Wazirin Katsina Sani Abubakar Lugga ya ajiye muƙaminsa

Lugga

Asalin hoton, Lugga web

An wallafa

A ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu ne Wazirin Masarautar Katsina Alhaji Sani Abubakar Lugga ya yi murabus daga muƙaminsa na Wazirin Katsina.

Sarkin Yaƙin Masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo wanda kuma shi ne sakataren masarautar ya tabbatar wa da BBC lamarin inda ya ce Masarutar Katsinan ce ta fara aike wa wazirin takardar neman bayani kan wasu kalamai da ya yi a birnin Ilori na jihar Kwara.

Wazirin Katsinan ya yi jawabi ne a wajen wani taro kan matsalolin tsaron da jihar KAtsina ke fama da su, inda ya ce ƙananan hukumomi bakwai ba sa hannun gwamnati, kuma hakimai da shugabanni sun yi ƙaura daga wuraren zuwa cikin birnin Katsina.

A jawabin nasa kuma, Alhaji Sani Abubakar Lugga ya ƙara da cewa an rufe makarantu a yankunan.

Sarkin Yaƙin ya ce ko da aka aika wa wazirin saƙon sai ya aiko da takardar ajiye aiki kafin ya bayar da amsa kan bayanin da aka nemi ji daga bakinsa.

Alhaji Ibrahim Ifo ya ce masarautar ta Katsina ta nemi ƙarin bayani daga bakin Alhaji Lugga ne saboda bayanan da ya yi a Ilori sun tayar da hankula a jihar.

"Sannan kuma wasu abubuwan da ya faɗa ba daidai ba ne. A matsayinsa na mai riƙe da babbar sarauta ya kamata duk abin da zai faɗa da ya shafi jama'a ya zama masarauta na da masaniya a kansu.

"Ba mu tura masa takardar neman bayani da nufin tozarta shi ko cin mutuncinsa ba," in ji ALhaji Ifo.

Sakataren masarautar ya ƙara da cewa daga baya Alhaji Lugga ya aika da takardar amsa kan bayanin da aka buƙata daga wajensa, inda ya ce ya yi bayanin ne a matsayinsa na Alhaji Lugga ba na Wazirin Katsina ba.

A yanzu haka Alhaji Ifo ya ce masarautar Katsina ta mashi buƙatar yin murabus ɗin wazirin, kuma nan ba da jimawa ba za a naɗa sabon waziri.