Davido ya ce abokansa sun tara masa sama da naira miliyan 100 a rana ɗaya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo

  1. Za a rufe makarantu a Indiya saboda gurɓacewar iska

    Delhi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar da ke tabbatar da kyau da ingancin iskar da ake shaƙa ta kasar Indiya, ta bayar da umarni ga kananan hukumomin birnin Delhi da makwabtan jihohi umarnin rufe makarantu saboda gurɓacewar iskar birnin.

    Ba ya ga rufe makarantu har sai baba ta gani, hukumar ta kuma bayar da umarnin dakatar da duk wasu ayyuka na gine-gine da ba su zama na dole ba da kuma rufe tashoshin samar da makamashi a Delhi da makwabtan garuruwa har zuwa ranar Lahadi.

    Haka kuma hukumar ta bukaci ofisoshin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba da su karfafa wa ma’aikatansu gwiwa kan su dinga aiki daga gida.

    Sai dai wannan mataki na rufe wurare tare da takaita yawan jama’a a waje bai yi wa wasu talakawa dadi ba, wadanda suka samu kansu a yanayi na gaba kura baya sayki.

    "Ba shakka akwai matsala," a cear wani makanike. "Rashin numfashi da kaikayin ido ne suka fi illa. Ta yaya za mu iya tsira daga wannan? Dole ne mu zauna a gida domin guje wa gurbatar iskar. "Amma idan muka kuma zauna a gida ta yaya za mu rayu?’’

  2. An umarci Amurkawa su gaggauta ficewa daga Ethiophia

    Ethiophia

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar Harkokokin Waje na Amurka ta gargaɗi Amurkawa mazauna Ethiopia cewa zai yi wuya a iya kwashe su idan matsalar tsaron kasar ta sake rincaɓewa.

    Wakiliyar BBC ta ce wani babban jami'in ma'aikatar ya umarci 'yan kasar su gaggauta ficewa daga Ethiopia, yana mai jaddada cewa gwamnatin ba ta da wani keɓaɓɓen shiri na kwashe 'yan kasar kamar yadda aka gani a Afghanistan.

    Amurka da ƙungiyar hadin-kan Afirka (AU) na ci gaba da matsa wa gwamnatin Ethiopia lamba da 'yan tawayen Tigray domin kawo karshen yaƙin da suke gwabzawa.

    Dubban mutane sun mutu sannan sama da miliyan biyu sun rasa muhallinsu a shekara ɗaya da aka kwashe ana tafka rikici.

  3. Korona ta kashe ƙarin mutum biyar a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum biyar da cutar korona ta yi ajali ranar Talata.

    Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce wasu mutum 144 sun kamu da cutar a jiha 13, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

    Jihohin su ne:

    • Imo (38)
    • Plateau (20)
    • Lagos (17)
    • Abuja (16)
    • Kwara (15)
    • Zamfara (15)
    • Ondo (7)
    • Rivers (5)
    • Taraba (4)
    • Oyo (3)
    • Bauchi (2)
    • Edo (1)
    • Ekiti (1)

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 213,321 ne suka harbu da cutar, sannan ta kashe mutum 2,973. Sai dai an sallami 206,206 daga asibitoci bayan sun warke.

  4. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin samun rahotanni kan abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.