Bankwana
Da haka muke sallamaku a wannan shafi na labarai kai-tsaye sai kuma gobe da yardar Allah. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umaymah Sani Abdulmumin
Da haka muke sallamaku a wannan shafi na labarai kai-tsaye sai kuma gobe da yardar Allah. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

Asalin hoton, Others
An gudanar da taron waɗanda suka shahara a shafukan sada zumunta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, inda aka tattauna yadda za a shawo kan matsalar yaɗa kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya a intanet yayin da ake tunkarar zaben 2023.
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa CITAD ce ta shirya taron inda ta gayyaci ƙwararru da masu ruwa da tsaki a fannin fasahar sadarwa inda aka gabatar da lakcoci a fannoni daban-daban.
Mutanen da suka yi fice a dandalin sada zumunta da saraun masu ruwa da tsaki a wannan fanni ne aka gayyata wannan taro inda aka gabatar da jawabai iri daban-daban kan yadda za a magance matsalar kalaman ƙiyayya da kuma labaran jabu dangane da zabuka a Najeriya.
Shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere jihar Gombe Farfesa Umar Pate na daga cikin wadanda suka gabatar da maƙala.

Asalin hoton, Aliyu Dahiru Aliyu Facebook
Dr Kole Shatimma shugaban gidauniyar MacArthur a Najeriya ya ce shafukan sada zumunta suna da muhimmanci ga zaben ƙasar don haka yana da kyau a fahimta da masu ta’ammali da su.
Ko me mahalarta wannan taro suka fahimta daga irin jawaban da aka gabatar.
Bayanai na cewa labaran ƙarya da wasu ke yaɗawa a shafukan sada zumunta na ci wa hukumar zabe mai zaman kanta INEC tuwo a ƙwarya, inda rahotanni suka ambato shugaban hukuma na cewa sun tashi haiƙan don yaƙar wannan matsala tun kafin ta haifar musu da cikas.
Shafukan sada zumunta dai, akwai wasu da ake kira sojojin-baka ko kuma ƴan soshiyal midiya wadanda ba su da aiki sai koda dan siyasa da faɗin alherinsa, al’amarin da yake jawo ce-ce-ku-cen da ake ganin ya kamata a rika yin taka tsan-tsan don kada ya haifar da fitina.
Majalisar jam'iyyun siyasa a Najeriya ta amince da matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na amfani da na'urar tantance masu kada ƙuri'a da aka fi sani da BVAS a babban zaben da ke tafe.
A yau ne hukumar zaben ta yi zama da jam'iyyun siyasar, inda ta yi musu bayani a kan shirin da take yi wa zabe.
Honarabul Muhammad Lawan Nalado shi ne shugaban jam'iyyar Accord na kasa, kuma ya yi wa Ibrahim Isa karin bayani a kan batutuwan da suka tattauna:

Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Francis ya yarda cewa akwai malaman coci maza da mata da ke kallon hotunan batsa ta intanet.
A kan haka ya gargade su cewa yin haka abu ne mai hadari.
Shugaban mabiya addinin Kiristan ya ce babu wani nau'in hoton batsa da addini ya yadda a kalla.
A cewarsa ta hakan ne shaiɗan ke samun kafar shiga jikinsu ya karya zuciyoyinsu.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce bayyana bala’in ambaliyar ruwan da aka samu a kasar a zaman wanda ba taba gani ba a tarihinta.
Ministan Albarkatun Ruwa na kasar Injiniya Sulaiman Adamu ne ya sanar da a gaban taron majalisar zartarwar kasar na mako-mako a yau Laraba.
Fiye da mutane 600 ne aka tabbatar sun mutu a hukumance a ambaliyar da ta shafi kashi biyu bisa uku na jihohin kasar 36.
A cewar gwamnatin ta Najeriya, babban musabbabin wannan ibtila’I shi ne saukar ruwan sama fiye da yadda ake zato a daminar bana har ma a yankunan kasar wadanda ga al’ada suke da karancin ruwan sama saboda kusancinsu da hamada.
A nasa jawabin gaban manema labarai ministan ayukkan da gidaje na Najeriyar Babatunde Fashola ya ce ya shaidawa majalisar cewa ambaliyar talalata hanyoyi da gadoji sama ga 150 a duk faɗin kasar abin da ke bukatar zunzurun kudi har Naira biliyan 80 kafin a gyara su:
"Mun samu gano tituna da gadoji 154 da suka lalace wadanda kuma ya kamata a gyara su da gaggawa don ci gaba da amfani da su.
"Kuma kudaden da ayukkan gyaran za su ci a wadannan wuraren kawai sun kai Naira biliyan 80 kuma har yanzu ba mu gama sanin sauran wuraren ba.
"Sakamakon haka muka bai wa manyan jami’na ma’aikatar ayukka ta tarayya da ke jihohi umarnin su fita su tattaro alkaluman sauran hanyoyi da gadojin da suka lalace da kuma irin lalacewar da suka yi.
Don haka yanzu haka ana ci gaba da daukar hotunan da bidiyo wuraren, a halin yanzu muna kan hada rahoto amma dai ba um kare ba. Saboda akwai wuraren da ba su ruwa ba su janye ba dole ne mu jira."
To sakamakon yadda wasu wuraren da ambaliyar ta shafa ke cike cinjim da ruwa har yanzu, ne ya sa ake fargabar barkewar cututuka a can.
To amma ministar harkokin jinkai da kai dauki inda musibbu suka afkawa Hajiya Sadiya Farouk ta ce suna kokarin tunkarar wannan matsalar ita ma.
Ministar dai ta shaidawa majalisar cewa kawo yanzu ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutane 612 yayin da wasu 2776 suka samu raunukka.
Haka kuma ambaliyar ta raba mutum fiye da miliyan 1 da dubu 400 da gidajensu, jimilla dai mutane kimani miliyan 3, da dubu dari biyu, ibtila’i ya shafi idan aka hada da wadanda ambaliyar ta mamaye wa gonaki.
Lebanon ta fara shirinta na mayar da yan gudun hijira daga Syria kasashensu.
Yanzu haka kason farko na mutum 6,000 na kan hanyarsu ta komawa gida.
Gwamnatin Lebanon na fatan ganin ta kai wajejen yan gudun hijira 15,000 a kowane wata.
Rahotanni na cewa kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce Lebanon ta saka Syriyawan cikin hadarin fuskantar cin zarafi idan suka koma gida saboda yaki.
To amma gwamnatin Lebanon ta ce matsin tattalin arzikin da ta ke ciki yasa ba zata iya ci gaba da ajiye yan Syria kusan miliyan daya da rabi ba.

Asalin hoton, EFCC
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar din kasar Ahmad Idris da wasu mutum 3 a gaban wata bababr kotun da ke Abuja kan zargin sama da fadi da kusan naira billiyan 109.
Saura mutum uku sun hada da Olusegun Akindele da Muhamamd Usman da Gezawa Commodity and Exchange limited.
An dai fara gurfanar da wadan da ake zargi a gaban kotun mai shari’a Adeyemi Ajayi a cikin watan Yulin da ya gabata, bisa zargin laifuka 13 da ke da alaƙa da almubazarancin naira biliyan 109, wanda daga bisani aka mayar da shari'ar gaban mai shari'a Yusuf Halilu.
A yayin zama kotun na yau, wadanda ake zargi sun musanta laifukansu.
Hukumar EFCC ta dai yi zargin cewar a tsakanin watan Fabareru zuwa watan Decembar 2021, tsohon akanta janar din, Ahmad Idris ya karbi cin hanci na naira biliyan 15 da miliyan 1 daga hannun Olusegun Akindele, a matsayin karin ƙaimi wajen hanzarata amincewa da biyan kashi 13 ga jihohin 9 na Najeriya da ke da arzikin man fetur, da za a yi ta karkashin ofishin babban akanta janar na kasa.
Haka zalika EFCC ɗin ta kuma zargi Olusegun Akindele da Muhamamd Usman, da karkatar da kimanin naira biliyan 84 daga asusun gwamnatin tarayya, a tsakanin watanin Fabarairu zuwa Nuwamban 2021.
Hukumar EFCC ɗin dai ta ce laifin ya ci karo da sashen 155 da na 315 na kundin manyan laifuka na Penal Code, ta Najeriya na 1990.
Yanzu dai mai shari’a Yusuf halilu ya dage ci gaba da zaman kotun zuwa ranar 23 ga watan Nuwambar 2022, don kara saurararon shari’ar.

