Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Sai gobe
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu and Awwal Ahmad Janyau
Sai gobe
Fira Ministocin Poland da Jamhuriyar Czech da kuma na Slovenia sun isa kyiv domin nuna goyon bayansu ga Ukraine a yayin da ta ke fuskantar mamaya daga Rasha.
Shugabannin wadanda suka yi tafiyar a jirgin kasa, za su gana da shugaba Zelensky nan gaba kadan.
Firaminsitan Poland, Mateusz Morawiecki, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a birnin Kyiv da yaki ya daidaita tarihi ya maimaita kansa kuma makomar turai na cikin halin kila wa kala.

Somalia ta nemi tallafi daga kasashen duniya domin ta ciyar da kusan mutum miliyan bakwai da ke fuskantar matsananciyar yunwa da rashin ruwan sha.
Firaministan kasar Mohammed Hussein Roble, ya ce bala'in farin da kasar ke ciki tsawon fiye da shekara 10, ya tilastawa ‘yan kasar dubu dari biyar barin gidajensu.
Rahotanni sun ce dubban yara ne suka daina zuwa makaranta sakamakon farin.
Kafar talbijin din kasar ta ce wasu mutum uku sun mutu saboda tsananin yunwa a kudu maso yammacin kasar inda 'yan tawayen kasar suka dasa shingaye.
A kokarinsu na samun goyon baya, kungiyar Al -Shabaab na rarraba abinci da ruwan sha a yankunan da ta ke iko da su.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun yi wa ofishin ƴan sanda a Nasko ƙofar rago tare da kashe DPO.
An kashe DPO Umar Mohammed Digari a ranar Talata da wasu ƴan sanda biyu, kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar cewa ƴan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne bayan harin da aka kai masu a maɓuyarsu inda aka ƙwace shanun da suka sato sama da 800.
Sai dai babu wata sanarwa daga rundunar ƴan sandan jihar da ta tabbatar da lamarin.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Joe Bidenana sa ran zai gana da shugabannin Tarayyar Turai da na Nato a Brussels a mako mai zuwa, kamar yadda fadar White House ta bayyana.
Tattaunawar ana sa ran za ta fi mayar da hankali kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, kuma batun da ake sa ran za su mayar da hankali sun kunshi batun tsaro da harakokin ƙasashe waje.
Shugaban na Amurka zai haɗu da takwarorinsa na Turai a ranar Alhamis 24 ga watan Maris.
Hukumomi a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da cewa mafarauta sun bindige wani zaki da ya gilma kusa da wani kauye a yankin Konduga.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda daraktan Kula da Gandun Daji da Namun Daji na jihar, Mista Ayuba Peter ya yi wa Ishaq Khalid karin bayani.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da 'yan Ukraine miliyan uku ne suka tsere daga kasar, kuma kusan rabinsu yara ne.
Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce – kowace daƙiƙa – yaro ɗaya a Ukraine na zama ɗan gudun hijira.
UNICEF ta ce akwai tsananin buƙatar ayyukan kare yara -- ƙananan 'yan gudun hijira, musamman wadanda aka rabu da iyayensu domin sun fi fuskantar cin zarafi da kuma safararsu.
Wannan shi ne matsalar 'yan gudun hijira mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu kuma matsalar ba ta nuna alamun raguwa ba.

Asalin hoton, Ofishin Sanata Ida
An nada tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mohammed Ida a matsayin Wazirin Katsina.
Sarkin Yaƙin Katsina kuma sakataren masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo ne ya tabbatar wa BBC ranar Talata.
Sanata Ida ya maye gurbin Alhaji Sani Abubakar Lugga wanda ya yi murabus daga muƙaminsa na Wazirin Katsina a watan jiya.
Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.
An haifi Sanata Ida a birnin Katsina a shekarar 1949, kuma ya yi karatunsa na boko a Najeriya da Birataniya da kuma Amurka.
Sabon Wazirin na Katsina ya soma aikin gwamnati da Babban Bankin Najeriya, kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati, ciki har da Babban Sakatare na Ma'aikatar Tsaron Najeriya.
Sannan ya wakilci shiyyar Katsina ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar tsakanin 2007-2011.
Sanata Ida yana da mata daya Hajiya Khadija da 'ya'ya da jikoki da dama.

