Sarki Charles lll ya gana da shugabannin Commonwealth a Fadar Buckingham
Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh, Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya
Masu Alhini na ci gaba ajiye furanni a wurare daban-daban a fadin duniya
Mutane da dama a fadin duniya na ci gaba da bayyana jimamin rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta hanyar ajiye furanni tare mika sakonnin jaje a ofisoshin jakadancin Burtaniya.
Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Bayanan hoto, Masu alhini birnin Washington na kasar Amurka ke ajiye furanni a ofishin jakadancin Burtaniya
Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Bayanan hoto, Nan kuma Cocin St Andrew's Cathedral da ke birnin Sydney na kasar Australiya inda suke ajiye furanni da hoton sarauniyar domin bayyana nasu jimamin
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wata mace kenan ke ajiye furanni a wajen ofinshin jakadancin Burtaniya a birnin Tokyo, na kasar Japan
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani mutum yayin da yake ajiye nasa furen domin nuna juyayi ga mutuwar sarauniyar a birnin Ottawa, na kasar Canada - kasar da sarauniyar ta kwashe shekaru masu dimbin yawa tana mulka.
Ƙasashe rainon Ingila na Commonwealth sun bayyana godiyarsu ga Sarauniya
Sarauniya dai ta kasance mai nuna sha'awarta ga Commonwealth - ƙungiyar da ke ƙunshe da ƙasashe 50 da suka fito daga Daular Burtaniya.
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun bayyana godiyarsu ga jajircewarta da ƙoƙarinta.
Firaministan Indiya, Narendra Modi ya ce ana matuƙar girmamata saboda nutsuwarta.
Gwamnatin Jamaica ta sanar da yin ƙasa-ƙasa da tutocinta a duk gine-ginen gwamnati tsawon kwana 12.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce ƙwazonta abu ne na koyi ga duniya baki ɗaya.
Shi kuwa Firaministan Australia Anthony Albanese ya yaba wa Sarauniyar saboda yadda ta shafe rayuwarta bisa hidimtawa al'umma da iyalinta da kuma addinta.
Ya ce wannan babban rashi ne da ya taba zukatanmu a Australiya, marigayiya Elizabeth ita kadai ce Sarauniyar da akasarinmu muka sani, kuma sarauniyar da ita kadai ta taba zuwa Australiya.
Babban ɗan Sarauniya, Charles ya ce mutuwar mahaifiyarsa abin baƙin ciki ne gare shi
Asalin hoton, PA MEDIA
A yau ne babban ɗan Sarauniya, Charles zai koma birnin London daga Balmoral inda za a ayyana shi a matsayin Sarki a hukumance a Fadar Saint James.
An tabbatar za a riƙa kiran shi a matsayin Sarki Charles na uku wato King Charles the Third.
Cikin wata sanarwa, magajin Sarauniyar ya ce mutuwar mahaifiyarsa abin baƙin ciki ne gare shi da kuma iyalin masarautar.
Shugaba Buhari ya ji baƙin cikin rasuwar Sarauniyar Ingila
Asalin hoton, Getty Images
A saƙonsa na jimami da alhinin rasuwar Sarauniyar
Ingila Elizabeth, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya ji baƙin ciki matuka
da samun labarin mutuwar Sarauniyar.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa
da mai taimaka masa kan yaɗa
labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya Alhamis.
"Ni da iyalaina da al'ummar
Najeriya sama da miliyan 200 duk mun ji takaici sosai na rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkinta na tsawon shekara 70 mai cike da ban
sha'awa da babu irin sa.
“Mulkin marigayiyar shi ne
kadai masarauta mai girma a Turai da kashi 90 cikin 100 na al'ummar duniya a
yau da suka sani.”
Ya ƙara da cewa “a daidai wannan lokaci na jimami
mun bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen
alhinin rashin Sarauniya Elizabeth.
"Muna miƙa ta’aziyyarmu ga illahirin iyalan masarautar
da mutanen ƙasar Birtaniya da ma ɗaukacin ƙasashe Rainon Ingila na (Commonwealth).”
Shugaba Buhari ya ce tarihin
Najeriya a matsayin ƙasa ba zai taɓa kammaluwa ba, ba tare da an
taɓo babin Sarauniya Elizabeth ta biyu ba, shugabar da
zamto tamkar wata bango ga ƙasashen duniya ta
kuma yi fice da shahara.
“Ta sadaukar da rayuwarta wajen
gina ƙasarta da ƙasashe rainon Ingila da ma ƙoƙarin tabbatar da duniya ta zama
waje mai kyau", sanarwar ta ƙara da cewa.
Shugaba Buhari ya yi maraba da
Mai Girma Yarima Charles bisa gadon mulkin da ya yi, ya kuma yi addu'ar ganin
ci gaba da samun ƙarin ingantuwar dangantaka da
alaƙa tsakanin ƙasashen biyu a yayin mulkin
Yarima Charles na III.
Ƙasashen duniya na ci gaba da alhinin rasuwar Saruniyar Ingila
Bayanan hoto, Putin ya ce Sarauniya ta kasance mai mutunta al'ummarta Biden kuma ya bayyana marigayiyar a matsayin mai kishin ƙasa
Ƙasashen duniya da dama na ci gaba da bayyana alhini da jimami na rasuwar Sarauniya Elizabeth da ta fi daɗewa kan karaga a Burtaniya.
Ta rasu ne jiya Alhamis tana da shekara 96. An yi ƙasa-ƙasa da tutoci a Amurka yayin da Shugaba Joe Biden ya bayyana marigayiyar a matsayin mai kishin ƙasa da tsayuwar daka.
Cikin dare kuma, an kashe fitilu a Hasumiyar Eiffel da ke Paris. Shugaba Macron ya ce zai tuna da ita a matsayin ƙawar Faransa.
Shi ma Shugaban Jamus yana bayyana Sarauniyar a matsayin wadda ta ba da gudummowa a wannan ƙarni.
Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya ce ta kasance mai mutunta al'ummarta.
Shi kuwa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce mutuwar Sarauniya Elizabeth gagarumin rashi ne ga duniya baki ɗaya.
Buɗewa
Asalin hoton, PACEMAKER
Masu bin wannan shafi na BBC Hausa assalamu alaikum, barkanmu da safiyar Juma'a.
Kamar yadda kuka sani dai a jiya Alhamis ne Fadar Buckingham ta Birtaniya ta sanar da rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth II, tana mai cewa Sarauniyar ta rasu ne salin-alin a gidanta da ke Balmoral.
A yau wannan shafi da zai mayar da hankali ne kacokan wajen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniyar.