Mun yi nasara a shari'o'i fiye da 3,000 a 2022 - EFCC
Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Halima Umar Saleh, Haruna Kakangi and Umar Mikail
Sai da safe
Ma'abota BBC Hausa, mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu zo da wasu sababbi kai-tsaye.
Kafin lokacin, ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa a yau Juma'a.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekara 76 da haihuwa
Asalin hoton, @officialABAT
Ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya abokin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 da haihuwa.
A yau Juma'a ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma haifaffen Jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar tasa.
"Ina taya Atiku Abubakar murnar ranar haihuwarsa ta 76," in ji Tinubu cikin wani saƙon Twitter. "Ina yi masa fatan alheri."
Wannan ne karo na shida da Atiku zai yi takarar shugaban ƙasa bayan ya yi rashin nasara a 1993, da 2007, 2011, da 2015, da kuma 2019.
A ranar 25 ga watan Fabarairu mutanen biyu za su fafata a babban zaɓen da 'yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da 'yan majalisar jiha da na tarayya.
NNPC zai samar wa birnin Maiduguri lantarki
Asalin hoton, @HMPowerNG
Ministan Lantarki na Nijeriya Injiniya Abubakar D. Aliyu ya bai wa kamfanin man fetur na ƙasa NNPC Limited lasisin gudanar da sabuwar tashar lantarki mai amfani da gas da za ta samar da megawatt 50 na wuta a Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
Tashar da tuni ake aikin gina ta, za ta ƙara yawan wutar da birnin ke samu musamman bayan matsalolin da aka fuskanta na lalata tashoshin lantarki da ake zargin ƙungiyar Boko Haram da yi.
Yayin miƙa lasisin ga kamfanin NNPC a yau Juma’a a ofishinsa, ministan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen ganin ta kawo karshen matsalar wutar lantarki a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa za ta yi hakan ne ta hanyoyi da suka haɗa da ba da tallafi ga kamfanonin da suke da ƙudirin ba da gudunmawa ta hanyoyin samar da wutar lantarki a duk fadin Nijeriya.
Asalin hoton, @HMPowerNG
Senegal ta ci wasan farko, ta kori Qatar daga Kofin Duniya
Asalin hoton, Getty Images
Masu masaukin baƙi Qatar sun fice daga Gasar Kofin Duniya bayan sun yi rashin nasara a karo na biyu a hannun Senegal.
Ƙasar da ke Gabas ta Tsakiya ta yi bakin ƙoƙarinta amma ta zama tawaga ta farko da ta fice daga gasar tun a zagayen rukuni bayan Netherlands da Ecuador sun yi canjaras 1-1 a nasu wasan na Rukunin A.
A gefe guda kuma, Senegal ta kama ƙasa a rukunin da makinta uku, abin da ya sa ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta ci wasa zuwa yanzu.
Boulaye Dia ne ya fara jefa ƙwallo a ragar masu masaukin baƙin minti huɗu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
An sake sare gwiwar Qatar ne bayan Famara Diedhiou ya ci ƙwallo ta biyu minti uku bayan dawowa daga hutun.
Sai a minti na 78 Muntari ya farke wa Qatar ƙwallo ɗaya amma minti shida a tsakani Dieng ya ƙara ta uku, wadda ta sa masu masaukin baƙin komawa ƙasan teburin rukunin ba tare da maki ko ɗaya ba.
Senegal za ta buga wasa na gaba kuma na ƙarshe a rukuni da Ecuador ranar 29 ga watan Nuwamba.
Wanzamin da ke yi wa 'yan ƙwallon ƙafar duniya aski
Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo
Wani wanzami dan kasar Tunisia da ke zaune a birnin Doha ya yi wa manyan 'yan wasan da ke fafatawa a Gasar cin Kofin Duniya aski.
Houssem Sakka ya bunkasa sana'arsa ne ta a shafin Instagram feeds da kuma amfani da basirarsa ta yin aski. BBC ta tattauna da shi a wurin da yake aski.
Mun yi nasara a shari'o'i fiye da 3,000 a 2022 - EFCC
Asalin hoton, EFCC
Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ta ce ta yi nasara a shari'o'i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin wata 11 na shekarar 2022.
Shugaban hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ƙwace kuɗi naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ƙasa waɗanda suka mayar wa gwamnati.
Kazalika, EFCC ta ƙwace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) - tsohon mataimaki na musamman ga tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki.
"Haka nan, mun yi nasarar ƙwace kadara 40 a Najeriya da Amurka da Landan da Dubai mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu," in ji shi.
