Rufewa
To masu sauraro da haka muka kawo karshen shafin namu na kai tsaye na yau.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Sai da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo
To masu sauraro da haka muka kawo karshen shafin namu na kai tsaye na yau.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Sai da safe.

Asalin hoton, reu
Tarayyar Turai ta aminta da saka fara a jerin abinci mai inganci da take so a rika nomawa.
Wannan ne karon farko da EU ta aminta kwaro ya zama abinci da bai da hadari ga lafiyar dan adam, tun bayan da ta aminta da cin tsutsar mealworm a watan Yuni.
Tarayyar Turai ta kara da cewa za a rika kasuwancin farar a matsayin abincin marmari, da kuma sarrafata ta hanyoyin da ake bukata.
Hukumar kula da ingancin abinci ta Turai (EFSA) itama ta ce za a iya cin fara matsayin abinci matsawar ta gawurta, lura da cewa tana gina jiki.
EU ta aminta da cin fara ne a karkashin dokar abinci da ta samar a 1997, da ta ba da damar cin wasu nau'ukan tsirrai da kwari a matsayin abincin da za a iya shigowa dashi daga wasu kasashe.
Kuma yanzu haka an mika bukatar amincewa da wasu nau'in kwari tara, don samun amincewar hukumar EFSA a rika kalaci da su.

Asalin hoton, Reuters
Likitoci a Sudan sun ce mutum 10 ne suka mutu bayan da jami'an tsaro suka harbe su, yayin da dubban mutane suke zanga-zanga don nuna ƙin jinin karɓar mulki da sojoji suka yi.
An toshe layukan waya da na intanet inda hakan ya janyo fargabar yunƙurin gwamnati na son yin rufa-rufa kan rikicin.
Masu fafutuka sun yi kira da a fito zanga-zangar don tunawa da ranar da ya kamata farar hula ya karɓi ragamar shugabanci.
Mutumin da ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya rusa gwamnati ya kama ƴan siyasa, daga baya kuma ya naɗa kansa shugaban sabuwar Majalisar Ƙoli.
An dade ana gudanar da bore daga bangaren masu goyon bayan mulkin soji da kuma wadanda ke adawa dashi.

Asalin hoton, @abdullahi.haruna
Rundunar ƴan sandan Kano ta shirya wa jami'anta gasar karatun Al-Kur'ani mai tsarki a jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya shaidawa BBC cewa an soma gasar ne a yau Laraba.

Asalin hoton, @abdullahi.haruna
Ya ce gasar ta iya ƴan sanda ce zalla kuma an buɗe gasar ne da masu Hizib biyu da biyar da 10 zuwa 20
Zuwa ranar Alhamis masu Hizib 40 da 60 za su fafata. Kuma akwai kyaututtuka dama da aka yi tanadi da za a ba waɗanda suka ya lashe gasar.

Asalin hoton, @abdullahi.haruna

Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da aka samu daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021 zai jefa karin mutum miliyan shida cikin talauci a kasar.
World Bank ya fadi haka ne a rahotonsa kan tasirin cutar korona a Najeriya.
Wani bangare na rahoton ya fadi cewa " hauhawar farashin kayayyaki da aka fuskanta a Najeriya daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021 zai mutum miliyan shida cikin kangin talauci. A don haka akwai bukatar bullo da shirye-shirye masu tasiri cikin takaitaccen lokaci."
Rahoton ya kara da cewa " adadin yan Najeriya da ke zaune cikin talauci zai karu daga kashi 40.1 zuwa kashi 42.8 cikin 100 saboda hauhawar farashin."
Wani abu da rahoton ya kuma bankado shine cewa talakawa a Najeriya sun fi masu arziki rungumar rigakafin cutar korona, wanda hakan ke nufin masu karamin karfin sun fi tsorata da annobar akan masu hannu da shuni.
Fitaccen mawakin Najeriya Davido Adeleke ya ce ya tara sama da naira miliyan 100 a rana ɗaya da abokan arzikinsa suka tura masa.
Mawakin ya nemi abokansa ne kowannensu ya aika masa naira miliyan ɗaya kafin zagayowar ranar haihuwarsa.
A sakon bidiyo da ya wallafa mawakin ya ce yana son abokansa da ke ji da shi kowannensu ya masa naira miliyan 100, kuma cikin rana ɗaya Davido ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya tara sama da naira miliyan 114.

