Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata cewa sojoji sun zubar wa mata ciki a asirce

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta dama wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Bappa

  1. Bankwana

    Da haka ni Umaymah Sani Abdulmumin nake bankwana da ku a wannan shafi da ke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  2. Wani babban jami'in Rasha ya tsallake rijiya da baya a Kherson

    Babban jami'i na biyu mafi girma da Rasha ta nada a yankin Kherson na Ukraine ya tsallake rijiya da baya, bayan yunkurin halaka shi.

    Jami'ai sun ce an tarwatsa morar Vitaly Bulyuk a garin Skadovsk da ke tsakanin Kherson da Crimea.

    A cewar jami'ai, an kashe direbansa, amma Mista Bulyuk yana kwance a asibiti a Crimea cikin wani mummunan yanayi, ko da yake sun ce lamarin da sauki.

    An tilastawa sojojin Rasha janyewa daga birnin Kherson a watan da ya gabata, amma sun ci gaba da rike ikon galibin yankunan kudancin kasar.

  3. Majalisar Turai na nuna damuwa kan wasu mambobinta da ake zargi da karban cin hanci a Qatar

    Shugabar Majalisar Tarayyar Turai ta bayyana fargaba kan wata badakalar da ta kunno kai da ta shafi wasu 'yan majalisa da ake zargin sun karbi cin hanci daga Qatar.

    Shugabar majalisar kenan Roberta Metsola ke cewa za su kaddamar da bincike kan dukkanin hujojin da suka shafi majalisar da ke da alaka da zargin cin hancin.

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce tun da farko yana da matukar muhimmanci a dauki tsauraran matakan yaki da cin hanci da rashawa a hukumar.

    Qatar ta musanta ba da cin hanci ga 'yan majalisar na Turai.

    Tuni aka kama wata yar majalisar Girka a Belgium, yayin da Girka ta toshe asusunta

  4. Matakin CBN na rage yawan hada-hada da kuɗi zai rage barazanar tsaro, in ji matasan Arewa

    Shettima Yerima

    Asalin hoton, Shettima Yerima

    Takaita amfani da takardun kuɗi da Babban Bankin Najeriya wato CBN ke kokarin aiwatarwa zai rage barazanar tsaro a Najeriya, in ji ƙungiyar tuntuɓa ta matasan Arewa.

    Shugaban ƙungiyar, Alhaji Shettima Yerima ya shaida hakan ne a wani taro da suka yi a Abuja, lokacin da yake tsokaci kan matakin bankin na sake wa kuɗin ƙasar fasali da kuma takaita mu'amala da takardar kuɗi.

    Yarima ya ce lura da halin da ake ciki a Najeriya akwai bukatar bijiro da matakan da za su bankaɗo masu rashawa da kuma masu niyyar sayen kuri'un mutane a zaɓen da ke tafe.

    Sannan a cewarsa yana ganin wannan mataki zai kuma kawo ko rage matsalolin tsaro a faɗin Najeriya.

    Batutuwa biyu wato sauya kuɗin kasa da kuma taƙaita kuɗin da za a karɓa daga banki a rana guda ta ATM ko Pos ya ja hankali sosai a Najeriya.

    Yayinda wasu 'yan kasar ke maraba da matakin, galibi sun yi suka inda suke ganin matakin zai fi tasiri kan talaka da 'yan kasuwa.

  5. An kashe wata 'yar Falasdinu a birnin Jenin

    Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce an kashe wata matashiya a wata arangama tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a birnin Jenin da ke gabar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

    An bayyana sunan yarinyar da Jana Zakarna mai shekaru sha shida.

    Kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya ce jami'an Isra'ila sun harbe ta a kai yayin da take tsaye saman gidansu.

    Sojojin Isra'ila sun ce za su binciki lamarin. sun kuma ce kama wasu mutum uku a samamen da suka kai birnin na Jenin, tare da cewa Falasdinawa sun bude masu wuta a yayin farmakin

  6. 'Yan bangar siyasa sun kona ofishin PDP a Gombe

    Jamiyyar PDP mai hammaya a jihar Gombe ta ce wasu da ake zargim yan bangar siyasa sun cina wuta a ofishin yakin neman zaben dan takararta na gwamnan jihar Mohamed Barde da tsakar daren jiya Litinin.