Mako biyu da suka wuce, wata kotu ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace wasu kadarori biyu na tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison- Madueke.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Yan sanda na bincike kan kisan abokin sabon sarkin Zulu
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a Afirka ta Kudu suna gudanar da bincike game da kisan kai guda biyu bayan an harbe wani abokin Sarki King Misuzulu ka Zwelithini da mai tsaron lafiyarsa.
Yarima Mbongiseni Zulu, babban dan gidan sarauta ne da ke cikin wadanda suka taimaka wa sarki ya hau kan mulki.
Kakakin rundunar 'yan sandan yankin Jay Naicker ya shaida wa BBC cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kashe mutanen biyu a garin KwaNongoma da ke arewacin KwaZulu-Natal inda suka je domin yin ziyara ga 'yan uwansu.
“Muna gudanar da bincike game da dalilin kisan kuma ba za mu yi shaci-fadi ba kan ko hakan na da nasaba da batun fafutukar hawa mulki,” in ji shi.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce Yarima Zulu shi ne makusanci na uku ga sabon sarkin da aka kashe a watannin baya bayan nan, a yayin da ake ci gaba da bincike kan sauran kashe-kashen da suka faru.
An yi matukar tayar da jijiyar wuya yayin da Sarki Misizulu yake neman darewa kan karagar mulki, inda wasu 'yan gidan sarauta suka kalubalanci nadinsa a matsayin sarki.
An yi yunkurin juyin mulki a Sao Tome and Principe
An dakile wani yunkurin juyin mulki a kasar Sao Tome and Principe.
Firaiminista Patrice Trovoada ya ce mutum hudu sun shiga hedikwatar sojoji yayin wasu mutane rike da bindigogi suka jira a waje.
An kama shugabannin mutanen da suka yi yunkurin juyin mulkin bayan an kwashe awa biyu ana ba-ta-kashi da bindigogi da abubuwan fashewa.
Mr Trovoada ya ce daya daga cikinsu shugaban Majalisar Dokoki mai barin gado kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ne, Delfim Neves.
Dayan kuma tsohon sojan haya ne wanda ya yi yunkurin juyin mulki shekaru 13 da suka gabata.
An kama mataimakin shugaban kasar Malawi bisa zargin cin hanci
Asalin hoton, Getty Images
An kama mataimakin shugaban kasar Malawi Saulos Chilima bisa zarge-zargen cin hanci inda ya karbi na-goro domin bayar da kwangiloli, a cewar hukumar da ke yaki da rashawa ta kasar.
Ana zarginsa da karbar $280,000 (£230,000) daga wurin wani dan kasuwar Birtaniya, a cewar sanarwar da hukumar ta fitar.
Mr Chilima ya bayyana a gaban kotu amma bai ce komai game da zarge-zargen da ake yi masa ba.
Tun a watan Yuni ne aka cire masa dukkan ikon da yake da shi a matsayin mataimakin shugaban kasa a yayin da aka zarge shi da cin hanci.
Mata biyar na rasa rayuwarsu duk awa ɗaya a hannun danginsu - MDD
Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2021, kusan mata da ƴan mata 45,000 ne makusantansu suka kashe.
Idan aka lissafa sosai, za a ga cewa fiye da mace biyar ce makusantansu ke kashewa duk awa ɗaya.
Wani rahoto da hukumomi biyu na Majalisar Dinkin Duniya da suka haɗa da ta yaƙi da shan muggan ƙwayoyi da aikata miyagun laifuka da kuma hukumar mata suka itar, ya fayyace ainihin yadda girman kashe mata yake.
Yankin Asiya ne inda aka fi kashe matan sannan sai Afirka inda aka kashe mata 17,000 a 2021 kuma makusantansu ne suka aikata hakan.
Sai dai nahiyar na fuskantar matsalolin aikata laifuka ne saboda girman yankin da yawan mata da take da shi.
Rahoton na hukumomin MDD ya ce "Mata da ƴan matan Afirka na fuskantar babbar barazanar kisa daga ko dai mazaje ko wasu makusantansu."
MDD ta yi kira ga hukumomi a nahiyar da su kawo ƙarshen irin waɗannan kashe-kashe.
Wani malamin addini a Iran ya ce bai kamata hukumomi su riƙa cin zarafin Ƙurdawa ba
Asalin hoton, Tasnim News Agency
Wani fitaccen malamin addini a Iran ya ce bai kamata jami’an tsaro su riƙa
cin zarafin Ƙurdawan Iran ba.
A khutbarsa ta yau Juma’a a birnin Zahedan, Imam Molavi Abdul Hamid ya ce idan
aka aika mutane gidan yari saboda sukar tsarin siyasa, hakan zai kai ga mulkin
kama-karya.
