Ba ni ba ne a bidiyo ɗauke da bindiga- Ministan tsaron Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Fauziyya Tukur

  1. Bankwana

    A nan za mu yi bankwana da ku.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe don ci gaba da samun labarai na Najeriya da na sauran ƙasashen duniya.

  2. Ba ni ba ne a bidiyo ɗauke da bindiga- Ministan tsaron Najeriya

    Magashi

    Asalin hoton, Nigeria Defense Headquarters

    Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan kafofin sada zumunta Mohammad Abdulkadri ya fitar ta ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yada hoton da sunan Janar Magashi.

    Ta kuma ce bincike ya gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon shugaban kwalejin rundunar sojin Najeriya na kimiyya da fasaha da ke Makurɗi wato Nigerian Army College of Environmental Science and Technology (NACEST) Makurdi, wanda muƙaminsa ya ba shi damar riƙe makamai idan zai yi tafiya.

    Sanarwar ta zayyano wasu abubuwa kamar kalar motar da mutumin ya shiga da takardar ke liƙe a jikin motar da ya dace a ce masu yaɗa bidiyon sun duba kafin su ayyana cewa ministan tsaron ne.

    Ta ce ministan na amfani da motar jeep ce ƙirar Land Crusier kuma baƙa kamar sauran takwarorinsa ministoci.

    Haka kuma, sanarwar ta ce ministan tsaron ba ya buƙatar ya ɗauki bindiga saboda kamar yadda aka gani a bidiyon saboda irin tsattsauran tsaron da ke tattare da muƙaminsa.

    Ministan ya sanar da cewa al'ummar Najeriya su san cewa ana yin dukkan mai yiwuwa don ganin an daƙile ƴan bindiga da masu ta da ƙayar baya a ƙasar.

  3. Dubban ƴan Tunisia sun goyi bayan matakin shugaban ƙasar na dakatar da majalisa

    Dubban ƴan Tunusia masu goyon bayan Shugaba Kais Saied sun yi tattaki don nuna goyon bayansu ga matakinsa na dakatar da majalisar dokokin ƙasar inda suka ce sun yabi ƙoƙarinsa na kawo sauyi a siyasar ƙasar.

    Tunusia

    Asalin hoton, EPA

    Tunisia

    Asalin hoton, Getty Images

    Tunisia

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Hukumar NDLEA ta kama wani sojan bogi da miyagun ƙwayoyi a Abuja

    Jami'an hukumar NDLEA da ke hana sha da fataucin miyagun wayoyi a Najeriya sun kama wani soja na bogi mai suna Hayatu Galadima da abokin huldarsa Hamisu Adamu yayin da suke safarar kwayoyi da makamai da na'urorin sadarwa ga ƴan bindiga da ke jihar Kaduna.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama mutanen biyu ne a hanyar Gwagwalada a Abuja ranar Juma'a 30 ga Satumban shekarar 2021.

    Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya bayyana cewa cikin abubuwan da aka kama su da shi akwai harsasai da aka ɓoye a cikin robar ruwa da wayar sadarwa guda 16 da takardar shaidar aiki da rundunar sojin Najeriya da katunan ATM guda 7.

    Sannan an kama su da tabar wiwi da ƙwayoyin tramadol da layukan MTN da 9mobile da airtel da waya

    Shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa ya ba da umarnin a miƙa mutanen da ake zargin ga rundunar sojin Najeriya da wata hukumar leƙen asiri wadda dama ta sa mutanen biyu cikin jerin mutanen da take bincike a kansu.

    Buba Marwa

    Asalin hoton, Others

  5. An kwashe ɗaruruwan mutane daga tsibirin Guanja na Honduras saboda wutar da ke cin gidaje

    Wata wuta da ta tashi a tsibirin Guanaja a Honduras ta lafa bayan da hukumomi suka kashe ta, bayan da ta lalata gwamman gidaje tare da tursasa wa ɗaruruwan mutane barin gidajensu.

    A ƙalla mutum uku ne suka samu raunuka a gobarar wadda ta fara ci da safiyar Asabar a cewar hukumomi.

    Ba a san abin da ya haifar da gobarar ba.

    Guanaja, tsibirin da ke da girman kilomita 19 na ɗaya daga cikin tsibirai uku na Honduras wadda mafi yawan kuɗn shigarta na fitowa ne daga yawon buɗe ido.