    PDP ta kuma ce wannan ba shi ne karon farko da ake kai wa ofishinta hari ba.

    Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta ce ta soma gudanar da bincike a kan lamarin.

    Babu dai cikakkun bayanai kan harin, amma dai PDP ta zargi APC da wannan hari.

    A sanarwar da ta fitar, Mohammed Barde ya ce sun tafka asara sosai a harin.

    Sai dai babban jami'in yada labaran gwamna mai ci Inuwa Yahaya, ya ce PDP kawai na neman abin tallata kansu ne.

    Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Gombe, ASP Mahid Mu'azu Abubakar, ya ce sun kaddamar da bincike kan lamarin.

  7. 'Yan Najeriya da ke harkar motoci na kuka da jami'an kwastam

    Kwastam

    Asalin hoton, others

    Masu shigo da motoci zuwa Najeriya sun yi zargin cewa jami'an hukumar kwastam a kasar na kama motocin tare da cinsu tara duk da cewa an biya kudin takardu na motocin Tokumbo da ake shigo da su daga kasashen waje.

    Masu motoci da direbobin matocin na zargin cewa wannan takura tafi tsanani ga motocin da ake tafiya da su yankin arewacin kasar.

    Sai dai a martanin da ta mayar, hukumar kwastam ta Najeriya ta ce motocin ba su da cikakkun takardu ko kuma ana shigo da su cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

    Direbobin sun yi zargin cewa jami'an hukumar na kirkiro wasu abubuwa da basu da tushe ballantana makama, inda sukan yi ikirari cewa takardun motocin basu cika ba ko kuma an biya kudi kasa da abinda ya cancanta a biya – wanda sakamakon haka kanzo a rike motocin Takumbon har sai masu motocin sun biya ko kuma a rike su.

    Wannan dai a cewar direbobin, yafi tsanani musanman a kan babbar hanyar daga jihar Legas zuwa yankin arewacin kasar, duk kuwa da cewa motocin suna dauke da cikakkun takardu da biyan kuɗin haraji da ya cancanta a biya ga hukumar.

    Dama dai gwamnatin Naijeriya ta haramta shigo da motoci ta kan tudu wato daga iyakokin kasar da ke makwabtaka da Najeriya kamar jamhuriyar Benin da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

    Najeriya dai kasa ce da kasuwar motocin da aka yi amfani da su a kasashen Turai da aka fi kira Tokumbo ta samu karɓuwa da kusan sama da kashi tamanin daga motocin da ke kasar Tokunbo ne.

    Gwamnatin kasar ta ce za a ke shigo da motoci a kasar ta gabar teku ne kadai dauke da takardu cikakku , wanda duk wani abu sabanin haka ya karya dokar kasar.

  8. Yadda 'yan bindiga suka yi sanadin rayukan mutum 4 a jihar Imo

    Rundunar 'yan sandan jihar Imo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya ta ce akalla mutum 4 suka rasa rayukansu, a wani artabu lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ofishin hukumar zabe ta kasa a garin Owerri.

    'Yan sandar sun nuna gawawaki da wasu kayayaki da 'yan bindigar suka bari bayan musayar wutar.

    A cewar Michael Abattam, mai magana da yawun hukumar 'yan sandar a jihar ta Imo ya ce an kai wannan hari ne da misalin karfe 3 na safiyar litinni,bayan da wasu 'yan bindiga guda goma suka tunkaro cibiyar hukumar zabe ta kasa a garin Owerri babban birnin jihar ta Imo.

    A cikin artabu da kwashi ba dadi da suka wakana tsakanin 'yan sandar da 'yan bindigar, dan sanda daya ya rasu ayayin da mutum uku suka rasa rayukansu daga bangaren 'yan bindigar, akwai kuma mutum guda da ya samu rauni.

