Hotunan yadda ake makokin mutuwar Yarima Philip a Burtaniya

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, PA Media


Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Reuters
A wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: "Cikin tsananin jimami Mai martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da mutuwar mijinta abin ƙaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburgh.
Buhari Muhammad Fagge, Halima Umar Saleh, Badariyya Tijjani Kalarawi and Umaymah Sani Abdulmumin

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, PA Media


Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Nijar Bazoum Mohamed ya aike wa sarauniyar Ingila da iyalan masarautar da sauran al'ummar Burtaniya sakon ta'aziyarsa. Shugaban ya yi musu ta'aziyar ce a wani sakon tuwita da ya wallafa a shafinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaban Zambia Edgar Lungu ya aike sakon ta'aziyarsa ga Sarauniya Elizabeth II wanda mijinta Yarima Philip ya rasu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Yariman Edinburgh ya kasance mai tafiya da zamani, wanda ya gamsu da irin rawar da kimiyya da fasaha kan taka wajen inganta rayuwa
Ra'ayinsa ya yi daidai da na Yarima Albert wanda sha'awarsa game da abubuwan da juyin juyaya halin masana'antu ya kawo, ya sa shi kirkirar Babban Baje-koli, wanda ba a taba yin irinsa ba, a 1851.
Yarima Philip ya kasance mai karfin zuciya tamkar Yarima Albert, wanda hakan ne ya sa ya kasa jurewa 'yan gargajiyar da koyaushe suke son a tsaya a kan gargajiya kuma suke zarginsa da daga kai.
Yarima Philip mutum ne wanda ya yarda da yin abu kai tsaye, hakan kuma ya bayyana a lokacin yake yake-yake, musamman ma lokacin da abokan gaba suka lalata jirgin yakinsu mai suna HMS Wallace a lokacin yana matsayin laftanal na soji.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike saƙon ta'aziyarsa zuwa ga sarauniyar Ingila bisa mutuwar mijinta Yarima Philip wanda ya rasu yana da shekaru 99.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu, Shugaban ya ce mutuwar Duke din Edinburgh ta kasance tamkar ƙarshen rayuwa.
Yana mai cewa; Yarima Philip na daga cikin manyan mutane masu daraja a duniya wanda gudunmawar da ya bai wa ƙasashen reinon Ingila za a jima ba a manta ba.
Sannan sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ba da gudunmawa a fanin ayyukan taimako, kare dabobbi da ci gaban matasa a ƙasashe sama da 130 da ke duniya.
Shugaba Buhari ya ce kasancewar marigayin miji ga sarauniya na tsawon shekaru 73, ya kafa tarihi a fanin zamantakewar aure a matakin ƙololuwa.
Sannan Buharin ya mika ta'aziya ga gwamnatin Burtaniya da mambobin ƙungiyar ƙasashen reinon Ingila a bisa wannan babban rashi a masarautar Buckingham.


Asalin hoton, EPA

Tsohon Firamistan Burtaniya, Gordon Brown, ya aike da sakon tuwita yana bayyana alhinin rasuwar Yarima Philip.
"Duk ƴan ƙasa na cikin baƙin ciki da mutuwar HRH Duke din Edinburgh kuma suna mika sakon ta'aziyarsu zuwa ga sarauniya a wannan rana. Muna aike ta'aziyarmu zuwa ga sarauniya da sauran iyalan masarautar."

Asalin hoton, PA Media
Ga shi sirikin sarki, mijin sarauniya kuma baban sarkin gobe, amma duk da haka, Maji Dadin Edinburgh ba shi da wani aiki a hukumance.
Aurensa da sarauniya ya kara masa martaba da samar masa mafaka irin ta siyasa da kwanciyar hankali da kuma nutsuwa, kamar yadda auren ya tabbatar da kasancewarsa cikin hidimtawa matarsa, yana biye da ita, duk inda ta sa kafa ta dauke, nan zai jefa tasa.
An taba tambayarsa dangane da gudummawarsa ga Burtaniya, sai ya kada baki cikin salonsa na ba da amsa kai-tsaye ya ce 'na yi iya kokarina. Wasu mutanen sun yi sam-barka, yayin da wasu kuma sukan yi akasin hakan. Yaya mutum zai yi? Wannan wani salo ne na rayuwata wanda ba zan iya sauyawa ba. Wani abu ne da ba yadda mutum ya iya da shi.
Yin waiwaye a kan kuruciyarsa zai taimaka wajen fahimtar wane ne shi. Philip shi ne da daya tilo ga Yarima Andrew na kasar Girika da gimbiya Alice ta Battenberg.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mutuwar Yarima Philip babban rashi ne ga ƙasashen renon Ingila da ma duniya baki ɗaya.
A wata sanarwa da ya fitar yana mai cewa marigayin mutumin kirki ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyawawan ayyuka.
Sannna ya shaida haduwarsu da yariman a shekara ta 2003 a wani taron ƙasashen reinon Ingila da aka gudanar a 2003 a Abuja, lokacin mulkin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo.
Atiku ya ce ayyukansa na soji, da irin gwagwaraya da taimakawa sarauniya Elizabeth II, ba abu ne da za a taɓa mantawa ba domin ya nuna biyayya da sadaukarwa.
Sanarwar a ƙarshe ta ce a Madadin Atikun da iyalansa da kuma magoya bayansa, yana mika sakon ta'aziya ga masarautar Burtaniya da addu'a babban rashin da aka yi na Duke din Edinburgh.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙararrawar ankararwa ta Westminister Abbey za ta ƙada suk bayan minti guda, har sau 99, daga 6 na yamma agogon ƙasar domin aihinin mutuwar Yarima Philip.
Yarima Philip, wanda ya mutu yana da shekara 99, yana da ɗaɗɗaɗiyar alaka da Abbey, inda ya auri sarauniyar a ranar 20 ga watan Nuwamba 1947.
A shekarar 2017 ya ziyarci wurin na ƙarshe, lokacin da yi wa sarauniyar rakiya a taron ƙasashen reinon Ingila.