Asalin hoton, Other
Bisa kuskure, wani yaro mai shekara uku ya harbe mahaifiyarsa har lahira yayin da yake wasa da wata bindiga a wajen birnin Chicago, kamar yadda 'yan sanda suka sanar.
Kamar yadda 'yan sandan na gundumar Dolton suka bayyana, wannan abin takaicin ya faru ne ranar Asabar da karfe 8:30 na dare a wurin da ake ajiye motoci na wani katafaren shago.
Yaron na zaune a kujerar baya ne, cikin motar mahaifinsa inda mahaifin nasa na zaune a kujerar direba tare da mahaifiyarsa a gaban motar.
Ba a san yadda yaron ya iya fito da bindigar ba, amma rahotanni na cewa ya rika yin wasa da ita ne a kujerar bayan motar.
Daga baya sai ya latsa kunamar bindigar kuma nan take harsashi ya fito kuma ya shiga ta wuyan mahaifiyarsa mai suna Deejah Bennett, inda ya kashe ta.
'Yan sandan Dolton sun ruga da matar zuwa asibitin Jami'ar University of Chicago Medical Centre, sai dai likitoci sun ce ta riga ta cika.

Hukumomi a jihar Legas ta kudancin Najeriya sun kama wata fitacciyar mata mai suna Mis Ogbulu Chindinma Pearl, kuma ta gurfanar da ita gaban wata kotun majistire a unguwar Oshodi ta jihar.
Ana dai tuhumar Mis Ogbulu ne kan tuhume-tuhume har guda hudu.
Na farko shi ne raba wa jama'a man fetur a matsayin tallafin biki (subiniya) yayin wani biki da ta yi ranar 5 ga watana Maris na wannan shekarar a wani dandalin gudanar da biki mai suna Havillah Event Centre a birnin Legas.
'Yan sanda sun ce laifin ya taka sashe na 251(1) da na 168 (1) da kuma na 244 na dokar jihar Legas ta 2015, da kuma sashe na 195 (2)(b) na dokar kulawa da muhalli ta jihar Leagas ta 2017.
Sai dai an bayar da belin matar kan naira miliyan 2 bayan ta gabatar da wasu mutum biyu da suka tsaya ma ta.
Kotun ta kuma dage zamanta zuwa ranar 24 ga wannan watan na Maris domin ta fara sauraron karar.


Asalin hoton, EPA
Firaministocin kasashen Turai uku, Poland da jamhuriyar Czech da kuma Sloveniya sun ce za su tafi birnin Kyiv na Ukraine ta jirgin kasa domin tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky da firaministan kasar.
Za su tafi can ne a matsayin wakilan Tarayyar Turai kuma za su bayyana irin goyon bayan da tarayyar za ta ba Ukraine, kamar yadda shugaban ma'aikatan ofishin firaministan Poland Michal Dworczyk ya ce.
Shugabannin uku za su yi tafiyar tare da shugaban jam'iyya mai mulki ta Poland Jaroslaw Kaczynski.
A halin yanzu jirgin da shugabannin ke ciki na kan hanya kuma har ya tsallaka kan iyakar Ukraine da Poland kan hanyarsa ta zuwa birnin Kyiv.
Dworczyk ya nanata cewa Nato ba za ta shiga cikin yakin ba amma za ta yi duk mai yiwuwa domin taimaka wa kasar kan mamayar da Rasha ke yi ma ta.

Asalin hoton, AFP
Wata zakanya da aka taba wallafa hotunanta yayin da ta ke fama da rashin lafiya da yunwa a gidan kula da namun dawa na al-Quraishi da ke Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce zakanyar mai suna Kandaka na cikin zakuna biyar da ke fama da karancin abinci da cututtuka - kuma biyu cikinsu sun mutu daga baya.
An mayar da sauran zakunan da suka tsira da rayukansu zuwa gandun namun daji na al-Bageir da ke kudu maso gabashin Khartoum.
Wanna sunan na Kandaka, a tarihi akan sanya wa sarauniyoyin tsohuwar masarautar Nuba ne dubban shekaru da suka gabata, kuma a shekarun yanzu sunan ya dawo inda ake sanya wa mata masu fafutukar kare hakin dan Adam - wadanda suka taimaka aka hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir kamar yadda AFP ta sanar.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Reuters
Tun da farko wasu kafofin yada labarai har ma da kamfanin dillancin labarai na Reuters na cewa wani jirgn sama da aka alakanta da mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich ya sauka a birnin Moscow.
Kamfanin dillancin labaran ya kuma ce attajirin ya bi ta filin jirgin saman Ben Gurion na kasar Isra'ila - kuma yanzu hotunansa a can sun bayyana.
Birtaniya ta dauki matakan ladabtarwa kan Mista Abramovich a makon jiya saboda alakarsa da Shugaban Rasha Vladimir Putin, kuma jim kadan bayan haka Tarayyar Turai ma ta dauki irin wadannan matakan. Ya dade yana musanta alakar kut-da-kut da ake cewa yana da ita da Shugaba Putin.

Hukumaomin sun ce Rasha ta kai wa wani filin jirgin sama a birnin Dnipro da ke kasar Ukraine.
Valentyn Reznichenko, wanda shi ne shugaban gwamnatin yankin Dnipropetrovsk ya ce harin ya yi "barna mai matukar yawa."
"Cikin dare, abokan gaba sun kawo mana hari kan filin jirgin saman Dnipro. Harin da aka kai da rokoki masu linzami biyu. An lalata kwaltar da jirage ke sauka a kai gaba dayanta. Dakin jami'an da ke kula da sauka da tashin jirage ma ya lalace. Lalacewa mai matukar yawa," inji Mista Reznichenko.

Asalin hoton, Russian Ministry of Defence
Kakakin ma'aikatar tsaro ta Rasha ya ce dakarun Rasha ne ke iko da yankin Kherson da ke kudancin kasar.
Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin kalaman na Igor Konashenkov ba.
Kamfanin dillancin labarai na Interfax-AVN ya ruwaito shi yana cewa sojojin Rasha sun kwace daukacin yankin.
Wani bidiyo da aka wallafa a baya ya nuna mazauna birnin na Kherson na gudanar da wata zanga-zanga kan mamayar da Rasha ke yi, duk da cewa sojojin na Rasha sun rika yin harbi a iska.

Asalin hoton, Other
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gbaa da sayar wa kamfanonin jiragen sama man jirgin sama na Jet A1 kan naira 500 ga kowace lita cikin kwana uku masu zuwa.
An dauki wannan matakin ne domin hana kamfanonin daina aiki.
Shugaba kamfanin mai na kasa a Najeriya NNPC ne ya bayar da wannan tabbacin bayan wata ganawa da yayi da dillalan man fetur da masu ruwa da tsaki da kuma hukumomin da ke s aido a bangaren albarkatun mai a Najeriya.
Ya ce za a ba kamfanonin lasisin shigo da man fetur.
Mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya Ahmed Wase ne ya jagoranci wannan zaman yain da ake kokarin gano musabbabin karancin man fetur da man jirgin sama wanda ya haifar da karuwar farashin tikitin jirgin sama a cikin Najeriya.

Asalin hoton, EPA
Cikin daren jiya Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya wallafa wani sakon bidiyo inda ya bayyana karfin gwuiwarsa kan tattaunawar da ake yi ta zaman lafiya tsakanin kasarsa da Rasha.
Ya ce da alama Rasha ta gane cewa ba za ta iya samun nasara a fagen yaki ba.
"Sun fara ganewa cewa ba za su iya cimma komai ba ta hanyar yaki," inji Zelensky.
Shugaban ya kuma yi jawabi ga dakarun Rasha kai tsaye, yana cewa "Idan ku ka mika wuya ga dakarunmu, za mu mutunta ku kamar yadda ya kamata a mutunta mutane."
Zelensky ya kuma bayyana godiyarsa ga wata mata da ta kutsa cikin dakin shirye-shirye a wata tashar talabijin ta rasha yayin da ake karanta labaran duniya, inda ta nuna wani allo da ke kira da a daina yaki.
Kamar yadda muka sanar da ku a baya, suna matar Marina Ovsyannikova, wacce edita ce a tashar talabijin din.