Asalin hoton, INEC
Hukumar zabe ta Inec a Najeriya ta ce 'yan kasar miliyan 93.5 ne ke da damar kada kuri'a a zabukan 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida hakan ne a Abuja a wannan Larabar a wani taro da ya gudanar da jam'iyyun siyasa.
Ya ce kawo yanzu 'yan Najeriya miliyan 12.29 ne suka kammala rajistan karbar sabbin katunan zabe, sannan bayan tantacewa sun cire sunayen mutane miliyan 2.78 daga kundinsu.
Jam'iyyun siyasar Najeriya sun nuna jindadinsu da wannan cigaba tare da fatan 'yan kasar da ke da katunan zabe za su fita a fafata da su a babban zaben 2023.
Majalisar Dinkin Duniya na rokon a hada sama da dala miliyan 30 don taimakawa Syria wurin yakar cutar amai da gudawa da ta barke.
Rahotanni sun ce kawo yanzu cutar ta karade ilahirin kasar, kuma ana hasashen ta kama mutum 24,000 ta kuma kashe akalla mutum 80 kawo yanzu.
Majalisar Dinkin Duniyar ta ce dama Syria na fuskantar karancin tsabtataccen ruwan sha, ga kuma mawuyacin halin da tsarin lafiyarta ya shiga tun bayan fara yaki sama da shekaru goma da suka wuce.
Yakin ya haddasa lalacewar magudanun ruwa, ga kuma karancin ruwa sama a kasar.

Asalin hoton, Twitter
Rahotanni daga Iran na cewa jami'an tsaro sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Saqez, mahaifar matashiyar nan Mahsa Amini, da ta mutu hannunsu watan da ya wuce.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Hengaw ta ce da farko an watsa wa masu gangamin hayaki mai sa hawaye, a lokacin da suka taru makabartar Saqez don tunawa da Ms Amini da ta cika kwana 40 da mutuwa.
Rahotannin da ba a tantance ba ma sun ce an shiga yajin aiki a fadin Saqez da wasu birane da ke gundumar Kurdawa.
Masu fafutuka sun ce an gudanar da wata sabuwar zanga zangar a wasu wurare a Iran, ciki har da Jam'iar Tehran, da Mashad da kuma Ahvaz da ke Kudu maso Yammacin kasar.
A cewar Hengaw jami'an tsaron Iran ke da alhakin mutuwar akalla masu bore 140.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar kasar ta yi karin haske game da wani harin soji ta sama da aka a yakin Tillaberi da ke kusa da iyaka da Kasar Burkina Faso.
A cewar sanarwar gwamnatin da ke dauke da saka hannun Ministan Tsaro na kasar, mutum bakwai ne suka mutu, shida nan take a wurin da jirgin ya kai harin guda kuma kan hanyar zuwa asibiti sanadiyar raunukan da ya samu.
Wasu guda 24 sun samu raunuka da yanzu haka suke jiya a wasu asibitoci a garin Sayi da kuma a babban assibittin birnin Yamai.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne bayan da wasu yan ta’adda suka kai hari biyu a jere ranar 22 da kuma 24 na wannan wata.
Abin ya faru a wani shingen tsaro na hadaka da ya ƙunshi ƴan sanda da jami’n tsaron gandun daji da kare muhalli, inda ƴan ta’addar suka kashe ‘yan sanda biyu kuma suka yi awon gaba da wasu kayayaki.
Bayan hakan ta faru ne wani jirgin sojoji ya kwarari ‘yan ta’addar da suka kai harin, har a wani wurin da ake hakar zinariya ba bisa kan ka’ida ba, da ke kusa da garin Tamou daga gabas.
Harin ya yi sanadiyyar rushe rumfuna da dama.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kalli atisayen makaman nukiliya da dakarun da ke kula da makaman nukiliyar kasar suka gudanar, a daidai lokacin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen yamma kan mamayar da kasarsa ke yi wa Ukraine.
Fadar gwamnatin kasar ta ce an harba makaman nukiliyar masu yawa a yankin gabashin kasar.
An sanar wa Amurka game da atisayen, karkashin yarjejeniyar fara atisayen makamai ta duniya.
An gudanar da atisayen ne a daidai lokacin da Rasha ke ikirarin cewa Ukraine na shirin amfani da bom mai dauke da tarin sinadarai masu lahani, zargin da kasashen yamma da dama suka musanta.
Ukraine ta yi gargadin cewa ikirarin da Rashar ta yi, alama ce da ke nuna cewa Rasha na shirin kai irin wannan hari cikin kasarta.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin kasar guda uku.
Ya ce babban bankin ya samu amincewar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin sauya fasalin takartun kuɗi na N200, da N500, da kuma takardar kuɗi ta N1000.
Ya ƙara da cewa sabbin kuɗin za su fara aiki ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe.
Mista mefiele ya ce ''daga yanzu an cire kuɗin da ake karba daga mutane a lokutan da suke zuwa saka kuɗi a banki.
Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar ana hada-hada da su ne ba ta hanyar bankin ba.
Ya ci gaba da cewa wannan mataki zai ƙara wa kuɗin kasar daraja.

