Jamhuriyyar Benin ta saki Sunday Ighoho

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a duniya

    Sai gobe.

  2. Ana ce-ce-ku-ce kan kisan wani sojan Nijar

    Wani sabon cece-kuce ya taso a game da kisan wani sojin Nijar da rana tsaka a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.

    Ana zargin wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka tura shi da karfi cikin wata mota suka tafi da shi, daga bisani kuma suka kashe shi.

    Lamarin ya tayar da hankalin jama'a.

    Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ta yada bayanan cewa gwamnati na kama sojoji da fararen hula bisa zarginsu da cin amanar kasa.

    Sai dai gwamnatin Nijar ba ta ce komi ba kawo yanzu kan wadannan batutuwan.

    Ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai.

    Bayanan sautiAna ce-ce-ku-ce kan kisan wani sojan Nijar
  3. Mummunan hari a gidan biredi ya kashe mutum 13 a Ukraine

    Jami'an ceto a Ukraine sun ce an kshe aƙalla mutum 13 a wani hari ta sama da aka kai kan wani gidan biredi da ke yammacin birnin Kyiv.

    An yi amanna cewa akwai mutum fiye da 30 da ke aiki a gidan biredin da ke garin Makariv.

    Tuni dai aka ceto wasu mutum biyar da ga baraguzan ginin.

    A garin Irpin kuwa, dubban mutane ne aka kwashe bayan dakarun Ukraine sun mayar da martani akan hare haren Rasha.

    A jiya Lahadi, bayanai sun nuna cewa mutane kusan dubu 2 ne suka tsallakew kawanyar da aka yi wa birnin Mariupol da kae Kudancin Ukraine.

    Ukraine

    Asalin hoton, Ukrainian State Emergency Service

  4. Jamhuriyyar Benin ta saki Sunday Ighoho

    Sunday Ighoho

    Asalin hoton, SIAF

    Gwamnatin Benin ta saki jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya Sunday Ighoho.

    An saki Ighoho domin ba shi damar zuwa ganin likita a asibiti bisa sharaɗin cewa ba zai bar asibiti ba ko Cotonou saboda wani dalili, kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyinsa Yomi Aliyu, ya tabbatar wa BBC.

    Ya ce Farfesa Wole Soyinkaɗaya daga cikin shugabannin Yarbawa ya taimaka aka Sunday Ighoho domin zuwa asibiti.

    A watan Yulin 2021 aka kama Sunday Ighoho mai da’awar kafa ƙasar Yarbawa ta Oduduwa.

    Ana tuhumarsa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, da laifin shiga kasar ba bisa ka'ida ba tare da kokarin tayar da husuma, amma ya musanta hakan.

    Igboho ya tsere ne daga Najeriya ya tsallaka Benin bayan samamen da 'yan sanda suka kai gidansa a farkon watan Yulin 2021, inda aka kashe biyu daga cikin yaransa.

  5. Direbobin babur mai ƙafa uku na yajin aiki a Damagaram

    Ƙungiyar direbobin babur mai ƙafa uku a A jihar Damagaram da ke sun tsunduma yajin aiki na kwanaki biyu.

    Ƙungiyar direbobin na zargin gwamnan jihar ta Damagaram da yin katsalandan a cikin lamarin shari’a da ke tsakanin kungiyar da kuma direbobin motocin haya.

    Jahar ta Damagaram dai na da aƙalla babura masu kafa uku sama da 4,000, kuma matasa ne ke aiki da su, domin samun abubuwan gudanar da rayuwarsu a zirga-zirga a cikin gari

    Ku saurari rahoton Abdou Halilou

    Bayanan sautiDirebobin babur mai ƙafa uku na yajin aiki a Zinder
  6. Yadda Pantami ya ɗana motar da aka haɗa a Najeriya mai amfani da lantarki

    Malam Pantami

    Asalin hoton, @FMoCDE

    Ministan sadarwa na Najeriya Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ya ɗana motar da ke amfani da lantarki da aka haɗa a Najeriya (Hyundai Kona).