    A cewar kakakin 'yan sandar, maharan sun kai harin ne ta hanyar jefa bama-bamai da aka sarafa da fetur a kan rufin hukumar zaben a lokacin da suka zo cikin wasu motoci guda hudu makare da makamai.

    Irin wadannan hare-hare a kan ofisoshin zaɓe na Najeriya ya yawaita a kudancin kasar a wannan lokaci da ake shirye -shiryen gudanar da babban zaben 2023.

  9. Iran ta kakabawa wasu manyan jami'in gwamnatin Jamus da Birtaniya takunkumi

    Iran ta kakabawa wasu manyan jami'in gwamnatin Jamus da Birtaniya takunkumi a matsayin martani ga sabbin takunkuman tarayyar Turai.

    Matakin wanda ya shafi shugabannin leken asirin Birtaniya - ya biyo bayan allawadai da Jamus ta yi da zatar da hukuncin kisa da Iran ta aiwatar kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

    Majid Reza Rahnavard an zartar masa da hukunci ne kan laifin kisan jami'in tsaron Iran guda biyu - inda aka rataye shi a birnin Mashahd a ranar Litinin.

    Rahotanni sun ce an hana shi yancin zabar lauyan da yake so.

    Ministar harakokin wajen Jamus kenan ke cewa takunkunan na EU sun shafi wadanda suka jagoranci zartar masa da hukuncin.

  10. Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata cewa sojoji sun zubar wa mata ciki a asirce

    Lai Mohammed

    Asalin hoton, Nig Govt

    Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton da ke cewa sojoji sun zubar wa mata ciki a asirce a arewa maso gabashin kasar.

    Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya karyata rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar a makon da ya gabata wanda ya ce cikin shekara tara dubban mata ne aka zubar wa ciki a wani shiri na rundunar sojin kasar.

    Rahoton ya ce galibin matan wadanda suka samu juna biyu ne tare da mayakan Boko Haram.

    Reuters ya ce ya tattauna da mata da ‘yan mata da dama wadanda suka bayyana yadda aka yi ba su magani da yi masu allura – kafin daga baya suka fahimci na zubar da ciki ne.

  11. Morocco kun sanya Afirka ta zamo abar alfahari - Muhammadu Buhari

    Dan wasan kwallon kafa

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya taya kasar Morocco murna bisa rawar ganin da ta yi na kasancewarta kasar Afirka ta farko ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da ake a Qatar.

    'Yan wasan na Atlas Lions, sun doke kasashe kamar Belgium da Spaniya da kuma Portugal kafin su kai matakin da suke a yanzu.

    Bisa irin rawar da suka taka a gasar cin kofin duniyar ya sa shugaban Najeriya Muhammadu ya yaba musu tare da cewa sun fitar da Afirka kunya, kuma irin kokarin da suka yi ya sanya fata a zukatan al'ummar nahiyar cewa za su iya daukar kofin.

    Najeriya dai ba ta cikin kasashen Afirka biyar da suka buga wasa a gasar a wannan karon da ake bugawa a Qatar.

    Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, ne ya wallafa sanarwar shugaban kasar a shafinsa na tiwita.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Babu hannuna a kisan kiyashin 2009 - Moussa Dadis Camara

    Moussa Dadis Camara

    Asalin hoton, AFP

    Tsohon shugaban mulkin soja na Guinea Moussa Dadis Camara, ya musanta hannunsa a kisan kiyashin da jami'an tsaro suka yi a shekara ta 2009.

    Ana tuhumar sa tare da wasu tsoffin jami'an soji da na gwamnati 10 kan kisan mutane sama da dari da hamsin da kuma yi wa mata fiye da dari fyade.

    Hakan ya faru ne a cikin wani filin wasan kwallon kafa inda ‘yan adawa ke kokarin gudanar da gangamin siyasa.

    Ana tuhumar Mista Camara ne da laifin daukar nauyin wadanda suka aikata mummunan laifin.

    An soma shari'ar kisan kiyashin a watan Satumba, kuma bayyanar Camara wani muhimmin abu ne ga wadanda suka tsira da rayukansu da kuma dangin wadanda aka kashe.