  6. Bashar al-Assad da Sarkin Jordan sun yi magana a karon farko cikin shekaru 10

    Bashar al-Assad

    Shugaban Syria Bashar al-Assad da Sarkin Jordan Abdullah II sun yi magana ta waya bayan shekara 10.

    Shugaban na Syria da shugaban na Jordan sun tattauna kan dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Wannan ce tattaunawa ta farko cikin tsakanin bangarorin biyu tun shekarar 2011 da kuma fara yaƙin basasar Syria.

    A yayin tattaunawar tasu, Sarki Abdullah II ya jaddada goyon bayan da Jordan ta ke bayar wa don tabbatar da ƴancin Syria da zaman lafiyarta.

    Jordan ta sake buɗe iyakarta ta Jaber-Nasib wanda ke kusa da Syria a makon da ya gabata don ƙarfafa alaƙarta da Syria.

  7. Asirin wasu attajirai da manyan ƴan siyasa na duniya ya tonu

    Shugabannin duniya

    Asirin wasu shugabanni da attajirai da manyan 'yan siyasa na duniya ya tonu a daya daga cikin manyan bankadar sirri da aka taba samu na bayanan arzikinsu.

    An gano bayanan arzikin wasu shugabannin kasashen duniya 36 da jami'an gwamnatoci fiye da 300 daga kamfanonin mai da aka sa a takardun Pandora.

    Bayanan sun gano cewa Sarkin Jordan ya boye dukiya mai dumbin yawa da kadarori har na fan miliyan 70 a Birtaniya da Amurka.

    Takardun sun kuma nuna yadda tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair da matarsa suka adana fan 312,000 a lokacin da suka sayi ofishinsu na Landan.

    Bankadar ita ce ta baya-bayan nan a cikin shekara bakwai da aka samu, bayan na FinCen Files da Paradise Papers da Panama Papers da kuma LuxLeaks.

  8. Mutum takwas sun mutu a haɗarin jirgin sama a Milan

    Plane Crash

    Asalin hoton, EPA

    Wani ƙaramin jirgi ya faɗa cikin wani gini a birnin Milan inda ya kashe duka mutane takwas ɗn da ke cikin jirgin.

    Jirgin ya tashi ne daga filin jirgin sama na Milan Linate kuma ya nufi tsibirin Sardinia, amma ya faɗi ɗan lokaci kaɗan bayan da ya tashi a waje-wajen birnin.

    Shaidu sun ce sun jiyo wata ƙara a lokacin da jirgin ya faɗa ginin mai hawa biyu sannan ya kama da wuta.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu yaro ne ƙarami a cewar kafofin yaɗa labarai na ƙasar.

    Wani baƙin hayaƙi na tashi daga cikin ginin.

  9. Za a mayar da hankali kan sunnonin Annabi Muhammad a huɗumar Juma'a a Pakistan

    Mai bai wa Firai Ministan Pakistan shawara kan harkokin addini, Hafiz Tahir Mehmood Ashrafi ya ce a watannin Rabiul Awwal da Rabiul Saani, huɗuba a masallatan Juma'a za su mayar da hankali ne kan sunnonin Annabi Muhammad.

    A lokacin wani taron manema labarai, ya ce an ɗamince da matakin ne a Majalisar Shura ta Pakistan da ke Punjab.

    Ya ce za a riƙa gabatar da huɗuba kan batutuwa daban-daban kamar ilimin mata da haƙƙoƙinsuda hijabi da kawar da ta'adanci da amfanin ilimi da sauransu.

    Ya ce yana da matuƙar muhimmanci a ilimantar da mutane kan yadda zamantakewa ta ke a Madina da kuma yadda shugabancin manyan Khalifan musulunci ya ke. Ya ce ana buƙatar haɗin kai don ganin an mayar da Pakistan kamar birnin Madina.

    Ya kuma ce zai buƙaci ministan ilimin Punjab ya shirya muhawar da gasanni kan batutuwan addini a duka makarantun a faɗin ƙasar.

  10. Ambaliya ta raba mutum 500,000 da gidajensu a Sudan ta Kudu

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin mutum 500,000 ambaliya ta shafa a kasar Sudan ta Kudu

    Ta ce kusan al'ummar ƙasar na rayuwa ne cikin ruwa, inda ruwan sama da aka tabka ya sa rafi ya tumbatse

    Shugaba Salva Kiir ya ce ambaliyar ta shafi gidansa, yana mai cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a hada kai domin magance matsalar.