    Ma’aikatar sadarwa ta wallafa hotunan ministan, kuma ta ce ya yi ɗanin motar ne bayan ya karbi baƙuncin shugaban Hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya (NADDC), Jelani Aliyu a wata ziyara da ya kai masa.

    Malam Pantami

    Asalin hoton, @FMoCDE

    Malam Pantami

    Asalin hoton, @FMoCDE

  7. Birtaniya da Canada da Netherlands sun ƙulla ƙawancen taimaka wa Ukraine

    Shugabanin Birtaniya da Canada da Holland

    Birtaniya da Canada da kuma Netherlands sun sanar da kafa kawance domin taimakawa Ukraine da Rasha ta abkawa.

    Firaminista Boris Johnson ya gana da takwarorinsa na Canada da Holland Justin Trudeau da Mark Rutte a Landan, inda suka yi kira ga sauran ƙasashe da su shiga ƙawancen.

    Mista Johnson ya ce ƙungiyar za ta ba da Ukraine taimakon soji da na tattalin arziki a fadan da Ukraine ke yi da Rasha, don tabbatar da abin da ya kira. "gazawar Putin."

    Ya ce shugaba Putin ya yi kuskure kan manufar Ukraine da haɗin kan ƙasashen yammacin Turai.

    Boris Johnson ya ba da sanarwar karin dala miliyan 230 na taimakon Burtaniya ga Ukraine, yayin da Justin Trudeau ya ce Canada za ta ƙara ƙaƙaba takunkumi kan karin 'yan Rasha guda 10.

  8. Nan gaba kadan za a fara zagaye na uku na tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine

    Wani mai bai wa shugaban Ukraine shawara Mikhail Podolyak, ya ce nan gaba kadan ne za a fara zagaye na uku na tattaunawa tsakanin wakilan Rasha da Ukraine a Belarus.

    Kodayake babu tabbas a game da halartar tataunawar daga bangaren Rasha.

    A wani labarin kuma ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya ce takarorinsa na Rasha da Ukraine zasu gana a birnin Antalya a ranar Alhamis.

    Mista Cavusoglu ma zai halarci tattaunawar.

    Tattaunawar da aka yi a baya ba ta amfanar komai ba saboda Rasha ta hakikance cewa ba za ta daina mamaye Ukraine ba har sai an biya mata bukatunta.

    Tun da farko Firaminstan India Narendra Modi ya bukaci Vladimir Putin da ya samu ya tataunawa kai tsaye da takaransa na Ukraine Volodymr Zelensky.

    Volodymr Zelensky.

    Asalin hoton, EPA

  9. Birtaniya ba ta yi maraba da 'yan Ukraine masu son shiga kasarta ba

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi watsi da kiraye-kirayen a ake yi cewa gwamnatinsa na sauwaka wa 'yan Ukraine da ke kokarin tserewa daga yakin da ake yi a kasarsu.

    Ya ce Birtaniya "kasa ce mai tausayi da kyautatawa" amma tana son ta hana kwararar da masu shiga kasar ke yi.

    Firaministan ya kara da cewa "A ganina abu ne mai kyau, ganin yadda al'amura ke kara rikicewa a Ukraine, mu tabbatar da muna iya tantance wadanda ke son shigowa kasarmu".

  10. Fadar Kremlin ta bukaci Ukraine ta amince yankin Crimea mallakin Rasha ne

    Taswirar Ukraine

    Rasha ta ce za ta iya kawo karshen ayyukan soji da ta ke yi "a duk lokacin da ta so" idan Ukraine ta cimma wasu sharuddan da Rashar ta gindaya.

    Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce tilas Ukraine ta amince cewa yankin Crimea mallakin Rasha ne, kuma Donetsk da Luhansk kasashe masu zaman kansu ne.

    Baya ga wadannan, Peskov ya kuma ce tilas Ukraine ta sauya tsarin mulkinta kuma ta yi watsi da niyyar shiga wata kungiya (a misali Nato).

