Korona ta kama ƙarin mutum 51 a Abuja
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 138 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Asabar.
Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a Abuja suke inda aka samu mutum 51 da suka kamu, sai jihar Anambra da aka samu mutum 28, da kuma Legas mai mutum 24..
Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Asabar:
- Abuja -51
- Anambra-28
- Lagos-24
- Benue-18
- Plateau-9
- Kaduna-7
- Jigawa-1
A jumullance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 206,064 sai dai 193,893 sun warke.
Akwai kuma mutum 2,723 da suka mutu