Asalin hoton, @Davido
Mawakin ya ta wallafa bayanan kuɗaden da aka tura masa a Twitter har zuwa lokacin da yawan kuɗin ya kai naira miliyan 114.
Daga cikin abokan mawakin da ya ce sun tura masa kuɗin sun hada da E-money da Obi Cubana da Tiwa Savage Femi Otedola da Naira Marley da sauransu.

Asalin hoton, re
Rundunar tsaron da ke kan iyaka a Poland ta ce baƙin haure kusan dubu biyu ne suke girke a iyakar ƙasar da Belarus, yayin da Tarayyar Turai ke ƙarfafa ƙoƙarinta na shawo kan rikicin.
Hukumar tsaron ta ce bakin hauren sun taru ne a kusa da shingen duba masu wucewa a Bruzgi-Kuznica a ɓangaren Belarus da ke kan iyaka.
Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta ce Tarayyar za ta aika da kayan abinci da barguna da sauran kayan agaji da kuɗinsu ya kai dala dubu tamanin ga baƙin hauren da ke kan iyakar.
A baya, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna da Shugaba Lukashenko na Belarus, sannan ta jaddada buƙatar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga harkokin agaji.

Asalin hoton, Reuters
Amurka ta cire Najeriya daga jerin kasashen da ke hana 'yancin gudanar da addini.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya bada sanarwar a yau Laraba.
Mr Blinken na kalamin ne gabanin kawo ziyara Abuja babban birnin Najeriyar.
To amma Blinken ya ce sun saka Rasha da China da wasu kasashe takwas jerin kasashen da ake tauye wa al'umma hakkin da suke da shi na 'yancin gudanar da addini.
" Amurka za ta cigaba da jajircewa wurin tabbatar da cewa gwamnatoci a kasashen duniya sun daina muzguna wa al'ummarsu, kan abinda ya shafi 'yancin addini." Inji shi.
A watan Disamban shekarar 2020 ne Amurka ta saka Najeriya a jerin kasashen da ke tauye wa al'umma 'yancin gudanar da addini.
A daya bangaren Antony Blinken ya ambato kungiyoyin masu tada kayar baya na Boko Haram da al-Shabaab da Houthi da IS a matsayin kungiyoyin da suka yi kaurin suna wurin keta dokar 'yancin gudanar da addini ta 'International Religious Freedom Act'.

Asalin hoton, LASEMA
Ƙungiyar Injiniyoyi a Najeriya ta ce ginin da ya rushe a Legas, wanda ya kashe mutum arba'in da biyar a farkon wata ya kere tsawon da asali aka tsara zai yi.
Ƙungiyar injiniyoyin ta ce binciken su ya gano cewa fiye da kamfanoni biyu ne ke aiki kan ginin a lokaci guda.
Itama gwamnatin Najeriya na gudanar da nata binciken kan ginin mai hawa ashirin da ɗaya, da ya rushe a farkon wannan watan a unguwar Ikoyi ta jihar Legas.
Tun a lokacin ne gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da dakatar da shugaban hukumar da ke kula da gine-gine a jihar Gbolahan Oki.
Shine matakin farko a wani bangare na binciken da hukumomin za su gudanar don gano musabbabin rugujewar ginin.