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, UN

  11. Algeria ta haramta wa jiragen Faransa ratsawa ƙasarta

    Gwamnatin Faransa ta ce Algeria ta haramta wa jiragen yaƙinta ratsowa sararin samaniyarta.

    Faransa ta sanar da haka ne a ranar Lahadi, bayan Algeria ta sanar da janye jekadanta domin nuna fushi da matakin shugaba Macron kan batun biza.

    Faransa na ratsawa ta Algeria ne domin shiga yankin Sahel inda dakarunta na Barkhane ke yaƙi.

    Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara tsami ne bayan da Faransa ta rage yawan biza da take ba ƴan Algeria da Morocco da Tunisia, tana mai zarginsu da rashin ɗaukar matakan da suka dace kan masu tsallakawa Faransa.

    Faransa
  12. PSG ta sha kashi

    Rennes ta ɗura ƙwallaye biyu a ragar PSG a fafatawar da suka yi Ligue 1.

    Karon farko kenan da aka doke PSG a gasar a kakar bana.

    An doke PSG ne duk da ta fara wasan da zaratan ƴan wasanta Messi da Neymar da Mbappe.

    Ana minti 44 dab da zuwa hutun rabin lokaci, Rennes ta fara zura ƙwallo a ragar PSG daga bisani kuma ta ƙara ƙwallo ta biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci

    PSG har yanzu ita ke saman teburin Ligue 1 da maki 24, tazarar maki shida tsakaninta da Lens, yayin da Rennes ta hauro matsayi na bakwai

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Afghanistan: An kai harin bom a masallaci a Kabul

    Mutane da dama sun mutu a wani harin bom da aka kai a masallaci a Kabul babban birnin Afghanistan.

    Kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid ya tabbatar da harin a Twitter inda ya ce bom ɗin ya tashi a ƙofar shiga Masallacin Idqa.

    Rahotanni sun ce an kai harin ne lokacin da ake gudanar da addu'o'i a masallacin ga mahaifiyar Zabihullah Mujahid wacce ta rasu a makon da ya gabata

  14. Taliban ta haramta sayar da makamai a Afghanistan

    Gwamnatin Taliban ta haramta sayar da makamai da motoci a Afghanistan.

    Kakakin gwamnatin ta Taliban Zabihullah Mujahid cikin wata sanarwa ya ce wasu sun ƙwace makamai da motocin gwamnati bayan da Taliban ta ƙwace ikon birnin Kabul, kuma yanzu suna ƙoƙarin sayar da su.

    Sanarwar ta ce an haramta sayar da makamai da motocin da ba tantance ba har sai yadda hali ya yi.

    An ba kwamandojin tsaro na yankuna su ɗauki mataki domin tabbatar da bin dokar.

    Taliban
  15. Bincike ya bankaɗo dubban masu lalata da yara a cocin Katolika a Faransa

    Shugaban wani kwamiti mai zaman kansa da ke binciken cin zarafi ta hanyar lalata a cikin cocin Katolika a Faransa ya ce akwai dubban masu lalata da yara a cocin a shekaru saba'in da suka gabata.

    Jean- Marc Sauvé ya faɗawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa hukumar ta bankaɗo malaman cocin da ke cin zarafin yara kusan 3,000, yana mai cewa wannan shi ne ƙiyasi mafi ƙaranci.

    A ranar Talata ne za a fitar da rahoton karshe na hukumar.

    Cocin Katolika ta Faransa ce ta kafa kwamitin binciken a 2018 kan badaƙalar da ake zargin ta dabaibaye cocin.

    An gudanar da binciken ne ta hanyar bayanan cocin da na kotu da ƴan sanda da kuma tattaunawa da waɗanda abin ya shafa da kuma shaidu.

    Cocin katolika a Paris

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Mata sun faɗi zaɓen ƴan majalisar Shura a Qatar

    Zaben Qatar

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakamakon karshe na zaben ƴan majalisar Shura, mai ba da shawara a Qatar ya nuna cewa babu wata mace da ta yi nasara a lashe kujera a majalisar.

    Fiye da kashi goma na ƴan takarar da suka fafata a kujeru talatin da ake da su mata ne.