    Ya kara da cewa Rasha za ta kammala tsaftace Ukraine, kuma sai bayan an biya dukkan wadannan bukatun ne "ayyukan sojin" da dakarunta ke yi za su kawo karshe "nan take".

    Kakakin Fadar Kremlin din ya nanata cewa Rasha ba ta da niyyar mallake kasar Ukraine fiye da wanda ta yi a yanzu.

    Rasha ta kwace yankin Crimea ne a watan Maris din 2014, kuma bayan wasu makonni ta goyi bayan 'yan awaren da ke kokarin ballewa daga a yankunan Donetsk da Luhansk na gabashin Ukraine.

  11. Abubuwan da suka faru kawo yanzu a yau

    Justin Trudeau, Boris Johnson and Marc Rutte, the leaders of Canada, the UK and the Netherlands are meeting in London

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Justin Trudeau da Boris Johnson da Marc Rutte, shugabanin Canada, da Birtaniyya da kuma kasar Holland yayin da suke ganawa a birnin Landan

    Idan yanzu ka fara bibiyar mu, ga abubuwan da suka auku a takaice a rana ta 12 ta mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

    • Za a ci gaba da tattauna a karo na uku tsakanin jami'an Rasha da na Ukraine daga karfe uku agogon Najeriya, kamar yadda jami'an kasar Ukraine cikin wata sanarwa
    • An soki wani sabon shirin tsagaita wuta a Ukraine wanda zai ba fararen hular kasar damar ficewa ta wasu hanyoyin da za a tsagaita yakin da ake yi - inda Birtaniya ta kira matakin "abu mai daure kai", kuma Ukraine ta kira shirin "abin takaici".
    • A karkashin tsarin na Rasha, fararen hula da ke tserewa yakin a Kyiv za su sami damar icewa zuwa Belarus, inda wadanda ke Kharkiv kuwa za su iya wucewa zuwa cikin Rasha ne kawai
    • Hanyoyin da aka samar a biranen Mariupol da Sumy za su nufi wasu biranen kasar Ukraine da na kasar Rasha
    • Ukraine ta ce dakarun Rasha na kai wa asibitoci da makarantu hari, kuma ta ce hare-haren sun rutsa da fararen hula
    • Rasha ta musanta kai wa fararen hula hari, kuma ta ce tana wani "aikin soji na musamman ne" kan "masu tsattsauran ra'ayi da 'yan nazi"
    • Farashin man fetur ya yi tashin goron zabi yayin da farashin gangar man fetur ya a kasuwar duniya ya kai dalar Amurka 139. Farashin man fetur a Birtaniya ya kai pence 155 ga kowace lita akron farko
    • Firaministan Birtaniya Boris Johnson na tattaunawa da firaministocin Canada da na Holland a Landan, a daidai lokacin da kasashen yammacin Turai ke shirin amincewa da kara sakawa Rasha takunkumai
  12. Macron ya yi Allah-wadai da halayen da Putin ke nunawa kan yaƙin Ukraine

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kasar Faransa,Emmanuel Macron ya yi Allah-lawadi da abin da ya kira ''rashin kyakkyawan zato ta fuskar ɗa'a da siyasa'' da Putin ke nunawa wajen bayar da kafar kai wa jama'a taimakon da ya dace.

    Tun da farko Ukraine ta yi watsi da batun bude hanya jama'a su shiga Rasha da Belarus yana mai cewa sam bai dace ba.

    Wata babbar jami'a a Ukraine Iryna Vereshchuk ta ce akwai jama'a da dama na cikin hadari a Ukraine matukar shugabannin kasashen duniya ba su yi ani abu na tabbtar da cewa an basu damar gujewa akin ba.

    Ta ce "na kira shugabannin kasashen duniya, kamar Emmanuel Macron wanda ke kokarin taimakawa, sannan na kira Boris Johnson, na kira Joe Biden, ya kamata su taimaka wajen tabatar da ficewar jama'a domin ceton rayukan dubban mutane ciki har da yan kasashen waje."

    Shugaba Macron na cikin shugfabannin duniyar da suke magana da Putin.