Asalin hoton, Getty Images
An kama tare da tsare shugabar kungiya likitocin Turkiyya saboda kiran da ta yi na a gudanar da bincike game da ikirarin da ke cewa sojojin kasar sun yi amfani da makamai masu guba a kan mayakan Kurdawa.
Masu shigar da kara a kasar sun ce ana zargin Sebnem Korur Fincanci da yada farfagandar 'yan ta'adda da kuma cin fuska ga kasar Turkiyya.
Matar mai fafutikar kare hakkin dan adam ta yi ikirarin ne a wata kafar yada labarai da ke goyon bayan Kurdawa.
Kasar Turkiyya dai ta sha musanta amfani da makami mai guba a kan kungiyar 'yan tawayen PKK, wadda tarayyar Turai da Amurka ke kallo a matsayin kungiyar ta'addanci.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da gudunmowar da kungiyar 'yan Najeriya mazauna ketare ke bayarwa wajen daga martabar kasar a kasashen waje, bayan da aka zabi wani dan kasar mai suna Ayo Owodunni a matsayin bakar fata na farko da ya zama kansila a mazabar Kitchener da ke birnin London Ontario na kasar Canada.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce nasarar da mista Owodunni ya samu a wannan zabe mai cike da tarihi, ya nuna karara yadda mutumin yake bullo da tsare-tsare na ci gaba, da goyon bayan 'yan Najeriya mazauna Canada a matsayinsa na mai bayar da shawara da kuma kokarinsa na hada kan 'yan kasar a kasar da yake zaune ta Canada.
Shugaba Buhari ya umarci 'yan kasar mazauna ketare da su kasance jakadun gwamnatin kasar na gari a duk inda suka samu kansu a fadin duniya, ya kuma shawarce su da kada su ji shakkun cimma muradunsu''.
Daga karshe shugaban ya taya mista Owodunni tare da matarsa Folake da kuma yaransu biyu murnar nasarar lashe zaben, wanda ya bayyana a matsayin ''mai matukar muhimmanci'.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƴan majalisa a Ghana na neman a gaggauta sauke ministan kuɗin ƙasar, tare da mataimakinsa saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma faduwar darajar kudin kasar.
Aƙalla ƴan majalisa 80 ne na jam'iyya mai mulkin kasar ta NPP suka gudanar da taron manema labarai ranar Talata, inda suka bukaci tsige jami'an biyu daga mukamansu, saboda zargin rashin iya gudanar da aikinsu.
Zuwa yanzu dai shugaban kasar da ministan ba su ce komai ba kan wadannan zarge-zarge da ake yi wa ministan.
Ƴan majalisar sun yi barazanar ƙaurace wa ayyukan majalisar, kamar tattaunawa game da kasafin kudin kasar na shekarar 2023 da ke tafe.
Wannan na zuwa ne bayan da ƴan majalisar ɓangaren adawa suka gabatar da kudurin tsige jami'an biyu a majalisar dokokin kasar.
Ministan - wanda a yanzu ke kokarin cimma yarjejeniya da asusun bayar da lamuni na duniya, domin karbo wa kasar bashin dala biliyan uku - na fuskantar matsin lamba tun cikin watan Disambar 2021, bayan kirkiro da harajin kashi 1.5 a kan hada-hadar kudi ta waya.
Darajar kudin kasar, wato Cedi, na ci gaba da faduwa, abin da ya haddasa karuwar farashin abinci da tsadar rayuwa a kasar, a yayin da hauhawar farashi ta kai kusan kashi 38 cikin 100.

