Buhari ya ce yanzu Osinbajo ne ke da wuƙa da nama
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Yanzu Osinbajo ne ke da wuƙa da nama – Buhari

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar ƙasar.
Shugaban ya faɗi haka ne a Abuja lokacin da zai taka jirgi zuwa London a ranar Lahadi.
Kafin ya hau jirgi, Buhari ya faɗa manema labarai a Abuja cewa mataimakin shugaban ƙasa ne zai ci gaba da tafiyar gwamnati idan baya nan, kamar yadda tsarin mulki ya yi tanadi.
Buhari ya tafi London ne domin ganin likitocinsa, kuma fadar shugaban na Najeriya ta ce, zai shafe tsawon mako biyu a can.
Buhari ya ce rashinsa ba zai shafi ayyukan gwamnati ba, domin yana sane da duk wani abin da ke faruwa ko da kuwa baya nan.
Yadda wasu masoya ƴan Ukraine suka yi aure a fagen yaƙi

Asalin hoton, Getty Images
Duk da ƴakin da ke yi amma wasu wasu masoya ƴan ƙasar Ukraine sun yi bikin aure irin na sojoji da aka gudanar a shingen bincike kusa da birnin Kyiv da ke fuskantar barazanar sojojin Rasha.
Magajin garin Kyiv - kuma tsohon zakaran damben boksin ajin masu nauyi na duniya - Vitaliy Klitschko, yana cikin waɗanda suka shaida auren.
Valery da Lysia, waɗanda suka shiga yaƙin Ukraine a matsayin ƴan sa-kai sun yanke shawarar bikin aurensu a fagen daga domin aurensu ya kasance wani labarin da za a tuna wata rana.

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta kama dubban ƴan ƙasarta masu zanga-zangar adawa da yaƙin Ukraine

Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Rasha ta ce sama da mutum 3,500 ne aka kama masu zanga-zangar adawa da yakin da Rasha ke yi a Ukraine.
An ce sama da mutun 5,000 ne suka yi fito zanga-zanga a Moscow da St Petersburg da sauran biranen Rasha.
Kungiyar da ke sa ido ta OVD ta ce ta tattara alƙalumma a wurare fiye da 50 a cikin Rasha, ciki har da Irkutsk a Siberiya da Vladivostok a gabas mai nisa.
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar suna yayata kalamai na adawa da yaƙi kuma suna bayyana cewa 'Ukraine ba maaƙiyarmu ba ce'.
Kungiyar OVD ta ce an tsare masu zanga-zangar adawa da yaƙin Ukraine sama da 12,000 tun lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamayar.

Asalin hoton, EPA
Zulum ya ce ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin Azumi

Asalin hoton, Borno Govt
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya yi alƙawalin cewa ƴan gudun hijirar Malam-Fatori za su koma garinsu kafin fara azumin watan Ramadan.
Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ziyarar gani da ido da tantance ayyukan jin-kai da ya kai karo na huɗu a garin Malam-Fatori a ranar Lahadi, kamar yadda sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ta bayyana.
“Iyalai 500 insha Allahu za su isa kafin azumin Ramadan, wannan ne lokacin da ya dace a mayar da su gidajensu na asali cikin aminci da mutunci kafin damina.” In ji Zulum.
A cewar sanarwar, Gwamnan ya bayyana cewa za a tallafa wa kowanne daga cikin wadanda aka dawo da su da kuɗi naira 100,000 a wani ɓangare na shirin sake raya al’umma.
Sanarwar ta ce za a sake tsukunar da mutanen da suka yi gudun hijira kuma suke zaune a garuruwan Bosso da Diffa da ke kan iyaka da Nijar tun 2014 da suka tsere wa hare-hare a ƙananan hukumomi 10 na arewacin Borno, a matsuguni na wuccin gadi.
Nakiya ta halaka sojojin Nijar biyar

Asalin hoton, Other
An kashe sojojin Nijar biyar a yankin Torodi da ke kudu maso yammacin ƙasar, bayan sun motar da suke ciki ta taka nakiya.
Ma’aikatar tsaron Nijar ta ce sojoji uku sun yi rauni a harin wanda ya faru a ranar Juma’a lokacin da motar da sojojin ke sintiri ta taka nakiya.
Jami’an na cikin ayarin sojoji 2,160 da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a kudu masu yammacin ƙasar kusa da kan iyaka da Burkina Faso.
Clarence Seedorf ya ce matarsa ta musuluntar da shi

Asalin hoton, @CLARENCESEEDORF
Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Holland, Clarence Seedorf ya musulunta, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Instagram, a ranar Juma'a.
Sojojin Rasha sun doshi Kyiv babban birnin Ukraine

