Sarki Charles lll ya gana da shugabannin Commonwealth a Fadar Buckingham
Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh, Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya
An karanto sanarwar naɗin Sarki Charles III a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Landan.
An karanto sanarwar naɗin Charles III a matsayin Sabon Sarkin Ingila a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Landan.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan sanarwar farko da aka karanto a Fadar St James..
Masu busa kakaki na ƙasar Ingila ne suka jagoranci wani ɗan ƙwarya-ƙaryar fareti kafin karanto sanarwar.
Cikin waɗanda suka halarci sanarwar har da Magajin Garin Landan da kuma wasu ma'aikata na biranen ƙasar.
Ra'ayi Riga: Rasuwar Sarauniya Elizabeth II
Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren wannan shirin
An harba bindiga a Hyde Park da Hasumiyyar London domin shaida naɗin sabon sarkin
Asalin hoton, Getty Images
An rinƙa harba bindiga bayan sanar da naɗin sabon sarkin Ingila.
Sojojin Ingila sun yi harbi sau 41 a Hyde Park haka kuma aka yi wani harbin sau 62 a hasumiyyar London domin shaida naɗin sabon sarki.
Yadda aka rinƙa busa kakaki bayan naɗa Sarki Charles
Asalin hoton, PA Media
Ranar jana'izar Sarauniya Elizabeth za ta kasance ranar hutu a Birtaniya
Ɗaya daga cikin abubuwan da sabon sarki ya bayar da umarni shi ne za a bayar da hutu a ranar da za a yi jana'izar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Labarai da dumi-dumi, Sarki Charles III na jawabi
Asalin hoton, PA Media
Sabon Sarki Charles III ya sanar da rasuwar "mahaifiyarsa wadda yake ƙauna, Sarauniya".
"Duniya baki ɗaya na taya ni alhini kan babban rashin da duka muka yi."
Ana saka hannu kan sanarwar naɗin sabon sarki
Mahalarta taron naɗin sarautar na ci gaba da saka hannu kan sanarwar da aka karanta ta naɗa Sarki Charles III.
Yarima William da Firaiminista Liz Truss da kuma Shugaban Cocin Ingila Justin Welby na tsaye suna kallo yayin da ake sa hannun.
Bayan an kammala sa hannun, abu na gaba shi ne za a karanta sanarwar naɗa Charles sabon sarki a hukumance a London da Edinburgh da Cardiff da kuma Belfast inda kuma za a soma harba bindigogi a Hyde Park da kuma hasumiyar Landan da zarar an naɗa sabon sarkin.
A halin yanzu waɗanda suka halarci naɗin za su tafi domin su gaida sabon sarki.
Asalin hoton, PA Media
Labarai da dumi-dumi, Ana karanta sanarwa- Charles III ya zama Sabon Sarkin Ingila
Ana karanta sanarwa: Yarima Charles Philip Arthur George ya zama Charles III
Asalin hoton, PA Media
Masu naɗin Sarki a Ingila sun taru domin naɗa Charles III
Masu naɗin sarki a Ingila da suka haɗa da wasu daga cikin mambobin Gidan Sarautar Birtaniya da Firaiminista da wasu manyan ƴan siyasa da kuma Shugaban Cocin Ingila duk a yanzu haka sun taru a Fadar St James da ke London domin naɗin Charles III.
Jama'a sun soma hallara wurin naɗin Sarki Charles III
Asalin hoton, PA Media
Manyan baƙi musamman ministoci da ƴan majalisu na Birtaniya sun soma hallara Fadar St James da ke birnin London.
Firaiministar Birtaniya Liz Truss wadda marigayiya Sarauniya Elizabeth ta naɗa a makon nan, ita ma ta isa fadar.
A harabar, fadar, akwai ƴan sanda wasu ɗauke da makamai wasu kuma suna tsaye kuma ƴan jarida ma sun hallara domin watsa labarai.
Nan da lokaci kaɗan ake sa ran za a yi wannan naɗi.
An soma shirye-shiryen tarbar akwatin gawar Sarauniya Elizabeth a Edinburgh
Asalin hoton, PA Media
An soma shirye-shryen tarbar akwatin gawar Sarauniya Elizabeth a Edinburgh, babban birnin yankin Scotland.
An rufe hanyoyi ana kuma kafa shingaye.
Ana sa ran ɗauke akwatin gawar daga Fadar Balmoral inda ta mutu zuwa Fadar Holyroodhouse da ke Edinburgh gobe Lahadi.
Bayan nan kuma ana sa ran za a ƙyale jama'a su kafa layi da ya bi ta gefen akwatin a Cocin St Giles Cathedral da ke babban birnin Scotland kafin a tafi da akwatin zuwa birnin London ranar Talata.
Abubuwan da ake sa ran za su faru yau a Birtaniya
10am: Za a naɗa Charles III a matsayin sarki a Fadar St James da ke birnin London. Manyan ministoci 200, inda 14 daga masarauta da kuma waɗanda ke riƙe da ofisoshin jihohi - kamar tsofaffin ministoci da ƴan majalisar wakilai za su halarci naɗin.
