An harbe mata uku a wajen shan gahawa a Italiya

Asalin hoton, GIORGIA MELONI/FACEBOOK
Wasu mata uku ciki har da aminiyar sabuwar firaiministar Italiya aka kashe bayan wani mutum ya bude wuta a wani wajen shan gahawa a birnin Rome na Italiya.
An raunata wasu mutum hudu a wajen.
Mutanen da ke cikin wajen na gudanar da taro ne a kan abin da ya shafi unguwarsu a lokacin da mutumin ya bude musu wuta.
Magajin garin Rome, Roberto Gualtieri, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sannan kuma zai kira taron gaggawa a kan lamarin.
Yanzu haka mutumin da ake zargi mai kimanin shekara 57, na tsare kuma rahotanni sun ce dama can yana da matsala tsakaninsa da shugabannin unguwar.
Daya daga cikin wadanda ke halartar taron ta shaida wa manema labarai cewa, mutumin ya shiga wajen ne a ranar Lahadi yana ihu yana cewa " Sai na kashe ku gaba daya" inda daga bisani kuma ya bude wuta da wata 'yar karamar bindiga.
Biyu daga cikin wadanda suka samu raunin mata ne, sauran biyun kuma maza.
Firaminista Giorgia Meloni, ta bayyana daya daga cikin matan da aka kashen Nicoletta Golisano, a matsayin kawarta, sauran matan da aka kashen kuma su ne Elisabetta Silenzi da kuma Sabina Sperandio.