Asalin hoton, Reuters
Rundunonin tsaro a Khartoum babban birnin Sudan sun watsa hayaƙi mai sa hawaye, don tarwatsa masu zanga-zanga kan karɓar mulki da sojoji suka yi a baya-bayan nan.
Tuni dama an toshe layukan waya da intanet a wani yunkuri na hana mutane taruwa.
BBC ta fahimci cewa jami'an tsaron Sudan na yin dukkan mai yiwuwa don ganin zanga-zangar ba ta kankama ba.
Masu fafutuka sun yi kira ga mutane a faɗin kasar su bazu kan tituna, don tunawa da ranar da ya kamata farar hula su karɓi ragamar shugabancin Majalisar Ƙolin ƙasar mai mulki.
A makon da ya gabata ne shugaban sojojin Abdel Fattah al-Burhan, wanda ya jagoranci juyin mulkin ya naɗa kansa shugaban Majalisar ƙolin, kuma da dama daga ciki da wajen Sudan na adawa da matakin.
A wata mai kama da haka Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi kira da a ci gaba da shirye-shiryen mika mulki ga farar hula a Sudan din.
Ya ce mutanen Sudan sun nuna ƙarara cewa suna goyon bayan gwamnatin demokuraɗiyya.
Mr Blinken ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabinsa a ziyarar da yake yi a Kenya, irinta ta farko da ya kai nahiyar Afrika tun bayan hawansa mulki.

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar Islamic State (IS) ta ce ita ce ta kai harin bam a Kampala, babban birnin Uganda ranar Talata.
IS ta yi amfani da kafar sada zumunta ta Telegram ta sanar da cewa ta kashe sama da mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a harin na kunar bakin wake.
To amma a cewar hukumomi mutum shida ne suka mutu da suka hada da mahara uku.
Hakama yan sanda sun ce sun kama mutum na hudu da suke zargi da kitsa harin.
Sanarwar IS din ta kara da cewa dalilin ta na kai hari Kampala na da nasaba da rawar da Uganda ke takawa wurin yakar kungiyar a Tsakiyar Afrika.
Wannan ne karon na uku da IS ta dauki alhakin kai hare-hare a Uganda kama daga watan Uganda.

Asalin hoton, Getty Images
Farashin makamashi da tsadar sufuri da sauran kayan masarufi ya karu da kashi biyu cikin 100, kamar yadda aka yi hasashe a baya a Burtaniya.
Hukumar Ƙididdiga ta Burtaniyar ta ce hauhawar farashin ta kai kashi 4.2 a watan Oktoba, kuma shi ne mafi girma a cikin shekara 10.
An samu hauhawar ce tun bayan buɗe kasuwanni daga kullen annobar korona da aka saka.
Ana ci gaba da samun hauhwara farashin kayayyaki a faɗin duniya sakamakon girman buƙatar da ake da ita da kuma ƙarancin kayan, wanda kuma hakan ya sa wasu sun fara shiga kuncin rayuwa.

Asalin hoton, Channels TV
'Yan sanda a Legas sun sce sun kama mutum 12 waɗanda ake zargi da hannu kan kisan wani jami'in rundunar mai suna Kazeem Abonde.
Abonde, wanda lauya ne kuma mai muƙamin sufiritanda, an kashe shi ne bayan wata shida da yin ritaya a watan Satumba yayin wani samame da aka kai kan mafakar waɗanda ake zargi da aikata laifuka a rukunin gidaje na Ajao.
Cikin wata sanarwa a ranar Talata, kakakin 'yan sandan Legas Adekunle Ajisebutu ya ce za a gurfanar da waɗanda aka kama ɗin a gaban kotu ranar Laraba.
A wani labari da ya fito ranar Laraba daga bakin mai magana da yawun yan sandan jahar Adekunle Ajisebutu, na cewa, wadanda aka kama bayan bincike da akayi za'a gurfanar dasu gaban shari'a ranar Laraba.
Daga cikin wadanda aka kama har da wani mai suna Isma'il Abdullahi Haruna mai shekara 23.
An kama sauran mutum 11 ɗin ne bayan mako huɗu ana bincike, a cewar Mista Ajisebutu.

Manyan mutane daga sassan Najeriya sun taru a birnin Kano domin halartar jana'izar ɗan uwan Aliko Dangote, mutum mafi arziki a nahiyar Afirka.
Kafin rasuwarsa, Sani ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote.
Sani Dangote ya rasu ne ranar Lahadi bayan gajeriyar jinya yana da shekara 61.



