Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Umar Mikail, Umaymah Sani Abdulmumin, Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya
Labarai da dumi-dumi, Sanata Ajayi Boroffice ya janye wa Bola Tinubu
Sanata Ajayi Boroffice ya janye wa Bola Tinubu.
Shi ne ɗan takara na shida da ya janye wa Tinubu yayin da ake shirin kaɗa ƙuri'a don fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Labarai da dumi-dumi, Gwamnan Jigawa Badaru ya janye wa Tinubu
Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya janye wa Bola Ahmed Tinubu.
Shi ne ɗan takara na biyar da ya janye wa Tinubu.
Da ma tun kafin yanzu Gwamna Badaru ya ce zai janye bisa matsayar da gwamnonin Arewa suka cimma ta bar wa 'yan Kudu takarar.
Sai dai ya ce yana jiran Shugaba Buhari ya amince da janyewar tasa.
A ƙarshe dai ya janye wa jagoran APC Bola Tinubu.
Labarai da dumi-dumi, Dimeji Bankole ya janye wa Bola Tinubu
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Dimeji Bankole ya janye wa Bola Tinubu.
Shi ne ɗan takara na huɗu da ya janye wa Tinubun.
Labarai da dumi-dumi, Kayode Fayemi ya janye wa Tinubu
Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ya janye wa Bola Ahmed Tinubu.
Shi ne ɗan takara na uku da ya janye wa Tinubu zuwa yanzu.
Labarai da dumi-dumi, Ibikunle Amosun ya janye wa Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun ya janye wa Bola Ahmed Tinubu.
Shi ne ɗan takara na biyu da ya janye wa Tinubu a filin zaɓen da ake shirin kaɗa ƙuri'a.
Kafinsa, tsohon Gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio ne ya fara janye wa Tinubu.
Labarai da dumi-dumi, Godswill Akpabio ya janye wa Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio ya janye takararsa yana mai goya wa Bola Ahmed Tinubu baya.
Da yake gabatar da jawabinsa, Akpabio ya ce yana da ƙwarewar da ta kamata ya jagoranci Najeriya amma Tinubu ya fi shi ƙwarewa.
Shi ne ɗan takara na farko da ya janye a filin zaɓen ya zuwa yanzu.
Zan mayar da hankali kan abu hudu idan na zama shugaban kasa - Ajayi Boroffice
Ajayi Boroffice shi ne na huɗu da ya yi jawabi. A cewarsa, ya ce ya cancanci zama shugaban ƙasa kuma yana da niyyar kawo sauyi a Najeriya.
Ya ce zai saka abu hudu a gaba, na farko tsaro sai tattalin arziki da ilimi da yaki da cin hanci da rashawa
Ya kuma bayyana cewa zai yi amfani da kimiyya da fasaha wajen tafiyar da ayyukan tattalin arziki da lamuran yau da kullum.
Zan bar ku da Umar Mika'il domin ci gaba da kawo rahotanni kai tsaye
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Bayanan hoto, Mustapha Kaita daga dama, Umar Mika'il daga hagu
A daidai wannan lokaci ni Mustapha Musa Kaita zan bar ku da Umar Mika'il wanda zai ci gaba da kawo muku rahotanni kai tsaye a wannan shafin kan yadda zaɓen fitar da gwani na APC ke gudana.
Yara za su yi karatu zuwa sakandire kyauta, za kuma mu ba ɗaliban jami'a bashi - Ahmad Sani Yarima
Tsohon Gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yarima shi ne na uku da ya yi jawabi.
Ya soma ne da ƙoda Shugaba Buhari kan irin ayyukan da ya yi.
Cikin abubuwan da ya ce zai yi har da batun inganta jami'an tsaro da kayan aiki domin magance matsalolin tsaro.
Haka kuma ya ce yara za su yi karatu kyauta har zuwa sakandire kyauta kuma ya ce zai fito da tsarin bai wa ɗalibai bashi ta yadda kowane ɗalibi zai samu ya yi karatu.
Ni na cancanci zama shugaban ƙasa- Lawan
Ahmed Lawan shi ne na biyu da ya soma jawabi, inda shi ma ya ce ya cancanta ya zama shugaban ƙasa
A cewarsa, ya shekara 23 a majalisa kuma a cewarsa yana da ƙwarewar da zai jagoranci Najeriya.
Ya bayyana cewa ko a ƙasashen da suka ci gaba, akwai da dama daga cikin waɗanda suka zama shugaban ƙasa da ƴan majalisa ne inda ya ce hakan ya sa ya cancanci zama shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa idan aka zabe shi, zai ɗora daga kan manyan ayyukan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa Najeriya
Ya kuma bayyana cewa irin dabarun da aka yi amfani da su wurin yaƙar ƴan Boko Haram a Arewa Maso Gabas, za su yi amfani da irin waɗannan dabaru domin yaƙar ƴan bindiga da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya
'A shirye nake na fara aiki daga ranar farko'
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne mai neman takara na farko da ya soma jawabi.
