗin ta farke a mintuna 25 na ƙarshen wasan.

    A yau ne dai aka dawo daga hutun mako shida da aka yi a gasar ta Premier dan bai wa 'yan wasa damar halartar gasar Kofin Duniya da aka buga a Qatar wadda ƙasar Argentina ta lashe.

    Ƙungiyar Arsenal ce dai ke jan ragamar teburin na Premier League da maki 37 daga wasa 14 da ta buga.

    A yau ne kuma za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar West Ham United a filin wasanta na Emirates.

  11. Koriya ta kudu ta kai hari kan jiragen koriya ta Arewa

    Koriya ta Kudu ta ce ta tura wasu jiragen yaƙi tare da kai harin jiragen yaƙi masu saukar ungulu a matsayin martani ga wasu jirage masara matuka na koriya ta Arewa da suka ratsa sararin samaniyarta

    Ta ce harsasai kusan 100 aka harba amma sun kasa kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen.

    Sojojin Koriya ta Kudu sun tsinkayi jiragen ne da safiyar yau Litinin da suka ratsa kan iyaka, kuma ɗaya daga cikinsu har ya ratso kusa da birnin Seoul babban birnin Koriya ta Kudun.

    Lamarin da ya sa aka rufe wasu manyan filayen jiragen sama guda biyu a birnin.

  12. China na shirin gudanar da atisayen soji a Taiwan

    China

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar tsaron Taiwan ta ce China na ƙaddamar wani atisayen soji mafi girma a cikin ruwa da sararin samaniyar Taiwan.

    Ta ce jiragen sojin saman China 71, ciki har da jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa ne suka shiga yankin Taiwan.

    Yankin Taiwan dai na cin gashin kansa, to sai dai China na kallonsa a matsayin wani lardinta wanda take son mayarwa cikin ƙasarta.

    A 'yan watannin baya-bayan nan dai dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin China ta Taiwan.

    Ko a watan Agustan da ya gabata ma dai China ta bayyana fushinta game da ziyarar da kakakin majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin na Taiwan, ziyara ta farko da wani babban ɗan siyasar Amurka ya taɓa kai wa yankin cikin shekara 25.

    Lamarin da ya sa ta mayar da martani ta hanyar shirya gagarumin atisayen soji a yankunan ruwayen da ke gaɓar Taiwan, tare da rufe hulɗar kasuwanci da tsibirin.

  13. Kano Pillars ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan tsohon ɗan wasanta David Ebuka

    Kano Pillars

    Asalin hoton, Kano Pillars

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars a Najeriya ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan tsohon ɗan wasan gabanta David Ebuka, wanda ya mutu a birnin Makurɗi bayan gajeriyar jinya.

    A saƙon ta'aziyyar da jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar Rilwanu Idris Malikawa ya fitar a madadin muƙaddashin shugaban ƙungiyar, da 'yan wasan ƙungiyar, da sauran ma'aikatan ƙungiyar da magoya bayansu, ya bayyana kaɗuwar ƙungiyar game da rasuwar matashin haziƙin ɗan wasan.

    Mista Malikawa ya ce sunan ɗan wasan zai ci gaba da kasancewa a zuciyar ƙungiyar da magoya bayanta.

    Ebuka ya koma ƙungiyar Kano Pillars ne a shekarar 2019, kuma yana daga cikin 'yan wasan da suka taimaka wa ƙungiyar lashe kofin Aiteo Cup a shekarar 2020.

  14. Ukraine na buƙatar ƙarin Gas da makamai - Zelensky

    Zelenksy

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya umarci ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ta G7 da su samar wa ƙasarsa ƙarin gas da makamai domin taimaka mata kuɓuta daga matsanancin sanyin da ke yin barazana ga rayuwar miliyoyin al'umar ƙasar da ke fama da hare-haren Rasha.

    Sakamakon dusar ƙanƙara da ke ci gaba da sauka a wasu sassan ƙasar da kuma lalala tashar wutar lantarkin ƙasar da Rasha ta yi, mafi yawan al'umar ƙasar na fama matsanancin sanyi sakamakon rashin makamashin da za su ɗumama jikinsu da shi.

    Yayin da yake jawabi ga taron ƙungiyar ta G7 ta bidiyo ranar Litinin, shugaba Zelensky ya ce Ukraine na buƙatar ''kusan cubic miliyan biyu'' na gas a wannan lokacin na hunturu.

    Ya kuma buƙaci ƙasashen da su aika wa Ukraine da ƙarin makamai ciki har da tankokin yaƙi da makaman atilari da makamai masu cin dogon zango.

  15. Mutum 17 sun mutu saboda saukar dusar ƙanƙara a Japan

    dusar ƙanƙara

    Asalin hoton, AP

    Jami'ai a ƙasar Japan sun ce sakamakon yawaitar saukar dusar ƙanƙara a manyan biranen ƙasar ya yi sanadin mutuwar mutum 17 gommai suka jikkata, cikin kwana 10, yayin da dubban gidaje ke fama da rashin wutar lantarki.