Malamin mabiyin mazhabar Sunni yana fitowa fili ya soki yadda hukumomi suke
tafiyar da masu zanga-zanga da ta biyo bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun
jami’an tsaro.
Ƴan bindiga sun tafka ɓarna a Birnin Gwari
A Najeriya,
al’ummar ƙauyen Damari da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna na can
suna ƙoƙarin tantance ɓarnar da ƴan bindiga suka tafka a wani hari da suka kai
jiya Alhamis da daddare.
Barnar ta yi sanadiyyar kashe mutum biyar da kuma sace
wasu, waɗanda har yanzu ba a tantance yawansu ba.
Shugaban ƙungiyar
ci gaban masarautar Birnin Gwari, Ishak Usman Kasai ya tabbatar wa BBC cewar ɓarayin
sun shiga ƙauyen ne a wani lamari mai kama da ramuwar gayya bayan artabun da
suka yi a ranar Litinin da wasu, waɗanda ake zargin mayaƙan ƙungiyar Ansaru ne,
waɗanda ke gudanar da lamurransu a yankin.
Ƴan Najeriya miliyan 1.6 ne ke shan ƙwayoyin cutar HIV
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cutar Sida (HIV) a Najeriya ya ce mutanen ƙasar 1.619,133 ke shan magungunan rage raɗaɗin cutar.
A lokacin wata tattaunawa da manema labaru ranar Alhamis, a Abuja, Gambo Aliyu ya ce hakan na nuna irin ci gaban da aka samu a ɓangaren yaƙi da cutar, kasancewar mutum 838,020 ne suke shan maganin a shekarar 2017.
Ya kuma ce yawan masu kamuwa da cutar ya ragu daga 103,404 a 2019 zuwa 92,323 a 2021.
Haka nan ya ce an samu ƙaruwar cibiyoyin kula da masu cutar daga 10 a 2017 zuwa 118 a shekara ta 2021, lamarin da ya sanya ya zuwa 2021 ake kula da sama da mutum 221,010.
Bayanan dai na zuwa ne gabanin ranar yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya ta shekarar 2022.
Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce taken ranar ta wannan shekarar shi ne samar da dama ga kowa wajen kula da kuma kare yaɗuwar cutar.
Ya ce an fitar da taken ne a matsayin wani sabon yunkuri na taƙaita yaɗuwar cutar.
INEC ta wallafa dokokin yin kamfe da na kashe kuɗin jam'iyyu
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta amince da sakin dokokin da suka shafi yaƙin neman zaɓe da yawan kuɗaɗen da ƴan takara da jam'iyyu za su kashe a zaɓen ƙasar da ke tafe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da ilimatarwa kan ƙuri'a na INEC Festus Okoye ya fitar ranar Alhamis, a Abuja.
Okoye ya ce hukumar ta yi taro a ranar ta Alhamis inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka haɗa da wallafa dokokin da suka shafi gangamin yaƙin neman zaɓe, da tarurruka na siyasa da kuma kuɗaɗen da jam'iyyu, da kuma ƴan takara ke kashewa.
Ya ce a yanzu an wallafa bayanai ƙunshi biyu a shafin intanet da shafukan sada zumunta na hukumar, sannan za a raba wa jam'iyyu, da ƴan siyasa, da masu ruwa da tsaki da kuma kafafen yaɗa labaru kwafe-kwafe na bayanan.
Festus Okoye ya kuma tunatar da jam'iyyun siyasa a kan nauyin da ke kansu na miƙa rahoto ga hukumar kamar yadda kundin dokar zaɓe ya tanada.
Ghana za ta fara amfani da zinare wajen sayen man fetur a maimakon kuɗi
Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban ƙasar Ghana Mahamudu Bawumia ya ce gwamnati na duba yiwuwar yadda ƙasar za ta rinƙa amfani da zinare wajen sayen man fetur ɗin da take shigowa da shi ƙasar a maimakon kuɗaɗen waje.
Jaridar Pulse ta ruwaito Bawumia na cewa matakin wani yunƙuri ne na magance faɗuwar da darajar takardar kuɗin ƙasar ke yi babu ƙaƙƙautawa da kuma tashin farashin kaya.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce "gwamnati na tattaunawa kan wani tsari ta yadda za mu rinƙa amfani da zinarenmu (a maimakon dalar Amurka) wajen sayen man fetur."
Jaridar ta ruwaito cewa tsarin zai fara aiki ne a ƙarshen watanni uku na farko na shekarar 2023.
