Hoton bishiyar tsarin gidan sarautar Birtaniya
Wannan bishiya ce da ke nuna yadda tsarin Masarautar Birtaniya yake.

A wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: "Cikin tsananin jimami Mai martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da mutuwar mijinta abin ƙaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburgh.
Buhari Muhammad Fagge, Halima Umar Saleh, Badariyya Tijjani Kalarawi and Umaymah Sani Abdulmumin
Wannan bishiya ce da ke nuna yadda tsarin Masarautar Birtaniya yake.

An sassauta tutar Birtaniya daga Fadar Buckingham sannan an lilliƙa takardun sanarwar mutuwar a ta ko ina a fadar.
Mutane sun yi ta ajiye furanni na nuna alamar jimami a wajen fadar, yayin da ake ci gaba da tururuwar taruwa a Fadar Windsor.
Wakilin BBC a fadar Nicholas Witchell ya ce "lokaci ne da ƙasar ta shiga cikin baƙin cikin wani babban rashi da ta yi" musamman duba da cewa sarauniya ta yi rashin mijinta da suka shekara 73 da aure - wani tsawon lokaci da ma'auratan suka yi tare da ba kasafau ake samu ba."
Ya kuma ce: "Yarima Philip ya taimaka wa sarauniya ƙwarai da gaske ta hanyar ganin ta samu nasara a mulkinta," yana mai bayyana yariman a matsayin wanda ya san muhimmancin rawar da sarauniya ke takawa - da kuma rawar da shi ma ya kamata ya taka."
Gabanin rasuwar Duke dai ya koma gidan sarautar na Winsor Castle a ranar 16th ga watan Maris bayan kwashe wata daya a asibiti.
Da farko an yi masa magani kan wasu kwayoyin cuta da suka shiga jikinsa amma daga bisani kuma aka yi masa tiyata a zuciya saboda wata dadaddiyar cutar da yake da.
Mahaifin na Yariman Wales ya rasu ne watanni biyu kacal kafin ya cika shekari 100 da haihuwa.
Ya kwashe mafi yawanci lokuttan kullen Corona tare da sarauniya a gidan Sarautar na Winsor Castle.

Da yake mayar da martani game da rasuwarsa, Faraministan Burtaniya Boris Johnson ya ce Duke na Edinburgh ya yi gidan sarauta da kuma tsarin sarautar jagora, abin da ya taimaka masa ya kasanci muhimmi ga rayuwar alummar a kasar.
Ya ce Yarima Philip ya samu ƙauna daga al'umma na zamani daban-daban duka a cikin kasar ta Birtaniya da kuma kasashen da Ingila ta mallaka, kuma ya kasance wani ginshikin na goyon bayan da'iman ga Sarauniya Elizabeth an mulkinta a kullum duk tsawon mulkinta.
Shi kuwa jagoran jam'iyyar adawa ta Labour Keir Starmer cewa ya yi Burtaniya ta yi rashin wani jami'in da ba kasafai ake samu irinsa ba, wanda ya sadaukar da ransa ga kasar.
A yau Juma'a ne Fadar Masarautar Birtaniya ta Buckingham ta sanar da mutuwar Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila.
Yarima Philip ya mutu ne yana da shekara 99 a duniya.
A wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: "Cikin tsananin jimami Mai martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da mutuwar mijinta abin ƙaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburgh.
"Mai martaba ya mutu a wannan safiyar a Fadar Windsor."
Wannan shafi ne da zai dinga kawo muku rahotanni kai tsaye na yadda ake jimamin mutuwar mijin Sarauniyar Ingila Yarima Philip.