  13. Malaman Jami'o'i a Ghana sun janye yajin aiki

    Malaman jami'o'in Ghana sun janye yajin aikin da suka soma a watan da ya wuce.

    Kungiyar malaman da ake kira TUTAG wacce ke wakiltar jami'o'in kasar su 10 ta ce ta janye yajin aikin ba tare da wani bata lokaci ba.

    A don haka kungiyar ta yi kira ga malamai su koma bakin aiki daga yau Litinin.

    Malaman sun shiga yajin aiki ne domin a kyautata musu yanayin aiki sannan gwamnati ta kara musu alawus na gyaran mota.

    Yajin aikin ya janyo tsaiko a harkokin ilimi a fadin kasar.

    Shugaban kungiyar ta TUTAG, Farfesa Collins Ameyaw ya shaidawa BBC cewa gwamnati ta ce za ta biya kudin alawus-alawus daga watan Yunin badi.eted for this year.

  14. Sojoji ba su zubar wa mata juna biyu ba - Gwamnatin Najeriya

    Mace mai juna biyu

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton da ke cewa sojoji sun zubar wa mata ciki a asirce a arewa maso gabashin kasar.

    Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya karyata rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar a makon da ya gabata wanda ya ce cikin shekara tara dubban mata ne aka zubar wa ciki a wani shiri na rundunar sojin kasar.

    Rahoton ya ce galibin matan wadanda suka samu juna biyu ne tare da mayakan Boko Haram.

    Reuters ya ce ya tattauna da mata da ‘yan mata da dama wadanda suka bayyana yadda ake ba su magani da yi masu allura – kafin daga baya suka fahimci na zubar da ciki ne.

  15. Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta fara raba katin zabe

    Mutane na karbar katin zabensu

    Ana raba katunan ne a ofisoshin INEC na kananan hukumomi.

    Jama'a na bin layin inda ake raba katin mazaba-mazaba.

    Jami'an INEC na ware katunan kafin su fara rabawa

    Duk mutumin da ya zo karbar katin sai ya gabatar da shaidar cewa ya yi rijista a baya sannan sai a duba sunansa a kundin rijistar zaɓe sai kuma a duba masa katin.

    Idan an sami katin sai kuma a rubuta sunansa ya saka hannu cewa ya karbar.

    Amma da farko sai mutum ya duba sunansa a kundin rijistar da aka yi baja-kolinta a jikin bango.

    Ana duba sunayen wadanda suka yi rijista

    Wadanda ba su ga sunayensu ba a kan ba su wata takarda su cike sannan sai a bukaci su dawo daga baya don karbar katinsu.

    Mutane na jiran a basu katin zabensu
    Katunan zabe

    Za a shafe kwanaki ana wannan aiki na raba katunan zabe a matakin ƙaramar hukuma kafin a koma matakin mazabu.

  16. An dawo da gawar sojan haya dan Zambia da aka kashe a yakin Ukraine Gida

    Lemekhani Nathan

    Asalin hoton, Zambians in Moscow/Facebook

    A ranar Lahadi ne aka dawo da gawar sojar hayar nan dan Zambia da aka kashe a yakin Ukraine gida.

    An kashe Lemekhani Nathan, ne a watan da ya wuce.

    Kungiyar sojojin haya ta Wagner da ke Rasha ta ce ta dauki matashin ne haya daga daya daga cikin gidajen yarinta a inda ya ke zaman daurin rai da rai saboda ta'ammali ta miyagun kwayoyi.

    Wagner ta ce da kanshi ya bukaci shiga cikin kungiyar.

    Gwamnatin Zambia dai ta bukaci a yi mata cikakken bayani a kan mutuwar matashin dan kasarta.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ta rawaito mai magana da yawun iyalan mamacin na cewa an kai gawarsa zuwa dakin ajiye gawa don yin bincike inda daga bisani kuma za a sanar da ranar da za a binne shi.