Bawumia ya ce "idan tsarin ya fara aiki, zai rage abin da muke kashewa, sannan zai rage ci gaban faɗuwar darajar kuɗinmu wanda ake alaƙantawa da tashin farashin mai, da ƙarfin lantarki, da ruwa, da sufuri da abinci.
Uba da kaka sun ceto ɗansu ɗan shekara biyar daga bakin mesa
Asalin hoton, Getty Images
Wani yaro ɗan shekara biyar ya sha da ƙyar a wajen wata ƙatuwar mesa da ta cije shi ta nannaɗe shi tare da jan sa cikin kwami wanka.
Mesar ta yi girman yaron mai suna Beau Blake sau uku, kuma ta rutsa shi ne lokacin da yake wanka a cikin kwamin, kamar yadda mahaifinsa ya shaida wa wata kafar yada labaran ƙasar.
Yaron da mesar da kakan yaron da ya shiga don ceto shi sun yi ta kokawa a cikin ruwan - inda daga bisani baban Beau din ya shiga ya fi ƙarfin mesar.
Lamarin ya faru ne a ƙasar Australiya.
Beau dai ya tsira amma ya ji ƙananan raunuka.
Ben ya shaida gidan redioyn cewa mesa ta yi yawa a yankin nasu.
Ana ci gaba da yin tur da kalaman Abdullahi Abbas na "ko da tsiya-tsiya" a Kano
Asalin hoton, Abdullahi Abbas
Ƴan hamayya a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da yin tur da wasu kalamai da ake zargin na haddasa rikici ne da shugaban jam'iyya mai mulki a jihar, ya yi a baya-bayan nan.
Masu sukar na cewa kalaman Abdullahi Abbas na ranar Laraba, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da zaɓe mai zuwa a jihar ta Kano.
Sun ce sun zuba ido ga hukumomi da jami'an tsaro don su ɗauki mataki, saboda gudun faruwar tashin hankali.
Jami'an ƙungiyar agaji ta Red Crescent sun karɓi haihuwar wata mata da naƙuda ta tasar mata a Masallacin Manzon Allah da ke Madina.
Shafin da ke kula da masallatai biyu masu daraja na Saudiyya Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook a yau Juma'a.
Jami'an Red Crescent din sun je ne bayan kiran gaggawa da aka yi musu.
Bayan nan ne kuma sai aka kai mai jegon da jaririnta wani asibiti Jibril Health Center don ci gaba da kula da su.
Mahaifin jaririyar tuni ya raɗa mata suna Taiba, kamar yadda shafin ya ruwaito.
Masallacin da ke cikin mafi tsarki a Indiya ya janye dokar hana mata zuwa ba tare da muharrami ba
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin da ke kula da daya daga cikin masallatai mafiya tsarki da muhimmanci da kuma tarihi a India -- Jamaa Masjid a birnin Delhi, sun janye dokar da suka sanya ta hana duk wata mata da ba ta tare da muharraminta shiga masallacin.
A baya sun sanya dokar ne da cewa yawancin masu ziyarar masallacin suna saɓa martabar wurin.
To amma yanzu sun janye dokar bayan da wani jami'in gwamnati ya bukaci hakan.
Tun da farko wani mai magana da yawun hukumar masallacin ya ce wasu matan da ke zuwa suna fakewa da ziyarar ne,
inda suke haduwa da samarinsu, ko kuma su dauki hotunan bidiyo da suke sanyawa a shafukan sada zumunta da muhawara.
DSS ta ce ba ta janye tuhumar da take yi wa Tukuru Mamu ba
Asalin hoton, Herals
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS, ta ƙaryata batun cewa ta janye ƙarar da take yi wa fitaccen mai shiga tsakani da masu tayar da ƙayar bayan nan, Tukur Mama.
A jiya Alhamis ne wasu kakafen yaɗa labarai suka ce DSS ta janye ƙarar da ta shigar ɗin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na neman ta ci gaba da tsare shi tsawon kwana 60.
Jaridar Daily Trust ta ce labarin da aka fara yaɗawan ya ce lauyan DSS A. M. Danlami, ya shaida wa Mai Shari'a Nkeonye Maha jim kaɗan cewa an janye ƙarar saboda wasu abubuwa da suka taso.
Amma a wata hira da Daily Trust ta yi da mai magana da yawun DSS Peter Afunanya, ya bayyana labarin a matsayin ƙarya ne.
Afunanya ya jaddada cewa hukumar DSS ba ta taɓa janye ƙarar Mamu da ta shigar ba, yana mai cewa ana ci gaba da shari'ar.
Tun a watan Satumba ne DSS ta kama Tukur Mamu, wanda ya suna sosai wajen shiga tsakanin masu satar mutane da dangin waɗanda aka sace.