Jamhuriyyar Benin ta saki Sunday Ighoho

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. Ƙoƙarin Najeriya na zama dunƙulalliyar ƙasa ya gamu da koma-baya tun 2015 - Obasanjo

    Ƙoƙarin Najeriya na zama dunƙulalliyar ƙasa, ya gamu da gagarumin koma-baya tun daga shekara ta 2015.

    Tsohon Shugaban ƙasar, Cif Olusegun Obasanjo ne ya bayyana haka cikin ƙarshen mako a wani ɓangare na bikin cika shekara 85 da haihuwa lokacin wani taron ƙasashen duniya a Cibiyar tabbatar Tsaron Bil'adama da Tattaunawa da ke Ɗakin Karatun Shugaba Olusegun Obasanjo a Abeokuta cikin jihar Ogun.

    Sai dai a nata martanin fadar gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta yi sa-in-sa da mai shekarun tsufa kamar Obasanjo ba.

    Bayanan sautiRahoton Mukhtar Bawa kan batun Obasanjo
  2. Wadanda ake tuhuma da safarar hodar Iblis tare da Abba Kyari sun amsa laifinsu

    Abba Kyari a gaban bababr kotun Abuja

    Mutum biyu cikin wadanda ake tuhuma da mu'amalla da hodar Ibilis a shari'ar da aka gurfanar da Abba Kyari tare da wasu mutu shida sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

    Mutane biyun ba sa cikin 'yan sanda hudun da ake tuhuma tare da babban jami'in 'yan sandan.

    Kamar yadda jaridar Premium Times ta intanet ta ruwaito, mutanen biyu wato Chibuna Umeibe da Emeka Ezenwanne sun ba lauyoyinsu mamaki bayan da suka amsa laigukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

  3. Abba Kyari ya ce bai aikata laifin safarar hodar Ibilis ba

    Abba Kyari tare da wasu jami'an 'yan sanda yayin da aka fara shari'arsu a Abuja

    Babban jami'in dan sanda Abba Kyari wanda hukumar NDLEA ke tuhuma da safarar hodar ibilis a wata shari'ar da ta gurfanar da shi a wata babbar kotun da ke Abuja ya musanta cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

    Hukumar hana tu'ammali da miyagu kwayoyi ta NDLEA ce ta gurfanar da Abba Kyari da wasu mutum shida a kotun.

    Sauran mutanen da ake tuhumar su da aikata laifin tare da Abba Kyari sun hada da Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan 'yan sanda da Bawa James, mataimakin sufritandan 'yan sanda da Simon Agirgba da kuma John Nuhu wadanda dukansu sufetan 'yan sanda ne.

    Sauran mutanen sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

    Hukumar NDLEA ta ce Abba Kyari da wasu jami'an da ke tamaka masa sun yi awo gaba da kilo 21.25 na koken, hodar Iblis din da suka kwace a hannun wasu masu safarar ta, kuma hukumar ta ce abin da suka aikata laifi ne.

    A yau Litinin ne aka fara wannan shari'ar.

  4. An fara shari'ar Abba Kyari da wasu mutum shida kan safarar hodar Ibilis

    Abba Kyari

    Babban jami'in dan sanda Abba Kyari da wasu mutum shida da ake tuhuma da safarar hodar ibilis sun isa wata babbar kotun da ke Abuja domin a fara shari'a kan laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

    Hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ce ta shigar da karar ranar 28 ga watan Fabrairu tana tuhumarsa da safara da kuma yin cinikin hodar Iblis.

    Jami'an tsaro dauke da makamai ne suka kai Abba Kyari da wadanda ake tuhumarsu da aikata laifin tare da shi kotun da misalin karfe 8:12 na saiyar yau cikin wata bakar motar bas samfurin Hiace.

    Sauran mutanen da ake tuhumar su da aikata laifi tare da Abba Kyari sun hada da Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan 'yan sanda da Bawa James, mataimakin sufritandan 'yan sanda da Simon Agirgba da kuma John Nuhu wadanda dukansu sufetan 'yan sanda ne.

    Sauran mutanen sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

  5. Amurka na zawarcin Saudiyya da Venezuela domin maye gurbin man fetur din Rasha da nasu

    About 10% of US oil imports come from Russia

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kashi 10 na dukkan man fetur din da Amurka ke amfani da shi daga Rasha ta ke sayo shi.

    Shugaban Amurka Joe Biden na son yin wata ziyarar aiki zuwa Saudiyya domin tattaunawa da Sarki Salman kan bukatar kasarsa na bunkasa yawan man fetur din da kasar ke hakowa.

