Yaƙin Ukraine: An bai wa mazauna birnin Kyiv bindigogi don kare ƙasarsu

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Rasha da Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. Sojojin Rasha sun shiga birnin Kyiv, in ji Ukraine

    Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda tankokin yaƙin Rasha ke tafiya a cikin Obolon, wanda yanki ne da ke arewa da ƙwaryar birnin Kyiv.

    A sa'o'in da suka wuce, ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta tabbatar da cewa dakarun Ukraine sun shiga cikin ƙasar.

    Ana kyauata zaton bidiyoyin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta mazauna birnin ne suka ɗauki hoton.

    BBC ta tabatar da wurin da aka ɗauki bidiyon Obolon ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. 'Rasha ta ragargaza wuraren farar hula 33 cikin sa'o'i 24'

    ..

    Ministan harkokin cikin gida na Ukraine ya bayyana cewa dakarun sojin Rasha na harin gwamman wuraren da farar hula suke a ƙasar.

    "Rasha ta ce ba ta kai hari ga wuraren da farar hula suke zaune ba sai dai an kai hari ga wuraren farar hula 33 cikin sa'o'i 24," kamar yadda Vadym Denysenko ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Dakarun Rasha sun shiga Kyiv babban birnin Ukraine inda suka bi ta arewa da gabashi da kudancin ƙasar.

    Hukumomi a Ukraine sun shaida cewa tuni dakarun Rasha suka shiga birnin, inda suke buƙatar ƴan ƙasar idan aka ce musu kule su ce cas.

  3. 'Ina kira ga gwamnatin Najeriya ta fitar da mu daga Ukraine'

    Bayanan bidiyo, Firdausi Muhammad Usman, ƴar Najeriya da ke karatu a Ukraine

    Kusan kowa a Ukraine na cikin tashin hankali sakamakon hare-hare da Rasha ta ƙaddamar a ƙasar.

    A babban birnin Kasar Kiv, ana ta jin karar jiniya domin yi wa jama'a gargadi , yayin da jerin gwanon motoci ke layin barin birnin, sannan kuma cincirindon mutane na ta ƙoƙarin neman mafaka a tashoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin kasa.

    Akwai ƴan Najeriya da dama da ke zaune a Ukraine kuma wasunsu sun shaida wa BBC cewa suna cikin tashin hankali.

    BBC ta tuntuɓi Firdausi Muhammad Usman, ƴar Najeriya da ke karatu a Ukraine kuma ta yi mana ƙarin bayani kan halin da suke ciki.

    Ga tattaunawar da muka yi da ita a sama

  4. Ba mu tsoron Rasha, in ji Shugaban Ukraine

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ba da jimawa ba Shugaban Ukraine Volodymyr Zelesnky ya yi jawabi ga ƙasarsa. Ga bitar wasu daga cikin abubuwan da ya fada.

    • Zelensky ya bayyana cewa aƙalla mutanen ƙasarsa 137 aka kashe a yaƙin nan zuwa yanzu, ciki har da farar hula. Haka kuma akwai mutum 316 da aka raunata.
    • Shugaban Ukraine din na ganin shi ne mutum na farko da Rasha ke hari. Ya ce ba shi da niyyar barin gidan gwamnatin da yake zaune a birnin Kyiv.
    • Ya kuma tabbatar da rahotannin da ke cewa Rasha ta harba makamai masu linzami masu yawa a cikin Ukraine da misalin ƙarfe huɗu na asuba agogon ƙasar.
    • Ya kuma ƙara kira ga ƙasashen yamma da su ƙara ƙoƙari kan saka takunkumai ga Rasha inda ya buƙaci su yi abin da ya fi saka takunkumin tattalin arziki ga Rasha.
    • A wani gargaɗi da ya yi ga Moscow, Zelensky ya bayyana cewa Ukraine ba za ta daina kare kanta ba har sai Rasha ta daina abin da take yi.
  5. Rasha ta shafe dare tana kai hare-hare ta sama a Ukraine

    ..

    Daren da Rasha ta shafe tana kai hare-hare ta sama ya sa Rashar ta yi illa ga yankin Pozniake da ke Kyiv babban birnin ƙasar.

    Manyan gine-gine da ke yankin sun kama da wuta inda tagogi suka yi ta fashewa.

    Masu aikin kashe gobara sun ta ƙoƙari cikin hayaƙi da ɓaraguzai domin kashe gobarar da ta tashi a daidai lokacin da ake samun fashewar abubuwa a cikin birnin.

    Aƙalla mutum takwas aka raunata a Pozniake. Ɗaya daga cikin mazaunin birnin ya bayyana cewa, "Putin, muna so mu ga an yanka ka kamar dabba."

    A wasu wuraren, sararin samaniya a cikin dare ya turnuƙe da hayaƙi sakamakon tashe-tashen bama-bamai.

  6. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Jama'a barkanmu da safiyar Alhamis, 25 ga watan Fabrairun 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.