Ƙarin 'yan Najeriya daga Ukraine 709 sun koma gida cikin dare

Asalin hoton, Nidcom
Ƙarin 'yan Najeriya 709 da suka maƙale sakamakon yaƙi a Ukraine sun sauka a Abuja a yau Lahadi daga Romania.
Matafiyan akasarinsu ɗalibai sun sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da misalin ƙarfe 12:30 na dare a jirgin Airpeace.
Wannan ne rukuni na uku da aka ɗebo daga ƙasashe maƙotan Ukraine da suka haɗa da Poland da Romania da Slovakia.
Hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta ce nan gaba kaɗan wani jirgin zai sauka a Abujar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X


