EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar Ahmad Idris

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Burkina Faso za ta dauki fararen hula domin yakar masu ikirarin jihadi

    ..

    Asalin hoton, afp

    Shugaban mulki sojin Burkina Faso ya kaddamar da wani shiri na daukar dubban fararen hula 'yan sa kai domin taimaka wa kasar yakar masu ikirarin jihadi.

    Jagoran kasar ya ce wannan yunkuri na shirin daukar fararen hula kusan 35,000, zai taimaka wajen kakkabe ayyukan masu ikirarin jihadi a kasar.

    Za a bai wa matasan horon aikin soji na tsawo mako biyu, kafin a rarraba su zuwa sassa daban-daban na kasar, domin gudanar da ayyukansu.

    Sau biyu dai kasar Burkina Faso ta fuskanci juyin mulki a wannan shekara, inda duka shugabanin ke alkawarta kawo karshen tashe-tashen hankula masu alaka da ayyukan masu ikirarin jihadi a kasar.

  2. Za a kara wa shugaban kasa da masu rike da mukaman siyasa albashi a Najeriya

    Buhari Osinbajo

    Asalin hoton, State House

    Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta kasa ta ce ta kammala shiri domin sake duba albashin masu rike da mukaman siyasa, da ma'aikatan shari'a, domin dacewa da halin da kasar ke ciki.

    A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la'akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.

    Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, kama daga shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da kuma albashin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma 'yan majalisun jiha da na tarayya.

    Mista Mbam ya ce hakkin hukumar ne ta tsara albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi da zuwa matakin tarayya.

    Haka kuma sanarwa ta ce aikin hukumar ya shafi zababbu da masu masu rike da mukaman siyasa, ban da albashin sauran ma'aikatan gwamnati, wanda hukumar ta ce ke hannan ma'aikatar tsara albashi ta kasa

    To sai dai kungiyar kwadago ta kasar ta nuna rashin jin dadinta game da matakin, tana mai cewa babu wadanda suka fi cancantar karin albashi a kasar kamar ma'aikatan gwamnati.

    Tana mai cewa a halin yanzu masu rike da mukaman siyasa sun fi kowa samun albashi mai gwabi a kasar.

  3. Ana bukatar daukar matakin gaggawa a gabashin Afirka - MDD

    ..

    Asalin hoton, others

    Shugaban hukumar 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi, ya ce ana bukatar daukar matakin gaggawa a gabashin Afirka, domin tallafa wa wadanda yake-yake da fari suka raba da muhallansu.

    Mista Grandi ya shafe kwanaki 4 a kasashen Kenya da Somalia, inda kusan mutane dubu 500 ne ala tilas suka bar gidajensu a wannan shekarar, yawanci saboda rashin samun zubar ruwa cikin shekaru hudu a jere.

    jami'in na Maja;lisar Dinkin Duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen su yi aiki hannu-da-hannu domin taimaka wa wadannan mutane da ke cikin halin kaka-na-kayi.

    A shekarar da ta gabata, hukumomi a Kenya sun yi barazanar rufe sansanon 'yan gudun hijirar Somalia guda biyu, saboda ba za su iya ci gaba da kula da dubun-dubatar 'yan gudun hijirar da ke wurin ba.

  4. Shugaban Jamus da na Faransa za su gana kan tsamin dangantakar kasashen

    .

    Asalin hoton, ge

    Nan gaba kadan ne shugabannin kasashen Jamus da Faransa za su fara ganawa a birnin Paris, a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke nuna alamun yin tsami.

    An dage taron hadin gwiwa tsakanin 'yan majalisun kasashen biyu wanda a baya aka shirya gudanarwa yau.

    A taron kungiyar Tarayyar Turai a makon da ya wuce, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa Jamus na tsaka mai wuya a kokarin da ta ke yi na kebe kan ta.

    Wannan batu ya janyo guna-guni, da ake dangantakawa da batun farashin iskar gas, da batun dala biliyan 200 da Jamus ta zuba a fannin makamashi domin tallafa wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa da iyalai.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai-tseye muna muku barka da safiyar wannan rana ta Laraba, wadda Hausawa ke yi wa kirari da 'Ta Bawa ranar samu'.

    Ku kasance da mu a wannan shafi na BBC Hausa domin karanta labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Haka kuma kuna iya tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhwara.

    Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar shafin a daidai wannan lokaci.