Asalin hoton, Reuters
An sauke tutoci a gine-ginen gwamnati yayin da ake cikin jimami da makokin mutuwar Yarima Philip.
Tutocin za su cigaba da zama a haka har zuwa lokacin da za a yi jana'izarsa.
Firai minista Narendra Modi, ya ce ya na taya al'ummar Birtaniya da masauratar alhinin rashin da aka yi. Ya kara da cewa ''Yariman ya rike mukami mai girma a rundunar sojin kasar, sannan ya na sahun gaba a dukkan ayyukan da suka shafi al'ummarsa.''
Firai minista Jacinda Arden ta ce:''A madadin daukacin al'ummar New Zealand da gwamnati, muna mika sakon ta'aziyya ga Sarauniya Izabel da iyalan masarautar Birtaniya baki daya.''
Firai minista Robert Abela ''Muna alhinin rasuwar Yarima Philip, wanda ya dauki Malta tamkar gida, ya na kuma yawan kawo mana ziyara. Al'umar mu ba za su taba mantawa da wannan lokaci ba."
Sarki Philippe ya aikawa sarauniya Izabel sakon ta'aziyya na musamman, ya kuma ce ya na fatan nan ba da jimawaba idan hali ya yi zai yi magana da ita kai tsaye.
Tsohon shugaban Amurka George W Bush ya jinjinawa marigayi Yarima Philip, inda ya ce ''ya yi tsahon rai mai albarka'' ya kuma sadaukar da rayuwarsa dan ci gaban al'ummarsa.
Masarautar Netherlands ta ce za ta tuna da Yarima Philip da girmamawa, tare da cewa ya sadaukar da rayuwarsa domin sauke nauyin al'ummar Birtaniya da ya rataya a wuyansa. Yanayin yadda ya ke gudanar da rayuwarsa abin burgewa ne.''
Sarki Carl Gustaf ya ce Yarima Philip aminin kwarai ne na iyalan gidanmu tsahon shekaru, dangantakar da muke matukar mutuntawa".
Mai magana da yawun fadar, Swedish Margareta Thorgren, ta shaida wa BBC cewa danganta tsakanin sarkin Sweden da yariman ta fara ne a lokacin da suka kewaya Birtaniya a cikin jirgin ruwa.
Ta kara da cewa; ''Wannan ne ya bude hanyar alaka kyakkyawar tsakanin mutanen biyu.''
Firai minista Scott Morrison ya ce marigayi yarima Philip ya dade ya na taimakawa sarauniya Izabel a fannoni da dama, sannan ya agazawa gwamman kungiyoyi na Australia.
Shima tsohon shugaban kasar,Julia Gillard, ya ce ''ya yin da Yariman ya kasance jajirtacce a fannin aikinsa, ya kuma zamo mutum mai yawan farin ciki.''

Sakonnin ta'aziyya na ci gaba da kwarara daga sassa daban-daban na duniya zuwa cikin Burtaniya daga ko ina a duniya.
Tsohon Shugaban Amurka George Walker Bush ya ce yariman ya yi rayuwa mai tsawo ta a zo a gani, inda ya sadaukar da rayuwar ga abubuwa masu muhimmanci da kuma ga kyautata wasu.
Faraministan India Narendra Modi ya yaba wa Yarima Philiph kan irin rawar ganin da ya taka a aikin soji da kuma gudummuwar da ya bai wa al'umma.
Firaministan Canada Justin Trudeau ya bayyana Duke na Edinburh a zaman mutum mai aƙida da kuma tsayawa kan manufa.
Yayin da Faraministan Australia Scott Morrisson ya ce marigayin ya nuna halin mutanen wani zamani da ba za a sake gani ba.
Shi kuwa Faraministan Israila Benjamin Natanyahu ya kira Duka na Edinburgh da wani ƙwararren mai yi wa al'umma hidima.