    Mafi yawan yankunan yammaci da gundumar Hakkaido da ke arewacin ƙasar na fuskantar yawaitar saukar dusar ƙanƙara a 'yan kwanakin nan.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito cewa akan samu yawan dusar kankara na kusan tsayin mita ɗaya a kowacce rana a wasu garuruwan gundumar Yamagata da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta gargaɗi mazauna yankunan da lamarin ya fi ƙamari da su kauce wa yin tafiye-tafiye bayan da ƙananan motoci suka yi ta maƙalewa cikin dusar ƙanƙara a kan wasu titunan ƙasar.

  16. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori jami'anta bakwai a jihar Imo

    'yan sanda

    Asalin hoton, others

    Rundunar 'yan sandan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta kori jami'anta bakwai waɗanda aka samu da laifukan da suka ƙunshi cutar da al'umma da razanarwa da yi wa jama'a ƙwacen kuɗi, da bincikar wayoyin jama'a ba bisa ƙa'ida ba, tare kuma da saɓa wa umarnin babban Sifeton 'yan sanda na ƙasar kan kyakkyawar mu'amala da sauran al'umma.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Mike Abattam ya fitar, ya ce an kama jami'an ne ranar 8 ga watan Nuwamban 2022 a harabar wani banki da ke birnin Umuahia na jihar Abia, a lokacin da suke tsaka da aikata munanan laifukan karɓar kuɗi a wajen mutanen da ba su aikata wani laifi ba.

    Ya ƙara da cewa an gurfanar da su a gaban kotun Majistare da ke birnin Owerri, inda aka same su da laifi, inda kuma nan take rundunar da kore su daga bakin aiki.

    Mista Abattam ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayar da umarni ga duka shugabannin ofisoshin 'yan sanda da ke faɗin jihar da su tabbatar da cewa sun gargaɗi jami'an da ke aiki a ƙarƙashinsu kan aikata makamancin wannan laifi,.

    Yana mai cewa duk jami'in ɗan sandan da aka samu da hannu a irin wannan laifi to zai fuskanci matakin ladabtarwa.

  17. 'Yan sanda sun kama fitaccen dan bindiga a Kaduna

    Kasurgumin dan fashin

    Asalin hoton, Kaduna Police Force

    Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kama fitaccen ɗan bindiga Bilyaminu Sa'idu a ƙaramar hukumar Zariya.

    Kakakin rundunar, DSP Mohammed Jalige, ya ce 'yan sandan da ke aiki a yankin Tudun Wada Zariya ne suka kama ɗan bindigar yayin da suke samame a Kwarkwaron Manu yankin Basawa inda suka tare wasu mutum biyu a kan babur da ba shi da lamba.

    Ya ƙara da cewa mutanen suna ɗauke da wasu jakunkuna da ake zargin an ɓoye bindigogi.

    Bayan an tare su ne, sai ɗaya daga cikinsu ya yi yunƙurin tserewa lamarin da ya sa aka kama shi.

    An gano bindigogi kirar AK47, da harsasai dari uku da arba'in da wayoyin salula goma da kuma magunguna a cikin jakar.

  18. Matakan kare kai daga haduran ababen hawa a Najeriya

    Bayanan bidiyo, Hira da shugaban hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta Najeriya

    Dauda Ali Biu, muƙaddashin shugaban hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta Najeriya, ya yi bayani game da tsare-tsaren hukumarsa game da yadda za su tunkari lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

    Ya ce hukumar ta fito da ƙarfinta da kayan aikinta ciki har da motoci da babura da motar bayar da taimakon gaggawa domin tunkarar wannan lokaci .

    Ya ƙara da cewa hukumar na da jumullar ma'aikata dubu 25, tare da ma'aikatan sa-kai 11,000, waɗanda a cewarsa duka hukumar ta tura su kan titunan ƙasar domin kiyaye aukuwar haɗura a lokutan bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara.

  19. An kashe mutum uku a harin da Ukraine ta kai sansanin sojin Rasha

    Jirgi

    Asalin hoton, Maxar Technologies/Handout via REUTERS

    Wani jirgi maras matuki na kasar Ukraine ya kai hari kan sansanin jiragen yakin Rasha na Engels da ke kudancin kasar lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku, a cewar Moscow.

    Rahotanni sun ce makaman da ke bayar da kariya a sararin samaniya sun kakkabo jirgin inda ya yi rugu-rugu ya fada kan mutanen lamarin da ya kai ga mutuwarsu da daddare.

    A farkon watan nan Rasha ta zargi Ukraine da kai irin wannan hari a sararin samaniyar yankin da take ajiye jirage masu kai hare-haren bama-bamai wadanda suke kai wa Ukraine hari.

    Sansanin yana da nisan kilomitat 500 daga arewa maso gabashin kan iyakar Ukraine.

    Rundunar sojin Ukraine ba ta yi tsokaci a hukumance game da harin ba amma Editan Sashen Rasha na BBC Steve Rosenberg ya ce harin na baya bayan nan wani abin kunya ne ga Rasha.

  20. Boxing Day: Yadda aka samo sunan ranar washe garin Kirsimeti da asalinta

    Boxing Day

    Asalin hoton, Getty Images

    "Boxing Day" - rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.

    Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben boxing da ake gudanarwa a faɗin duniya.

    Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin akwati kafin su bai wa mabuƙata - 'box' na nufin akwati a harshen Hausa.

    Boxing Day a al'adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu.

    Haka nan, a ranar ce su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.

    Ku danna nan domin karanta cikakken bayani a kan Boxing Day.