Atiku ya fi karfin Tinubu, in ji PDP
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Umar Mikail, Umaymah Sani Abdulmumin, Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya
Labarai da dumi-dumi, Rotimi Amaechi ya samu kuri'u 316
Labarai da dumi-dumi, Ahmed Sani kuri'a 4
Labarai da dumi-dumi, Dave Umahi ya samu kuri'a 38
Labarai da dumi-dumi, Tunde Bakare bai samu kuri'a ko guda ba
Labarai da dumi-dumi, NwaJiuba Chukwuemeka ya samu kuri'a 1
Labarai da dumi-dumi, An soma sanar da sakamakon zaɓe
Shugaba Buhari da uwargidansa Aisha Buhari sun dawo wajen taron

Asalin hoton, PRESIDENCY
Shugaba Muhammadu Buhari da uwargidan Aisha Buhari sun dawo wajen taron.
Shugaban da uwargidansa sun bar taron a cikin daren jiya lokacin da aka soma kada kuri'a
An dai kan tantace kuri'u kuma nan bada jimawa ba za a soma kidayasu domin sanar da mutumin da ya yi nasara.
Sai dai tun a wajen tantace kuri'un da kowanne dan takara ya samu, aka tabbatar da cewa Bola Tinubu ke da yawan kuri'a a zaben na fitar da gwanin.
Tinubu ke jan ragama bayan kammala tantace akwati 20

An kammala tantace akwatina 20 na kuri'un da aka kada zuwa wannan lokaci.
Tinubu ke kan gaba da yawan kuri'a a wadannan akwatuna.
Kawo yanzu, yana da yawan kuri'u 890, kuma ya bai wa Rotimi Amaechi da Yemi Osinbajo tazara sosai.
Amaechi ya samu kuri'u 175 zuwa yanzu, Osibanjo kuma na da kuri'a 126.
Nan da 'yan sa'o'i ake sa ran sanar da mutumin da ya yi nasara.
Hotunan yadda ware kuri'u ke kasancewa kafin a tattara a soma kidaya su




An tantace akwatinan zaɓe 10 kawo yanzu

An kammala tantace akwatina zaɓe 10 da ke nuna har yanzu, Bola Tinubu ke kan gaba.
Tantace wadannan kuri'u ya kunshi kirar suna ɗan takara da ke kan kowanne takardar zaɓe.
Alamomi na nuna cewa Mista Tinubu na da sama da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka tantace kawo yanzu.
Sauran 'yan takarar da suka samu ɗan kuri'u akwai tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da kuma Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Har yanzu dai ana ci gaba da tantace kuri'u, domin fayyace mai nasara cikin mutum 23 da ke fafatawa.
Minti ɗaya da BBC na Safe
Bayanan sautiA saurari labaran duniya cikin minti guda Tinubu ke kan gaba a kuri'un da aka tantace kawo yanzu

Asalin hoton, Others
Jagoran jam'iyyar APC kuma ɗan takara a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ke kan gaba da yawan kuri'u aka soma kidayawa domin tantace yawan kuri'un da kowanne ɗan takara ya samu.
Sauran wadanda suka samu kuri'a a wannan tantacewa sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, tsohon ministan Rotimi Amaechi da gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Ana dai kan tantace kuri'un da daliget 2,340 suka kada.
Da misalin karfe 2:40 na daren jiya aka soma zaɓe har zuwa 8 na safen yau Laraba.
Ana kan ƙidaya kuri'u

Za a ɗan dau lokaci ana kidaya kuri'un ganin cewa daliget sama da 2,000 ne suka kaɗa wannan kuri'a daga jihohin Najeriya.
Kidaya kuri'un na tafiya lafiya kawo yanzu ba tare da wata matsala ba. Yayinda 'yan Najeriya suka zuba ido domin ganin yadda za ta kaya.
Za a fara ƙirga ƙuri'u
A yanzu haka an soma gyara wajen don lissafa ƙuri'un da aka kammala kaɗawa.


An kammala kaɗa ƙuri'a
A yanzu haka dai an kammala kaɗa ƙuri'a a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC da ake yi a Abuja.
Yanzu kuma sai abu na gaba, wato ƙirgar ƙuri'u.
Abubuwan da suka faru a wajen zaben fitar da gwanin APC a taƙaice
Jama'a sun fara taruwa tun ƙarfe 4 na yamma
Gari ya waye

Bayanan hoto, A karya kumallo sai a taho karatun labarai Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da wayar garin Laraba lafiya.
Yaya gajiyarmu ta jiya? Allah Ya ba mu ikon warware ta a cikin tsanaki.
Wannan shafi zai ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa kai tsaye daga dandalin Eagle Square a Abuja, babban birnin Najeriya.
Har yanzu ana kaɗa ƙuri'a ne a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC. Sanna bayan an kammala za a fara ƙirga ƙuri'un.
Sunana Halima Umar Saleh, kuma ni da abokiyar aikina Umaymah Sani Abdulmumin ne za mu karɓi reagamar shafin a yanzu.
Bayan da Umar Mika'il ya shafe dare yana ba ku bayanan abubuwan da suka faru.
A jiya da yamma kuma Nasidi Yahaya da Mustapha Kaita ne suka ja ragamar shafin.
Har yanzu babu ɗan takara Emeka Nwajuba babu labarinsa

Asalin hoton, State House
Idan ba ku manta ba, tun a daren jiya Talata rahotanni suka nuna cewa ɗaya daga cikin masu neman yin takara a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Emeka Nwajuba, daga Jihar Imo ya yi ɓatan-dabo a filin taron na APC.
An kira sunan Nwajuba sau biyu don ya gabatar da jawabinsa kamar yadda sauran 'yan takara suka yi amma bai amsa ba.
Har ya zuwa loƙacin haɗa wannan rahoton babu bayani game da halartarsa wurin taron ko kuma dalilin da ya sa ya bar wajen.
Nwajuba ne tsohon Ƙaramain Ministan Ilimi a Najeriya, kuma yana cikin na farko-farko da suka sayi fom ɗin neman takarar shugagan ƙasa a jam'iyyar ta APC.
Deliget daga Jihar Zamfara sun shirya tsaf don kaɗa ƙuri'a
Masu kaɗa ƙuri'a daga Zamfara sun kai 42 da aka tantance kuma an nemi su fito don cika aikinsu.
Ɗan takara Ahmed Sani Yerima ya fito daga Zamfara.