Matar Sarki Charles, Camilla za ta raka shi, haka kuma magajinshi William ma zai halarci bikin.
11am: Daga barandar fadar za a sanar da jama'a naɗin. Za kuma a harba bindigogi a Hyde Park.
12pm: Za kuma a karanto sanarwar a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta London.
Da rana: Manyan ƴan majalisar Birtaniya za su yi mubaya'a ga Sarki Charles III a majalisun ƙasar.
Yau za a naɗa Charles III a matsayin sabon Sarkin Ingila
Asalin hoton, PA Media
Nan da ƴan sa'oi masu zuwa ne ake sa ran naɗa Sarki Charles na uku a matsayin sabon Sarkin Ingila a wani biki da za a gudanar a Fadar St James da ke birnin London.
Majalisar naɗa sarki za ta hallara a Fadar St James da safiyar yau kuma za ta tabbatar da Charles a matsayin Sarki.
Babban ɗan marigayiya Sarauniya Elizabeth ya zama Sarki kai tsaye ne tun bayan rasuwarta amma majalisar za ta tabbatar da matsayinsa a wani taro mai cike da tarihi da za a yaɗa ta Talabijin a karon farko.
Manyan ministoci da magajin Sarki Charles wato Yarima William za su halarci wajen.
Za kuma a fara ayyana Charles a matsayin Sarki a fadar sannan a bayyana shi gaban jama'a a London.
Barkanmu da safiya
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Jama'a barkanmu da safiyar Asabar, 10 ga watan Satumbar 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye musamman kan yadda ake ci gaba da alhinin rasuwar Sarauniya Elizabeth da kuma batun naɗin ɗanta Charles a matsayin sabon sarki.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko
kuma na Instagram domin
bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a
kai.
Rufewa
Anan muka kawo karshen shafin da mu ke kawo muku labarai da rahotanni, kan rasuwa da makokin da ake ciki na rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa da wasu sabbin rahotannin, da halin da ake ciki a Birtaniya, da sauran kasashe.
Badriyya Tijjani Kalarawi, ke muku fatan alkhairi.
Mun gode.
Me zai faru gobe?
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Za a ci gaba da makokin rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II
Ranar za ta kasance mai alhini ga yawancin mutane. Tituna da wuraren shakatawa da ke kewayen Fadar Buckingham da Windsor da Balmoral inda Sarauniyar ta rasu, za su cika da jama'a, dauke da furanni da wasikun ta'aziyya da za su dinga ajiyewa a gaban fadar.
Me zai faru a ranar asabar?
Da misalin karfe 10 na safiya agogon kasar, a hukumance za a ayyana Charles a matsayin sabon Sarki, inda za a yi a St James a birnin Landan, inda dan shi Yarima William zai take masa baya
Karfe 11 za a sanar da al'umar Birtaniya sabon Sarkinsu ta barandar St James.
Karfe12 za a sanar da sauyin da aka samu ga daukacin al'ummar daga birnin Landan, da tsakar rana kuma za a sanar a Scotland, sai kuma Arewacin Ireland da Wales
Za a maida tutar Birtaniya yadda ta ke, na tsahon awa 26, hakan ke tabbatar da an nada sabon sarki, bayan nan sai a maida su kasa kamar yadda aka yi tun rasuwar Sarauniya, za su kasance haka har zuwa ranakun zaman makoki
Tsakanin karfe 2 zuwa 10 na dare, 'yan majalisar Birtaniya za su hallara domin girmamawa ga marigayiya Sarauniya
An sauya taken kasa zuwa Allah ya ja zamanin Sarki
Ya yin da Sarauniya
ta rasu, Sarki Charles na III, ya zama sabon Sarki, nan da nan aka sauya taken
kasar ta Birtaniya, inda aka cire wasu daga cikin kalmomi da maye guirbinsu da sabbi.
Za a daina fadar ‘’Allah ya ja zamanin Sarauniya’’, a koma fadar ‘’Allah ya ja
zamanin Sarki’’.
Rabon da aji
kalmomin Allah ya ja zamanin Sarki’’ tun bayan nadin Sarauniya Elizabeth, bayan
rasuwar mahaifinta da hawanta karagar Mulki a shekarar 1952.
Tun da Yarima mai
jiran gado namiji ne, za a dade ana amfani da ‘’Allah ya taimaki Sarki,’’
shekaru da dama masu zuwa.
Babu dai wani
bayani a hukumance kan na ainahin wanda ya fara kirkirar sanya sunan Allah ya
ja zamanin Sarki a taken Birtaniya.
Abu muhimmi shi ne
an fara amfani da ita a karni na 18.
Yarima William zai gaji sarautar babansa ta Yariman Wales
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Sabon Yarima da Gimbiyar Wales
Sarki Charles III ya ce dansa Yarima William zai gaji sarautarsa ta Yariman Wales.
A jawabin da ya gabatar ga 'yan kasa a karon farko bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth.
"A matsayinsa na magajina, a yanzu William zai gaji sarautar da na bari ta Scotland, wadda nake alfahari da ita," in ji shi.