Asalin hoton, AFP
Daga ranar Talata 'yan Kenya za su fara biyan sabon farashin man fetur yayin da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine ke haifar fa hauhawar farsshin labarkatun mai kamar man fetur da dangoginsu.
Kamfanin da ke sa ido kan farashin albarkatun man fetur ya ce farsahin man fetur zai karu da Shillingi biyar na Kenya.
kamfanin ya kuma ce farashin kananzir, wanda yawancin 'yan Kenya suka dogara da shi ba zai karu ba a yanzu.
Wani shirin saka tallafi na gwamnatin Kenya ya hana a yi karin farashin albarkatun man fetur na tsawon wata hudu a jere.
Bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, farashin danyen mai na Brent yayi tashin da bai taba yi ba cikin shekara 14. A sanadiyyar wannan lamarin, ana sa ran farashin kayan masarufi ya tashi a kasar da ke yankin gabashin Afirka.

Asalin hoton, Perviy Kanal
Cikin dare mun ga bidiyon wata mata dauke da wani allo wanda aka rubuta sakon "A daina yaki" wacce ta kutsa cikin daki shirye-shiryen yayin da ake gabatar da labaran duniya na yamacin ranar a tashar Channel 1 mallakin gwamnatin Rasha.
A jikin allon ana iya ganin sakon da matar ta rubuta, wanda ke cewa "Ban yarda da yaki ba! A daina yaki! Kar ku yarda da farfaganda, karya suke shara muku a nan".
An bayyana sunan matar Marina Ovsyannikova, kuma an ce edita ce a tashar talabijin din.
An rika jin muryarta yayin da ake karanta labaran duniya tana cewa "Ban yarda da yaki ba! A daina yaki!" kafin daraktan shirye-shiryen tashar ya yanke hoton zuwa ga wani rahoto da aka nada tun gabanin a fara karanta labaran duniya.
Tashar talabijin din na karkashin kulawar gamantin rasha ne kuma ta kan sa ido kan dukkan labaran duniya da ake watsa wa a cikin kasar a dukkan tashoshin rediyo da na talabijin.
Ana hasashen Ovsyannikova na hannun jami'an tsaro.

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Chadi sun mika wani tsohon jagoran wata kungiyar 'yan tawaye a jamhuriyar Tsakiyar Afirka, CAR ga kotun da ke hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC).
Maxime Jeoffroy Eli Mokom shi ne ya jagoranci wasu mayakan kungiyoyin anti-balaka kuma ana tuhumarsa da aikata laifukan yaki da na cin mutuncin bil Adama a 2013 zuwa 2014.
Kotun ta mika sammacin a kamo mutumin ne tun 2018.
Kotun ta kuma ce ana tuhumar Mista Mokom mai shekara 43 da haihuwa da kisa da tashin al'umma daga wani wuri zuwa wani wurin da karfin tsiya, baya ga azabtar da su da sassare wasu sassan jikinsu da kuma shigar da kananan yara su zama sojojinsa da ma wasu manyan laifukan.
Rikici ya barke ne a watan Maris na 2013 bayan da 'yan tawaye Musulmi da aka fi sani da Seleka su ka gwace iko a yankin. Bayan wannan matakin ne Kirista kasar suka kafa kungiyar 'yan tawaye ta mayakan anti-Balaka.
An kashe dubban 'yan kasar kuma akalla mutum miliyan daya sun rasa muhallansu a cikin kasar da ke tsakiyar nahiyar Afirka tun 2013, kmar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.
Sojojin Chadi sun shiga tsakani bayan rikicin na 2013 amma sun janye bayan da aka tuhume su da daukan bangaren Musulmin kasar.