    Masu sharhi sun ce mai yiyuwa ne sarkin Qatar Tamim Bin Hamad Al Thani, zai yi amfani da haƙƙinsa don nada wasu mata a kujeru goma sha biyar da suka rage.

    Jami'an zabe sun ce kusan kashi biyu bisa uku na waɗanda suka cancanci kaɗa kuri'a sun yi zaɓe. Ko da yake kashi 90 na ƴan ƙasar baƙi ne ma’aikata daga ƙasashen waje.

    Wasu na ganin zaɓen a matsayin wani yunƙuri da mahukuntan ƙasar ke yi na samar da kyakkyawan yanayi ta fuskar dimokuraɗiyya a Qatar mai arzikin mai a idon duniya.

  17. Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da harsasai 340 da ya ɓoye cikin buhun garin rogo a Delta

    Kwamishian ƴan sandan Delta Ari Mohammed Ali

    Asalin hoton, Other

    Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta cafke wani da ake zargi ɗan fashi ne ɗauke da harsasai 340 da ya ɓoye cikin buhun garin rogo.

    Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Bright Edafe ne ya bayyana hakan a birnin Asaba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Ƴan sandan sun ce sun kama mutumin ne da aka goyo kan keke ɗauke da buhun garin rogo a wani shingen bincikensu kan titin Bomadi/Toamo a ranar Juma’a.

    Bayan sun tare shi ne ƴan sandan da ke baki aiki suka yanke shawarar binciken bugun garin da yake ɗauke da shi.

    “Lokacin binciken aka samu harsasan bindiga na AK47 guda 340 da aka ɓoye a cikin buhun."

    Yan sandan sun ce suna tsare da shi kuma suna ci gaba da gudanar da bincike.

  18. Ƴan sandan Zamfara sun kama gawurtattun ƴan fashi 21

    Ƴan fashin daji

    Asalin hoton, Zamfara Police

    Rundunar ta ƴan sandan Jihar Zamfara ta ce ta kama gawurtattun ƴan bindiga 21 a wurare daban-daban na jihar sannan sun kashe wasu guda biyar. bayan sabbin matakan tsaroda gwamnati ta ɗauka.

    Daga cikin waɗanda aka kama akwai ɗaya daga cikin kwamandan ƴan bindiga Bello Rugga da aka fi sani da sunan Turji wanda ya addabi mutane a dajin ƙaramar hukumar Gummi.

    Ƴan sandan sun ce sun kama makamai a hannunsa da suka hada da bindiga ƙirar AK47.

    Haka kuma, ƴan sandan sun ce sun daƙile hare-hare huɗu tare da kuɓutar mutane sama da 200 da ke hannun ƴan bindiga a wurare da dama kuma tuni suka koma wurin danginsu.

    Rundunar ƴan sandan ta jihar Zamfara ta ce dalilin sabbin matakan tsaron, sauran manyan laifuka da ake aikatawa a jihar kamar fashi da makami da ƙwace mota da sata da dai sauransu sun ragu sosai.

  19. Algeria ta ce Faransa na shisshigi ga harakokinta

    Algeria ta dawo da jakadanta daga birnin Paris, inda ta zargi Faransa da yin katsalandan a harkokinta.

    Algeria ta ce tana mayar da martani ne kan kalaman da watajaridar Faransa ta ambato Shugaba Emmanuel Macron na yi.

    Jaridar ta rawaito shugaban yana cewa tsohon tsarin mulkin mallaka na Faransa, cike yake da siyasar soji da aka rika yi cikin rashin gaskiya.

    Takaddamar diflomasiyyar na zuwa ne kwanaki bayan Faransa ta rage yawan bizar da ta ke ba ƴan Algeria da sauran kasashen Arewacin Afirka.

  20. Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzami

    Koriya ta Arewa ta ce ta harba wani sabon nau'in makami mai linzami a gabar tekun gabashinta.

    Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce masana kimiyyar tsaro sun duba lafiya da mugun gudun sabon makamin mai suna Hwasong Eight.

    Sojojin Koriya ta Kudu sun tabbatar da cewa an yi sabon gwajin makami mai linzami a Koriya ta Arewa.

    =A baya bayan nan dai Pyongyang ta matsa kaimi wajen yin gwajin makamai masu linzami yayin da zaman dar-dar ke ci gaba da karuwa a yankin.

    Makamin Koriya ta Arewa

    Asalin hoton, Reuters