Asalin hoton, AFP
Masu zanga-zanga na ci gaba da tururuwa a kan titunan birnin Khartoum na Sudan, yayin da masu fafutika ke kiran mutane su ci gaba da nuna fushinsu ga gwamnatin sojan ƙasar.
Duk da barazanar da suke fuskanta daga sojoji, masu zanga-zangar sun ci gaba da fafutika biyo bayan rufe layukan salula da na intanet.
Da a ce ba su yi juyin mulki ba a makon da ya gabata, yau Laraba ce ya kamata ta zama rana mai ɗumbin tarihi ga al'ummar Sudan, inda gwamnatin soja za ta miƙa mulki ga Majalisar Mulki ta farar hula.
A madadin haka, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kankane mulkin ƙasar kuma da alama zai ci gaba da daƙile mutanen ƙasar wajen zaɓar jagororinsu da kansu.
Guardbel Zirkusu, ɗan uwa ga marigayi Birgediya Janar Dzarma Zirkusu, ya shaida wa BBC Hausa cewa ɗan uwansa ya samu kyakkyawar makoma saboda kirkinsa.
A ranar Asabar da ta gabata ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP da ke iƙirarin jihadi a yammacin Afrika sun halaka Birgediya Janar Zirkusu da wasu sojoji uku a lokacin da suka je kai wa dakaru ɗauki a fafatwar da suke yi da mayaƙan.
Rundunar sojin ta ce an kashe shi ne a ƙaramar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

A Najeriya, yayin da matsalar hare-haren ‘yan fashin daji ke ci gaba da addabar mutane a wasu jihohin arewacin ƙasar, wasu matasa sun ce zai fi kyau a koma kan teburin tattaunawa da 'yan bindigar.
A jiya Talata ma sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin Allah-wadai da aika-aikar 'yan fashin dajin ta kashe mutum 15 a baya-bayan nan cikin jihar Sokoto, inda ya ce hari ne na rashin hankali a kan mutanen da ba su ji, ba su gani ba, kuma lallai sai an yi hukunci a kai.
Sai dai, wasu matasa 'yan asalin Sokoto da Zamfara da Kebbi mazauna Abuja babban birnin ƙasar, sun ce a shirye suke su shiga gaba don tattaunawa da 'yan fashin dajin.
Sun bayyana hakan ne yayin wani taro da suka yi a Abujar ranar Talata.
Ku latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Ahmed Wakili:
Muna kawo yadda ake gudanar da jana'izar Alhaji Sani Dangote a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Sani Dangote wanda shi ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu ne ranar Lahadi bayan gajeriyar jinya.
Ya rasu yana da shekara 61 kuma ya bar mahaifiyarsa da mata ɗaya da kuma yara takwas.

Asalin hoton, State House
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi Allah-wadai da kisan mutum 15 da 'yan bindiga suka yi a ƙananan hukumomin Goronyo da Illela na Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.
A cewar wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ya fitar, Buhari ya ce sojoji na kai makamai na zamani domin kakkaɓe 'yan fashin dajin da ke kai hare-haren.
"Dole ne gwamnati ta zage damtse wajen kawo ƙarshen irin wannan tashin hankalin na babu gaira babu dalili," in ji shugaban.
"Bari na sake tabbatar wa 'yan Najeriya cewa wannan gwamnatin ba za ta yi watsi da su ba a irin wannan lokaci na tashin hankali da 'yan fashi ke aikatawa."
Ya ƙara da cewa: "Muna ci gaba da karɓar makamai domin ƙara ƙarfin sojojinmu...suna ci gaba da kai makamai na zamani domin tattara bayanan sirri da zummar kawo ƙarshen miyagu da kuma maƙiyan zaman lafiya."
Shugaba Buahri ya sha ayyana rashin jin daɗi da ɓacin ransa game da kashe-kashen da kuma ɗaukar alwashin cewa shi ne na ƙarshe. Sai dai hare-haren na ci gaba da faruwa duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke cewa suna yi.