  13. 'Yan addinin Buddha a Sri Lanka na zaman makokin mutuwar giwa mai shekara 68

    giwa

    Asalin hoton, SAVE ELEPHANT FOUNDATION

    Masu kaifin addinin Buddha a Sri Lanka na zaman makokin mutuwar wata shahararriyar giwa da ta mutu tana da shekara 68.

    Ana zaman makokin ne inda mabiya addinin Buddhan ke zuwa domin bankwanan da giwar mai suna Nadungamuwa Raja inda suke mata adu'a tare da taɓa haurenta.

    Shugaban kasar, Gotabaya Rajapaksa, ya bayar da umarnin da a adana gawar giwa don tarihi.

    Giwa Raja ta kasance mai mutukar muhimmanci a cikin giwayen da ke kasar saboda irin tarihin da ta bari a tsawn rayuwarta.

    A shekarar 2015 aka ware mutanen da za su rinka kula da giwar bayan da wani hadari ya rutsa da ita.

  14. Wata ƙungiyar agaji ta Afirka ta Kudu za ta aika wa Ukraine tallafi

    AFP

    Asalin hoton, Gift of the Givers

    Wata ƙungiyar agaji ta Afirka ta Kudu Gift of the Givers, ta ce za ta aika wa Ukraine tallafi, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa fiye da fararen hula miliyan ɗaya ne suka gudu daga ƙasar tun bayan kutsen da Rasha ta yi.

    A wata sanarwa, ƙungiyar ta ce za ta sanar da kayayyakin kula da lafiya da na sauran abubuwan buƙata don taimakon mutanen da yaƙin ya ɗaiɗaita a Ukraine.

    Sanarwar ta ce: "Ana ta tattauna wa da kamfanonin harhaɗa magunguna, da ƙungiyoyin lafiya don su goyi bayan abin."

    Za a aika wasu daga cikin tallafin Kharkiv inda a can ne Rasha ta fi kai hare-hare a unguwannin mutane.

    Kazalika Gift of the Givers za ta bayar da kuɗi a ƙoƙarin da ake yi na kwashe ɗaliban Afirka ta Kudu daga Ukraine don mayar da su gida.

    A baya wannan ƙungiya ta taɓa aika tallafin agaji zuwa Syria a lokutan yaƙi.

  15. Farashin man fetur ya yi tashin goron zabi a Birtaniya

    Petrol pump

    Asalin hoton, Getty Images

    A dalilin mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, kamfanin sufuri na AA ya sanar da cewa a karion farko, farashin man fetur ya kai pence 155 na kudin Birtaniya - matakin da ya kai kudi galan daya na man fetur ya kai fam bakwai.

    A yanzu, cika tankin motar da tankinta ya kai lita 55 zai sa a kashe karin kusan fam 17 idan aka kwatanta da yada farashin mai yake a bara, inda ya tashi daga fam 68.60 zuwa fam 85.59 a yau.

    Idan aka sauya kudin zuwa yadda ake sayen naira akasuwar bayen fage, farashin cika tankin mota mai cin lita 55 ya kai naira 66,760 ke nan.

    A jiya Lahadi farashin man ya kai pence 155.62 ga kowace lita, inda man diesel kuwa ya kai pence 161.28.

    Masana harkar makamashi na cewa akwai yiwuwar farashin zai ci gaba da tashi.

  16. Najeriya ta haramta wa 'yan kasarta zuwa Ukraine domin yakar Rasha

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Najeriya ta ce ba za ta ƙyale 'yan kasarta su shiga cikin mayakan da ke yaki da Rasha a kasar Ukraine ba.

    Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni da ke cewa an fara yi wa 'yan kasar 'yan sa kai rijista domin su taimaka wa sojojin Ukraine a mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

    Ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce ofishin jakadanci Ukraine da ke kasar ya musanta taka wata rawa a wannan abin takaicin.

    Sai dai ofishin jakadancin ya tabbatar cewa wasu 'yan Najeriya sun sanar da shi cewa a shirye suke a yi wannan yakin da su.