"Zai gaji sarautata ta Duke din Cornwall, zai fara aiki karkashin sarautar da nake kanta sama da shekaru 50.
"A yau, Ina alfahari da zan mika wa dana sarautar Yariman Wales, wadda ta kasance daya daga cikin abubuwan da nake alfahari da su.
"Na tabbatar kasancewar mai dakinsa Catherine tare da shi, Sabon Yarima da Gimbiyar Wales za su ci gaba da gudanar da ayyukan bai wa matasa gwiwa da tattauna batutuwan da suka shafi kasa."
Mai dakinsa Catherineza ta zama Gimbiyar Wales ta farko tun bayan rasuwar mahaifiyar William Gimbiya Diana a shekarar 1997.
Bisa al’adar Yariman yankin Wales ne kadai ke sarautar, amma bayan Sarki Edward I ya mamaye Wales a karni na 13, babban dansa ya fara sarautar Yariman Wales a wani biki da da aka yi Fadar Caernarfon.
Tun daga lokacin yawancin Sarakunan Birtaniya, suka fara bai wa manyan 'ya'yansu da za su gaji wannan sarauta ta Wales. Hakan ta kasance ga Sarauniya Elizabeth ta II, tana da danta Yarima Charles, matarsa kuma ta zama Gimbiyar Wales a shekarar 1969, wadda aka haskawa miliyoyin mutane ta gidan talbijin.
Sarki Salman: Shugabar da ba za a taba mantawa da ita a tarihi ba
Asalin hoton, others
Bayanan hoto, Sarki Salman da Sarauniya Elizabeth ta II, sun gana a Fadar Buckingham 28 ga watan Yuni 2000
Sarki Salman bin Abdul'azeez al-Sa'ud na masarautar Saudiyya ya aike da sakon ta'aziyya da jimami ga Sarki Charles III, da daukacin al'ummar Birtaniya da Arewacin Ireland kan rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II.
Jaridar Saudi Gazzete ta rawaito cewa, Sarki Salman na cike da alhini da bakin ciki gane da wannan rashin da duniya ta yi na shugaba ta gari.
Sarkin Saudiyyar ya ce: “Mun samu labarin wannan babban rashin na rasuwar Sarauniya Queen Elizabeth ta. Daya ce daga cikin shugabanni masu tafiya da zamani, da ba za a taba mantawa da ita a tarihi ba. Ba za mu manta irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninmu, da abota, da aiki tsatakanin kasashenmu. Mu na mika sakon ta'aziyya ga daukacin masarautar Birtaniya da al'ummar kasar baki daya.''
Shi ma Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, kuma mukaddashin Firaiminista, Mohammed bin Salman, ya bi sauran fitattun mutane na duniya, wajen aike da sakon ta'aziyyar rasuwar sarauniya Elizabeth II ga Sarki Charles na III, da Birtaniya.
Jaridar Saudi Gazzete ta ambato Yarima MBC na cewa: “Na yi bakin ciki da shiga damuwa lokacin da labarin rasuwar Sarauniya Queen Elizabeth II ya riske mu, hakika mace ce da ta sadaukar da rayuwarta ga aikin al'umarta, mace mai son zaman lafiya da yada kauna tsananin al'umma.
"Ta kasance jakadiyar zaman lafiya, mai tarin basira da kaifin tunani. A yau duniya za ta tuna da ayyukan alkhairi da ta aikata a lokacin da ta na raye. Muna taya maasarautar Birtaniya, al'ummar kasar da Sarki charles jimamain wannan rashi.''
Wanne irin Sarki Charles zai zama?
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Sabon sarki Charles na III
A daidai lokacin da Sarauniya ta rasu, nan da nan danta Charles, wanda tsohon Yariman Wales, ne ya zama Sarki.
To amma wanne irin Sarki ake sa ran Charles na III zai zama?
A yayin da yake matsayi na Yarima, Charles ya saba da yin tsokaci kan batutuwa da dama, amma a yanzu da yake matsayin Sarki wannan ya kau, ba zai sake mallakar fasfo dinsa na tafiye-tafiye ba, da katin shaidar tukin mota. Ba zai kara fitowa bainar jama'a a kashin kansa kamar lokacin yana Yariman Wales ba.
"Ni ba sakarai ba ne. Na fahimci lamari ne na daban na wata nahiya," kalamansa kenan a wata hira da BBC a shekarar 2018.
Kusan an san Charles zai so sassaukar masarauta. Da alama wannan gagarumin abu ne da ya kunshi tsirarun mutane a masarautar, hakan za ta sama daga Charles, sai Camilla, da Yaruima William da maidakinsa Catherine.
Zai zauna cikin nustuwa da hutawa, fitaccen mutumin da kowa zai so yin magana da shi idan ya fito bainar jama'a, babu cudanya da mutane sosai, babu yin raha barkatai. Lokacin yana Yariman Wales, ya kasance abin soyuwa ga jikokinsa, har abin nan na ''jika mayata kaka'' jikokinsa ke yi da shi amma cikin girmamawa.
Amma ga mutumin da ya haura shekara 70, da alama babu wani sassauci na kama aikin Sarki gadan-gadan.