A cewarsa, a shirye yake da ya soma aiki daga ranar farko da ya zama shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa shi mai ɗaukar abubuwa da gaske ne kuma bai zo da wasa ba. Ya bayyana cewa shi mutum ne mai son haɗin kan ƙasa.
Ya bayyana cewa a shirye yake domin ya yi wa Najeriya aiki.
'Akwatinan zaɓe 20 za a ajiye wurin zaɓen fitar da gwani na APC'
Masu ruwa da tsaki a taron zaɓen fitar da gwani na Jam'iyyar APC sun soma bayani kan yadda zaɓen zai gudana.
Shugaban kwamitin tsare-tsare na zaɓen Atiku Bagudu wanda shi ne gwamnan Kebbi ya bayyana cewa akwai rumfunan zaɓe biyu da akwatinan zaɓe 20.
Haka kuma ana sa ran daliget uku daga duka ƙananan hukumomi na Najeriya 774 za su yi zaɓen.
Labarai da dumi-dumi, Masu neman takara za su soma jawabi
Duka mutum 23 da ke neman takara za su soma fitowa suna jawabi ɗaya bayan ɗaya domin yin bayani kan abin da ya sa suke neman takara.
Abubuwa ba su rikice wa APC ba - Abdullahi Adamu
Shugaban Jam'iyyar APC a Najeriya Abdullahi Adamu ya ce abubuwa ba su rikice wa APC ba.
Ya bayyana haka ne a yayin taron jam'iyyar na zaben fitar da Gwani da ake yi a Eagle Sqaure lokacin da yake jawabi a kan dandamalin wurin taron.
Ya bayyana cewa abubuwa suna gyaruwa a jam'iyyar kuma akwai haɗin kai haka kuma ya ce APC na magana ne da murya ɗaya.
Labarai da dumi-dumi, Shugaba Buhari ya isa Eagle Square wurin zaɓen fitar da gwani
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Dandalin Eagles Square domin halartar zaɓen fitar da gwani na Jam'iyyar APC.
Shugaban shi ne na ƙarshe da ya shiga dandalin, inda daga shigar shi aka rufe ƙofa aka soma taron.
Tinubu, Osinbajo, Lawan da wasu masu neman takara a APC sun isa Eagle Square
Kusan duka masu neman takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar APC sun isa dandalin Eagle Square.
Na baya-baya da suka shiga dandalin sun haɗa da Bola Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo.
Waɗanda suka zo tun da farko sun haɗa da Yahaya Bello da Ahmed Sani Yarima da Rotimi Amaechi da Ahmad Lawan.
Aisha Buhari ta isa Eagle Square
Uwar gidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta isa dandalin Eagle Square domin halartar zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC.
Sanata Yarima ya ce bai janye wa wani ɗan takara ba
Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani ya ce bai janye takararsa ba inda ya ce ya je dandalin Eagle Square da niyyar yin takara.
BBC Hausa ta tambaye shi cewa me zai ce kan batun mutum biyar da aka ce sunayensu aka bayar a matsayin masu yin takara inda ya ce "ai wannan an ce ne, amma ka ganni nan na zo takara.
"Saboda haka an ce an ce ba gaskiya ba ne, da gaskiya ne da ba a ganni a nan ba."
Ya kara da cewa babu wanda ya tuntube shi batun janyewa.
Ya ce a halin yanzu suna jira ne a fara zabe.
Mata sun yi taron tsinuwa kan maharan coci na Ondo
Wasu mata a garin Owo na Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya sun gudanar da abin da suka kira taron tsinuwa domin tsine wa waɗanda ke da hannu a harin da aka kai a coci, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
A ranar Lahadi, 5 ga watan Yunin 2022 ne wasu ƴan bindiga suka kai hari cocin St Francis inda suka kashe aƙalla mutum 20, kusan 50 kuma suka samu rauni.
Matan dai sun ce sun yi kira ne ga aljanu da su yi musu yaƙi amadadinsu tare da hukunta waɗanda suke da hannu a lamarin
Wani daliget ɗin APC ya rasu a Abuja
Asalin hoton, OTHER
Wani daliget a Najeriya da ya je Abuja babban birnin ƙasar domin halartar zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a APC ya rasu.
Rahotanni sun ce daliget ɗin mai suna Isa Baba-Buji, ɗan asalin Jihar Jigawa ne kuma ya rasu ne a lokacin da yake karya kumallo kafin tafiya dandalin Eagle.
Wasu da suka tabbatar wa BBC da lamarin sun bayyana cewa ana shirin mayar da shi Jigawa domin gudanar da jana'izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada