Yaƙin Ukraine: An bai wa mazauna birnin Kyiv bindigogi don kare ƙasarsu
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Rasha da Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh and Umar Mikail
Mu kwana lafiya
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi, amma za ku iya ci gaba da karanta abubuwan da muka rawaito muku game da halin da ake ciki yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kan Kyiv babban birnin Ukraine.
Ku duba ƙasa domin samun labaran.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku gobe don samun wasu sababbin rahotannin.
Labarai da dumi-dumi, Amurka za ta saka wa Shugaba Putin kansa takunkumi
Rahotanni daga Fadar White House na cewa Amurka na shirin ƙaƙaba wa Shugaban Rasha Vladmir Putin takunkumi shi kansa da kuma Ministan Harkokin Waje Sargei Lavrov.
Gidan talabijin na CNN ya ruwaito wasu majiyoyi na cewa nan gaba kaɗan za a saka wa shugaban kai-tsaye takunkumi.
Tuni Washington ta saka wa bankuna da wasu manya-manyan Rashawa takunkumai kan kadarorinsu da kuma hana su tafiye-tafiye.
Ita ma Tarayyar Turai ta ce za ta ƙaƙaba wa Putin da Mista Lavrov takunkumai amma kan kadarorinsu kawai ban da hana tafiye-tafiye.
Yaƙi gazawa ce, yana mayar da duniya baya - Fafaroma Francis
Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Francis ya wallafa wani saƙo na ƙin jinin yaƙi a shafinsa na Twitter a harshen Ukraine da Rashanci da kuma Ingilishi, yana mai cewa duk wani yaƙi na mayar da duniya baya fiye da yadda ya same ta".
"Yaƙi gazawa ce ta siyasa da kuma ɗan Adam," a cewarsa, yana mai kwatanta shi da "abin kunya, abin alfahari ga miyagu".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Nato za ta ƙara yawan dakaru a gabashin Turai
Shugabannin ƙungiyar tsaro ta Nato sun ce za su tura ƙarin dakaru zuwa gabashin Turai bayan Rasha ta afka wa Ukraine.
"Bai kamata waɗannan ƙarairayin na Rasha su ruɗi kowa ba," a cewar shugabannin 30 cikin wata sanarwa.
Nato ta yi kira ga Rasha ta janye dukkan dakarunta daga Ukraine sannan "ta kauce wa tsokanar da ta zaɓa".
"Matakin da Putin ya ɗauka na kai wa Ukraine hari abu ne mai haɗari wanda Rasha za ta ɗanɗana kuɗarta ta hanyar tattalin arziki da kuma siyasa a shekaru masu zuwa," a cewar sanarwar.
Game da tura dakaru zuwa gabashin Turai, Nato ta ce "za ta tura dukkanin dakarun da suka dace don tabbatar da tsaro".
INEC za ta yi taro don sanin yadda za ta yi aiki da sabuwar dokar zaɓe
Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓe ta INEC a Najeriya ta ce za ta gudanar da taro na musamman ranar Asabar da zimmar sanin yadda za ta aiwatar da sabuwar dokar zaɓe da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu a babban zaɓe na 2023.
Kwamashinan hukumar da ke kula da wayar da kai, Festus Okoye, ya ce dokar zaɓen ta 2022 na ƙunshe da tanade-tanade da za su inganta zaɓe a Najeriya.
"Duk da irin ƙayyade lokuta da sabuwar dokar ta yi, INEC za ta ci gaba da shirinta cikin zumuɗi bisa tsarin dokar," in ji Mista Okoye cikin wata sanarwa.
A yau Juma'a ne dai yayin wani ƙwarya-ƙwaryar biki a fadarsa, Shugaba Buhari ya sanya wa dokar hannu bayan ta shafe kwana kusan 25 a gabansa.
Tun lokacin da majalisun dokokin ƙasar suka miƙa wa Buhari daftarin dokar da suka yi wa kwaskwarima INEC ta ce ba za ta fito da jadawalin babban zaɓe na 2023 ba har sai ya saka mata hannu.
Makamai masu linzami sun fara faɗowa birnin Kyiv
Babbar wakiliyar BBC kan harkokin ƙasashen duniya Lyse Doucet ta wallafa a shafinta na Twitter cewa makamai masu linzami sun fara dira a birnin Kyiv.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, EU za ta saka wa Shugaba Putin da ministansa Sargei Lavrov takunkumi
Tun farko mun ba da rahoto cewa Tarayyar Turai (EU) za ta sanya wa jagoran Rasha Vladmir Putin da ministansa na harkokin waje Sargei Lavrov.
Yanzu haka lamarin ya tabbata.
Sai dai BBC ta fahimci cewa kadarorinsu za a riƙe ba hana su tafiye-tafiye za a yi ba.
"Bari na bayyana cewa shugabannin da EU ta taɓa saka wa takunkumi shi ne Bashir al-Assad na Syria da Lukashanko na Belarus da kuma yanzu Putin," a cewar Josep Borrell shugaban sashen tsare-tsare na EU.
Euefa ta ɗauke wasan ƙarshe na Champions League daga Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai watau Champions League na bana a Paris, bayan da aka dauke daga Rasha saboda kutsen da kasar ta yi a Ukraine.
A baya an shirya buga wasan mafi girma a Turai a filin wasa na Gazprom Arena da ke St Petersburg a ranar 28 ga watan Mayu.
Amma a yanzu hukumar kwallon Turai - UEFA ta ce a filin wasa na Stade de France da ke Paris.
Hukumar Uefa ta nuna godiya ga shugaban Faransa, Emmanuel Macron saboda "nuna goyon baya da taimakon da yake bai wa kwallon kafa a Turai."
Labarai da dumi-dumi, Har yanzu muna nan a cikin ƙasarmu - Shugaban Ukraine Zelensky
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya wallafa wani bidiyo da aka ɗauka a kan titunan birnin Kyiv bayan yaɗa jita-jita a kafofin yaɗa labaran Rasha cewa ya gudu daga ƙasar.
"Ga mu nan duka a nan," a cewarsa kewaye da masu ba shi shawara da firaministansa.
"Muna kare 'yancin kanmu ne da ƙasarmu, kuma za mu ci gaba da yin hakan."
An wayi garin yau Juma'a da sojojin Rasha na kunnawa cikin birnin na Kyiv bayan sun shafe tsawon ranar Alhamis suna fafatawa da dakarun Ukraine a kewayensa.
Za mu mayar da zazzafan martani idan Sweden ko Finland ta shiga NATO - Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi gargaɗin cewa idan har Finland ko Sweden suka shiga ƙungiyar tsaro ta Nato Rashar za ta mayar da martani mai zafi.
Da take magana yayin wani taron manema labarai a Moscow, Maria Zakharova ta yi gargaɗi cewa yunƙurin ɗaya daga cikin ƙasashen na shiga Nato "zai jawo zazzafan martanin soja da na siyasa da zai sa ƙasarmu ta ɗauki matakin da ya dace," kamar yadda kamfanonin labarai na Rasha suka ruwaito.
"Muna kallon ƙoƙarin gwamnatin Finland na ƙulla ƙawancen da ba na soja ba a matsayin hanyar inganta zaman lafiya a arewacin Turai," in ji Zakharova.
Duk da cewa Finland na aiki da Nato a wasu lamuran kuma tana harlartar taron yau a Brussels, har yanzu ba ta bayyana shiga ƙungiyar ba a hukumance.
A watan da ya gabata ne Firaminista Sanna Marin ta ce "akwai yiwuwar" Finland za ta nemi shiga Nato kafin mulkinta ya zo ƙarshe.
Dokar zaɓe: Buhari na son a goge sashen da ya ce masu muƙaman siyasa su sauka kafin zaɓe
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.
Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.
Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga muƙamansu kafin babban zaɓe na 2023.
Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe "kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu".
"Sai dai abin ba haka yake ba... a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri'a a manyan tarukan jam'iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe," in ji shugaban.
Buhari ya shafe kusan kwana 25 kafin ya sanya wa dokar hannu, wadda 'yan majalisar suka yi wa kwaskwarima sau biyu kafin ya amince da ita.
Shugaban Turkiyya ya soki martanin da Nato ta yi kan rikicin Rasha da Ukraine
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya soki irin martanin da Nato ta yi kan mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, inda ya ce, ya kamata a ce ƙawancen ya dauki mataki fiye da wanda ya dauka a yanzu.
Da yake magana a birnin Santanbul, shugaban ya kara da cewa, Nato da kasarsa Turkiyya wadda mamba ce a kungiyar, tare da Taryyar Turai, sun gaza yin abin da ya kamata a kan rikicin.
Ya ce: "Kamata ya yi NATO ta dauki tsattsauran mataki, ba kamar abin da ta yi ba yanzu.
"Mun yi kyakkyawar tattaunawa da Stoltenberg. A yayin wannan tattaunawa, mun gaya musu matsayinmu. "Yin Allah-wadarai da abin da Rasha ta yi ko alama bai isa ba."
Ya bayyana fatansa na ganin Nato a yayin taron da za ta yi nan gaba a yau Juma'a za ta dauki mataki na gasken-gaske.
Kotun Jihar Legas ta yanke wa Evans hukuncin ɗaurin rai da rai
Asalin hoton, Other
Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta yanke wa riƙaƙƙen wanda ake zargi da garkuwa da mutane Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans hukuncin ɗaurin rai da rai.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an yanke wa Evans tare da muƙarrabansa Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifi kan wasu zarge-zarge biyu waɗanda suka haɗa da haɗa baki domin aikata laifi da kuma garkuwa da mutane.
Alƙali Hakeem Oshodi wanda ya yanke hukuncin, ya kama mutum ukun da laifin garkuwa da babban daraktan kamfanin haɗa magunguna na Maydon Pharmaceuticals Limited wato Donatus Dunu.
Ya bayyana cewa akwai cikakkun hujjoji da suka tabbatar da suna da laifi.
Ukraine ta bayar da bindigogi 18,000 ga ƴan ƙasarta masu aikin sa kai
Asalin hoton, AFP via Getty Images
A daidai lokacin da dakarun Rasha ke ƙara matsawa cikin babban birnin Ukraine wato Kyiv, hukumomin Ukraine ɗin na kira ga ƴan ƙasar da su yi duk mai yiwuwa domin kare ƙasarsu daga kutsen Rasha.
Mai bayar da shawara a ma'aikatar harkokin cikin gida na ma'aikatar tsaro ta Ukraine Vadym Denysenko, ya ce tuni aka bayar da bindigogi masu sarrafa kansu 18,000 ga ƴan sa kai waɗanda ke son kare babban birnin ƙasar.
Ma'aikatar tsaro ta ƙasar da ma'aikatar harkokin cikin gida duk sun roƙi jama'ar ƙasar da su ankarar da hukumomin ƙasar idan suka ga gittawar dakarun Rasha haka kuma a kai musu hari da bam ɗin fetur na kwalba.
Ƴan Ukraine na fama da ƙarancin mai da kuɗi da kayan kula da lafiya
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa 'yan Ukraine da suka tsere daga gidajensu, saboda yaƙin da ake yi na fuskantar ƙarancin mai da kuɗi da kayan kula da lafiya.
Mutane da yawa ne ke ta gudun tsira, kafin dakarun Rasha da suke durfafawo su kai ga inda suke.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta yi kiyasin cewa kusan mutum 100,000 tuni sun rabu da gidajen, amma kuma hukumar na ganin wasu mutanen kusan miliyan biyar za su yi kokarin ficewa daga kasar zuwa waje yayin da fadan ke kara rincabewa.
Ministan harkokin waje na Hungary ya ce, akwai dogayen layukan motoci, da su kai tsawon kilomita biyar a kan iyakar kasarsa da Ukraine da Poland.
Kuma ta ce tuni mutum kusan 29,000 sun riga sun tsallaka cikinta daga Ukraine a jiya Alhamis.
Birtaniya ta yi watsi da kiran saka dokar hana jiragen sama wucewa a kan Ukraine
Ministan Tsaro na Birtaniya ya yi watsi da kiran da ake yi na a sa dokar hana jiragen sama wucewa a kan Ukraine.
Ben Wallace ya shaida wa BBC cewa, idan da jiragen yaki na Birtaniya za su kai hari kai tsaye a kan jiragen sama na Rasha, hakan zai haddasa yaki tsakanin Rasha da Nato a fadin Turai.
Sai dai ya yi alkawarin cewa za su yi duk abin da za su iya wajen cika bukatar Ukraine din ta aika mata da kayan yaki da tallafi.
Can kuma a wani bangaren gwamnatin Jamus ce za ta kara yawan kudaden da take kashewa a harkar tsaro bayan da kwamandan sojinta na kasa, ya ce kasar tana kamfar kayayyakin yaƙi, ta tunkari barazanar Rasha.
Hotunan yadda ƴan Ukraine ke neman mafaka a wurare
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tashoshin jiragen ƙasa na birnin Kyiv sun cika maƙil
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutane da dabbobi duka suna neman mafaka domin guje wa harin ba-zata
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutane na ta fakewa a wuraren ɓoyewa da dama domin guje wa harin bam.
Yadda motocin sojin Rasha ke shiga Kyiv babban birnin Ukraine
Bayanan bidiyo, Yadda motocin soji ke shiga Kyiv babban birnin Ukraine
Kamar yadda muka kawo muku rahotanni a yau, an ga motocin soji suna shiga arewacin babban birnin Kyiv babban birnin Ukraine.
BBC ta tabbatar da bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta da gaske a Obolon ne.
Ukraine za ta ɗauki har waɗanda suka haura shekara 60 aikin soja
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta wallafa saƙo a shafin Twitter inda take kira ga duka faren hula su shiga aikin soja inda ta ce ko da mutum ya haura shekara 60 ne.
A sanarwar da kwamandan dakarun ƙasar Yuri Galushkin ya fitar, abin da ake buƙata wajen ɗaukar sojan fasfo ne kaɗai da lambar ɗan ƙasa.
Tun da farko an samu ruɗani bayan an yi sanarwar sakamakon sojin sun ce mutum ko shekarunsa nawa zai iya shiga aikin, sai jama'a suka yi zaton ko ana nufin har da ƙananan yara, amma daga baya sun fito sun bayyana cewa suna nufin ko mutum ya haura shekara 60 ne zai iya shiga aikin.
Rasha ta haramta duka jiragen Birtaniya shiga ƙasarta
Asalin hoton, EPA
Rasha ta haramta duka wasu jirage da ke da alaƙa da Birtaniya shiga ƙasarta.
Wannan na zuwa ne bayan da Birtaniya ta dakatar da kamfanin jirgin saman Rasha wato Aeroflot daga shiga Birtaniya bayan Rashar ta kai hari ga Ukraine.
Rashar ta bayyana matakin nata a matsayin martani kan takunkuman da Birtaniya ta saka mata ta ɓangaren jiragen sama.