Asalin hoton, AFP
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Captain Ibrahim Traoré, ya nada ministoci 23.
Sabbin ministocin za su taimaka wa gwamnatin mulkin sojin wurin tafiyar da aiki har zuwa watan Yulin 2024, lokacin da aka tsara mayar da mulki hannun farar hula.
A ranar Juma'a ne dai aka naɗa Apollinaire Joachim Kyelem de Tembela, mai shekarar 64, a matsayin firaministan kasar.
Sabbin waɗanda aka naɗa sun kunshi ministoci biyar na tsohon hamɓararren shugaban mulkin sojin kasar laftanar kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.
Manyan sojoji ne dai suka samu mukaman ministoci a ma'aikatun tsaron kasar.
Sabbin ministocin sun haɗa da mata biyar, ciki har da Olivia Ragnagbnewendé Rouamba wadda aka nada a matsayin ministar harkokin wajen kasar.

Asalin hoton, get
Amurka ta bayar da umurnin fara kwashe wasu ƙananan ma'aikatanta wadanda ba a bukatar aikinsu cikin gaggawa tare da iyalansu daga Najeriya saboda barazanar kai hari.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ne ya tabbatar da hakan a bayanan da yake wallafawa na shawarwari game da ƴan kasar mazauna Najeriya, a ranar Talata.
Sanarwar ta ce ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ba zai iya samar wa 'yan kasar mazauna Najeriya taimakon gaggawar da suke bukata ba, haka kuma ayyuka sun yi wa karamin ofishin da ke birnin Legas yawa.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotonni daga kasar Indonesiya na cewa wata mesa ta kashe tare da hadiye wata mata a lardin Jambi na kasar.
lamarin ya faru ne ranar Lahadi da safe lokacin da matar mai suna Jahrah, mai shekara 50, ta tafi wajen sana'arta ta diban ruwan karo a wani daji da ke bayan gari.
Bayan da iyalanta suka fahimci ba ta dawo ba, sai suka fara nemanta, inda bayan kwana guda wasu mazauna kauyensu suka ga wata mesa mai katon ciki a bayan kwance a bayan kauyen.
Inda nan take suka kashe ta, tare da farka cikinta suka kuma sami gawar matar a cikin mesar.
Shugaban 'yan sandan lardin ya shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa ''an samu gawar matar wadda ta fara kumbura a cikin mesar''.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da mesa ke kashewa tare da hadiye mutane a Indonesiya ba.
A shekarar 2017 da 2018 ma dai an samu irin wadannan rahotonni.

Asalin hoton, gett
Babbar kotun tarraya da ke zama a Umuahia babban birnin jihar Abia ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shugaban kungiyar 'yan aware na IPOB naira miliyan 500 a matsayin diyya.
Mai shari'a Evelyn Anyadike ce ta yanke hukuncin a zaman kotun na yau kan shari'ar da Kanu ya shigar a kan cewar an tilasta dauko shi daga kasar Kenya zuwa Najeriya a watan Yunin 2021, inda ya ce hakan ya saba ka'ida.
A watan Maris ne, lauyoyin Kanu suka shigar da karar a kan cewa matakin gwamnatin Najeriya na dauko shi daga Kenya ba tare da yardarsa ba, an keta masa 'yancinsa.
Kawo yanzu babu martani a hukumance daga wajen gwamnatin Najeriya a kan wannan shari'ar ta yau.
Makonni biyu da suka wuce, kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi wa madugun 'yan awaren, Nnamdi Kanu a wata shari'ar ta daban da aka yi.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce watsi da karar ba yana nufin a saki Kanu daga kurkukuba ne, kuma a cewar gwamnatin akwai shari'u daban-daban da ke tsakaninta da shugaban na IPOB.