    Ofishin jakadancin ya kuma nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya bukaci dukkan dan Najeriyar da ke son shiga yakin da ya biya dalar Amurka 1,000 a matsayin kudin tikitin jirgin sama da na biza.

    Wannan matakin na Najeriya na zuwa ne bayan kwana daya da kasar Senega ta gargadi 'yan kasarta masu sha'awar tafiya Ukraine da su guji daukan wannan matakin.

    Ta umarci jakadan kasar Ukraine da ya sauke wasu bayanai da ofishinsa ya wallafa a Facebook yana kira ga 'yan Senegal su yi rajista domin a tafi da su can su yi yaki.

  17. Kamfanin taki na duniya ya ce yakin Ukraine na barazana ga samar da abinci a duniya

    Shugaban kamfanin taki mafi girma a duniya, ya shaida wa BBC cewa yakin da ake yi a Ukraine babbar barazana ce ga samar da abinci a duniya saboda Rasha ce sahun gaba a samar da kayan hadin taki.

    Shugaban kamfanin Yara International, Svieen Toora Houlsether, ya ce wannan kadai zai sanya farashin kayan abinci su yi tashin gwauron zabbi.

    Tun da fari Babar Balock na shirin samar da abinci na MDD ya ce lallai 'yan gudun hijirar Ukraine na bukatar taimako.

    Ya ce "yawancin wadanda suka baro Ukraine mata ne da kananan yara, suna shafe sa'o'i akan layi, wasu har kwanaki suna bukatar taimakon kasashe makwafta da abinci da ruwan sha.

    "Ga tsakanin sanyin da ake fama da shi. Lamarin ya munanan."

  18. Mamayar Ukraine: China ta mara ma Rasha baya

    China - Russia relatiuons
    Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladimir Putin yayin wata ganawa da yayi da Shugaba Xi Jinping na China

    Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya bayyana goyon bayan kasarsa ga Rasha kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.

    Jaridar Vanguard ta Najeriya ta wallafa wannan rahoton, wanda a ciki ministan ke cewa: "Duk yadda yanayin siyasar duniya zai rikice, China da Rasha za su ci gaba da renon dangantakarsu mai matukar muhimmanci."

    Mista Wang ya bayyana China da Rasha a matsayin mawabta kuma makusantan kasashe masu muradu iri daya, ya kuma ce "dangantaka ce ta kut-da-kut wadda kusan babu irinta a duniya."

  19. Kotu ta ki bayar da belin Abba Kyari

    Abba Kyari a gaba babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan zamanta na yau

    Babbar kotu tarayya da ke Abuja wadda ke sauraren karar da hukumar NDLEA ta shigar tana tuhumar babban jami'in dan sanda Abba Kyari da wasu mutum shida ta ki amincewa da bukatar da lauyoyinsa suka mika ma ta na a bayar da belinsa.

    Sai dai kotun ta ce za ta saurari bukatar a zamanta na gaba.

    Lauyan Abba Kyari ya shaida wa manema labarai a gaban kotun cewa kotun ta dage zamanta zuwa ranar Litinin 14 ga watan Maris domin sake duba batun belin.

    Amma ya ki cewa komai game da abubuwan da suka wakana cikin kotun, cii har da mika wuyan da wasu mutum biyu cikin mutum shidan da ake tuhuma da aikata laifukan suka yi.

  20. Indiya ta roƙi Putin ya tattauna da Ukraine

    Putin da Modi

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya roƙi shugaban Rasha Vladimir Putin da ya tattauna kai tsaye da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.

    Kamfanin dillancin labara na Reuters ne ya ruwaito hakan daga wata majiya ta gwamnatin Indiya.

    "Shugaba Putin ya yi wa Firaminista Modi ɗan taƙaitaccen jawabi kan halin da ake ciki na tattaunawar sulhu tsakanin tawagogin Rasha da Ukraine," a cewar majiyar, wacce ba ta so a ambaci sunanta gabanin fitar da sanarwa a hukumance.