    Wata mujallar siyasa ta Amurka mai suna Axios ce ta wallafa labarin, tana cewa nan da watan gobe shugaban Amurkan zai kai ziyarar yayin da Fadar White ke kokarin shawo kan rikicin karancin makamashi a duniya wanda yakin Rasha da Ukraine ya haifar.

    Sai dai kakakin Fadar White House ta ce kawo yanzu ba a bayyana ranar da zai kai ziyarar ba, yana cewa "dukkan abubuwa da ake cewa hasashe ne kawai."

    Akwai wani rahoton da ke cewa jami'an gwamnatin Amurka da na Venezuela kan janye takunkumin da Amyurka ta kakaba wa Venezuelan. Wasu 'yan majalisar Amurka na cewa Amurka na iya maye gurbin man fetur din da Amurka ke sayowa daga Rasha da na Venezuela.

    A halin yanzu, Amurka na dogara da kashi 10 na dukkan man fetur din da ta ke amfani da shi daga Rasha ne.

  6. Abin da ya faru a Ukraine tun wayewar garin Litinin

    A fire is seen in Mariupol after Russia launched a massive military operation against Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Ga wadanda sai yanzu su ka sami zarafin bibiyar mu, ga abubuwan da ke faruwa ciki sa'o'in da suka gabata:

    • Rasha ta ce za ta kyale fararen hula a biranen Ukraine masu dama su fice domin kauce ma hare-haren da ta ke kai wa cikin kasar. Cikin biranen akwai Kyiv babban birnin kasar da Mariupol wanda tun kwanaki uku da suka gabata ake kai komo tsakanin Rasha da Ukraine kan kyale mutanen da rikicin ya rutsa da su
    • Shugaba Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da kasha fararen hula bayan harin da Rasha ta kai kan birnin Irpin ya halaka wasu 'yan gida daya
    • Dakarun Ukraine na cewa sun kwace garin Chuhuiv daga hannun sojojin Rasha
    • Akwai rahotannin da ke cewa sojojin Rasha na yi wa birnin Mykolaiv mai tashar jirgin ruwa a kudancin kasar luguden wuta
    • Birtaniya ta ce za ta ba Ukraine karin dalar Amurka miliyan 100 a matsayin tallafi ga gwamnati kasar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta
    • Farashin man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba tun 2008 bayan da Amurka ta ce tana tunanin saka wa albarkatun man Rasha takunkumi
  7. Ukraine ta ce za a ci gaba da tattaunawar sulhu a karo na uku tsakaninta da Rasha

    yaki

    Gwamnatin Ukraine ta ce a yau Litinin za a ci gaba da tattaunawar sulhu a karo na uku tsakaninta da jami'an Rasha, sai dai kawo yanzu Moscow ba ta tabbatar da hakan ba.

    Fatan da ake da shi na samun sassauci bai taka kara ya karya ba.

    A jiya Lahadi Shugaba Putin ya shaida wa shugabannin kasashe biyu cewar dole Ukraine ta amince da dukkan bukatun shi kafin ya kawo karshen mamayar da ya yi wa kasar.

    Jami'an gwamnatin Farasnsa, sun shaida wa BBC cewa Mr Putin ya fada wa Shugaba Emmanuel Macron, yana da aniyar cimma manufarsa ko ta sasantawa ko da karfin yaki.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce kasarsa na da ƙwararan shaidun da suka nuna da gangan aka kai wasu hare-hare kan farar hula da gangan a Ukraine.

  8. Dakarun Ukraine na ci gaba da jajircewa don hana sojojin Rasha shiga birnin Kyiv

    Ukraine da Rasha

    Dakarun Ukraine na ci gaba da jajircewa domin tabbatar da sojin Rasha ba su danna birnin Kyiv ba.

    Sojin Ukraine sun haka ramuka masu zurfi da min kewaye mashigar Kyiv, yayin da wasu kuma suka kafa shingaye a kan hanya dauke da makaman roka da tankokin yaki.

    Magajin birnin Kyiv Vitaliy Klitschko, ya ce ba za su taba mika wuya ba.

    Ya ce "a yanzu an ci gaba da gwabza yaki a Irpin da Bucha, da Hostomel, dakarunmu na fafatawa, abin da nake son shaida muku shi ne, babu inda za mu, ba kuma za mu bar Kyiv b, babu mai son mutuwa, amma dole mu tsaya mu kare 'ya'yanmu da iyalanmu."

    Burinsu mu mika wuya, hakan kuwa ba za ta taba faruwa ba.

  9. Barkanmu da safiyar Litinin

    Za mu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa a fagen dagar da Rasha ta buɗe yayin da ta ke ci gaba da kai hare-hare a Ukraine tun daga ranar Alhamis, 24 ga watan Fabarairu.

    Ku biyo ni Sani Aliyu a wannan shafin don samun rahotannin kai-tsaye.