  17. Karnuka sun yi fareti a Legas

    Mace na sumbatar kare

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito cewa masu karnuka a birnin Legas da ke kudancin Najeriya, sun fito don nuna karnunkansu a wani bikin nuna dabbobi karo na hudu da aka yi a karshen makon da ya wuce a jihar.

    Karnukan da aka zo su wajen sun fito cikin kwalliya bayan an samu kaya masu kyau.

    Kare

    Asalin hoton, Reuters

    Manufar bikin ita ce don a fito a nuna cewa ba gaskiya ba ne cewa 'yan Afirka na gallazawa karnukansu.

    Wadda ta shirya bikin Jackie Idimogu, ta ce " Mun shirya bikin ne don mu fahimtar da mutane cewa karnuka ba wai gadi suke mana ba kawai, a kodayaushe muna tare da su".

    Kare sanye da gilashi

    Asalin hoton, Reuters

    Karya Pasha, wadda ta sanya kaya iri daya da mai ita ta sha gilashi kuma ita ce karyar da lashe kyautar bana a wajen bikin.

    Mace tare da Kare

    Asalin hoton, Reuters

  18. 'Yan siyasa na da hannu a matsalar tsaro a Imo - Uzodinma

    Imo

    Asalin hoton, Uzodinma/Instagram

    Gwamnan jihar Imo a kudancin Najeriya, Hope Uzodinma ya ce harin da aka kai ranar Litinin a babban ofishin INEC da ke Owerri ya nuna cewa akwai hannun 'yan siyasa a matsalar tsaron da ke addabar jihar.

    Da yake jawabi ga manema labarai a shalkwatar 'yan sanda a yau, gwamnan ya ce masu tsatsauran ra'ayi ne suka kai harin.

    "A wannan jihar akwai 'yan siyasar da ke son lashe zabe kota halin kaka ba tare da bin tsari ba," in ji Uzodinma.

    Gwamnan ya kara da cewa " Ina jin dadin aikin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro. Kuma zamu ci gaba da basu goyon baya."

    Uzodinma ya yi alkawarin cewa lamuran tsaro za su inganta kafin bukukuwan kirismeti.

  19. Iran ta kashe mutum na biyu da aka kama da laifin zanga-zanga

    Majidreza Rahnavard

    Asalin hoton, IHRIGHTS

    Iran ta aiwatar kisa kan mutum na biyu a bayyanar jama'a da aka kama da hannu a zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka shafe watanni biyu ana yi.

    Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce, an rataye mutumin mai suna Majid Reza Rahnavard, a birnin Mashhad.

    An same shi da laifin caka wa wasu jami'an tsaro biyu wuka abin da ya yi sanadiyyar rasa rayukansu.

    A ranar Alhamis din data wuce ne aka kashe mutum na farko da aka kama da irin wannan laifin.

    An kashe Majid Reza ne kwanaki 23 bayan an kama shi.

    Wannan mataki na mahukuntan kasar na shan suka daga kasashen yamma.

  20. Mutum uku sun mutu bayan 'yan bindiga sun kai hari a ofishin INEC da ke Imo

    INEC

    Asalin hoton, Daily Trust

    An kaddamar da hari a kan babban ofishin hukumar zaben Najeriya INEC a Owerri babban birnin jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    An kai harin ne da safiyar yau litinin inda rahotanni suka ce 'yan bindiga fiye da 10 suka diranma ofishin.

    Darijar Daily Trust ta wallafa rahoton cewa ofisoshi uku ne suka kama da wuta kafin jami'an tsaro su kai daukin gaggawa inda suka kashe mahara uku.

    Kakakin 'yan sanda a jihar Imo, CSP Mike Abattam ya tabbatar da kai harin amma bai yi wani karin bayani ba.

    "Da safiyar yau litinin 'yan bindiga da ake zargin 'yan Ipob ne sun kai hari a ofishin Inec inda suka wurga bam din da ake hadawa da fetur," in ji Abattam.

    A cikin 'yan watannin nan 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar aware ta IPOB ne suna yawan kai hare-hare a ofisoshin INEC da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    Inec