Yau ce rana ta 20 ta mamayar da Rasha ke yi a Ukraine

Asalin hoton, UKRAINE STATE EMERGENCY
Ga wasu cikin abubuwan da suka faru kawo yanzu safiyar Talata a yakin da Rasha ke yi da Ukraine:
- Rasha ta ci gaba da jefa bama-bamai a birnn Kyiv da safiyar nan, har wani bene mai gidajen zama ya kama da wuta baya ga fashewar abubuwa da aka rika ji cikin babban birnin na Ukraine. Ma'aikatar da ke kula da ayyukan agaji ta ce an kashe gobarar
- A shirya bude wasu hanyoyi na jin kai daga karfe 9 na safe zuwa karfe 9 na dare a yankin Sumy da ke arewa maso gabashin kasar, kamar yada gwamnatin yankin ta sanar
- Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a yau, kamar yadda wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Ukraine ta sanar
- Wani mai ba gwamnatin Ukraine shawara ya ce a ganinsa za a kawo karshen wannan yakin a farkon watan Mayu