Asalin hoton, Reuters
Sojojin Ukraine na ci gaba da ƙarfafa tsaron Kyiv yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da ƙoƙarin kutsawa cikin babban birnin kasar.
Sojoji sun yi ta tona ramuka tare da toshe hanyoyi ta amfani da tankokin yaki.
Hukumomin ƙasar sun ce ana ci gaba da luguden wuta a biranen uku da ke arewa maso yammacin Kyiv -- Bucha, Hostomel da Irpin.
Ana ci gaba da gwabza kazamin faɗa a yankin. Dakarun Rasha sun harba rokoki kan fararen hula a Irpin a lokacin da suke ƙoƙarinrin tserewa, inda suka kashe wata uwa da yara biyu tare da raunata mahaifinsu.
An kuma tarwatsa wata gada ta wuccin gadi da mutane ke ratsa kogi domin tserewa daga ƙasar.
Labarai da dumi-dumi, Rahotanni na cewa an kashe farar hula uku
Yayin da fararen hula ke ci gaba da guduwa daga garin Irpin na arewacin Kyiv, rahotanni na cewa an kashe mutum 'yan gida ɗaya.
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa harin da Rasha ta kai kan wata karyayyar gada ne ya yi ajalinsu.
Jaridar ta ce mutanen na ƙoƙarin hawa gadar ce a kusa da titi tare da sojojin Ukraine na raka su lokacin da lamarin ya faru.
Labarai da dumi-dumi, Yarjejeniyar tsagaita wuta ta sake karyewa
An dakatar da aikin kwashe fararen hula daga garin Mariupol da ke kudancin ƙasar a karo na biyu, a cewar ƙungiyar agaji ta Red Cross.
Dakarun Rasha da na Ukraine na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta don bai wa fararen hula damar tserewa daga garin, bayan irin wannan yarjejeniyar ta karye a jiya Asabar.
Tun farko an shata hanyoyin da za a bi wajen kwashe mutanen kafin yarjejeniyar ta wargaje.
Buhari ya tafi Landan

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanya zuwa birnin Landan a yau Lahadi.
Fadar shugaban ta sanar cewa ya je ne domin a duba lafiyarsa.
Tun a ranar 1 ga watan Maris aka sanar cewa Buhari zai je ganin likita a Landan bayan ya kammala halartar taro a Kenya, amma sai ya koma Abuja daga Nairobi.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, State House
Romania za ta karɓi ɗaliban Najeriya daga Ukraine su ƙarasa karatunsu a ƙasar

Asalin hoton, MFA
Gwamnatin Romania ta yi tayin bai wa ɗaliban Najeriya damar ci gaba da karatu a jami'o'in ƙasar bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake tafkawa a ƙasar, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Najeriya.
Babban sakatare a ma'aikatar, Gabriel Aduda, ya ce ministan ilimi na Romania wadda maƙociyar Ukraine ce, shi ne ya bayyana hakan.
Mista Aduda ya ƙara da cewa yanzu haka suna tattaunawa da sauran maƙotan ƙasashe kamar Poland da Hungary da Girka don su bai wa 'yan Najeriya irin wannan damar.
'Yan Najeriya kusan 2,000 ne aka tabbatar sun tsallaka ƙasashe maƙotan Ukraine a yunƙurinsu na samun mafaka daga yaƙin da aka fara fafatawa ranar 24 ga watan Fabarairu.
Tuni aka kwaso 'yan ƙasar kusan 1,000 amma har yanzu akwai ɗalibai a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnati don su koma gida.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hanyoyin da fararen hula za su fice daga filin yaƙi

Asalin hoton, Reuters
A ci gaba da kawo rahoton tsagaita wuta a yankin Mariupol da ke kudu maso gabashin Ukraine, hukumomin yankin sun ce an fara shirin kwashe fararen hula bayan sanarwar tsagaita wutar.
An fara shirin awa ɗaya da ta wuce, amma ba mu da tabbas ya zuwa yanzu ko motoci sun isa wurin ko kuma sun fara ɗibar mutane.
Za a gudanar da ayyukan ne ta hanyoyin da sojojin Rasha suka shata wanda kuma dakarun Ukraine suka amince.
Rasha ta katse tashar talabijin ta BBC a ƙasar

Asalin hoton, PA Media
Kamar yadda muka yi ta ba da rahoto, hukumomi a Rasha sun toshe shafukan kafofin yaɗa labarai na ƙasashen Yamma, ciki har da BBC.
Yanzu kuma an katse tashar talabijin ta BBC mai yaɗa labarai ga duniya wato BBC World News a Rashar.
Ku taimake mu mu koma gida - 'Yan Najeriya da suka maƙale a Ukraine na neman agaji

Asalin hoton, Channels TV
'Yan Najeriya da suka maƙale a Ukraine na neman agajin gwamnatin ƙasarsu don su koma gida sakamakon yaƙin da ake yi a ƙasar.
Wani bidiyo da ya ɓulla a shafukan zumunta ya nuna dandazon ɗaliban na ife-ifen neman taimako, suna cewa "we want to go home" - "muna so mu koma gida".
Matsan waɗanda suka ce ɗalibai ne a Jami'ar Sumy, sun ce yanzu haka ba su da ruwan sha, ba wuta sannan abincinsu ya kusa ƙarewa.
"Yanzu mun kwana kusan uku ba mu yi wanka ba," in ji wata ɗaliba da ta yi magana a bidiyon.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An kama masu zanga-zanga 600 a Rasha - Ƙungiyar fafutika

Asalin hoton, EPA
Masu zanga-zanga fiye da 600 aka kama a garuruwan Rasha 21, a cewar wata ƙungiya mai lura da lamurra OVD-Info, bayan sun fito nuna ƙin jinin yaƙin da ƙasarsu ta ƙaddamar a Ukraine.
Ƙungiyar ta ambato kafofin yaɗa labarai na Rasha na cewa an tsare mutum fiye da 200 a birnin Novosibirsk da ke yankin Siberia.
Jagoran adawa Alexi Navalny ya yi kiran a fito zanga-zanga a manyan dandali da ke ƙasar da ƙarfe 2:00 agogon ƙasar (12:00 agogon Najeriya) a biranen Moscow da St Petersburg.
An daɗe ana tsare masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Rasha. OVD-Info ta ce aƙalla mutum 8,000 aka tsare ko aka kama a Rasha tun bayan ƙaddamar da yaƙi a Ukraine kwana 11 da suka wuce.
Ukraine ta yi iƙirarin kashe sojojin Rasha 11,000
Ukraine ta yi iƙirarin cewa ta kashe dakarun Rasha fiye da 11,000 tun bayan da Rashar ta ƙaddamar da hare-hare a kanta ranar 24 ga watan Fabarairu.
Sai dai ba ta bayyana sabon adadin nata sojojin da aka kashe ko jikkata ba.
A jiya Asabar, Ukraine ta ce sojojin Rasha da ta kashe sun zarta 10,000.
Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da ingancin iƙirarin ba.
Labarai da dumi-dumi, Rasha ta ce ta lalata sansanin sojan Ukraine da makamai masu linzami
Rasha ta kai hare-hare tare da lalata wani sansanin sojan sama na Ukraine a Starokostiantyniv da makamai masu linzami, a cewar ma'aikatar tsaro ta Rasha.
"Dakarun Rasha na ci gaba da kai wa cibiyoyin sojan Ukraine hari," in ji Igor Konashenkov mai magana da yawun ma'aikatar tsaro.
"Da safiyar 6 ga watan Maris, an kai hare-hare da makamai masu linzami masu nisa. An lalata sansanin sojan Ukraine a Starokostiantyniv."
Ya ƙara da cewa an lalata makamin S-300 na Ukraine a hare-haren.
Kazalika, Rasha ta harbe jiragen Ukraine 10 ciki har da na helikwafta cikin awa 24 da suka wuce, a cewarsa.
Labarai da dumi-dumi, 'Yan gudun hijira fiye da miliyan 1.5 ne suka fice daga Ukraine - MDD
Fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka tsallaka zuwa ƙasashe maƙotan Ukraine cikin kwana 10 da suka wuce, kamar yadda kwamashinan gudun hijira na MDD Filippo Grandi ya bayyana.
Wannan ne adadin 'yan gudun hijira mafi yawa a nahiyar Turai tun bayan Yaƙin Duniya II.
Labarai da dumi-dumi, An sake sanar da tsagaita wuta a Mariupol
An sake sanar da wata tsagaita wutar a garin Mariupol mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin Ukraine daga 10:00 na safe zuwa 9:00 na dare agogon Ukraine (9:00-11:00 agogon Najeriya), a cewar majalisar yankin.
Fararen hula za su samu damar ficewa ta hanyoyin da aka amince daga 12:00 agogon ƙasar (11:00 agogon Najeriya).
Irin wannan tsagaita wutar da aka sanar jiya Asabar ba ta yi aiki ba jim kaɗan bayan ayyana ta.
