Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tura jirage don nemo ƴan matan Jangebe

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Halima Umar Saleh

  1. 'Yan daba sun ƙona ofishin 'yan sanda a Jihar Imo

    Ofishin 'yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu tsageru sun ƙone ofishin 'yan sanda na Aboh Mbaise da ke Jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.

    'Yan bindigar sun cinna wa caji ofis ɗin wuta ne a jiya Alhamis ta hanyar wurga abubuwan fashewa cikinsa.

    Kakakin 'yan sandan jihar, Orlando Ikeoku, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun yi musayar wuta da maharan kafin daga baya su tsere.

    Rahotanni sun ce ba a daɗe da sake gina ofishin ba biyo bayan cinna masa wuta da aka yi a loƙacin zanga-zangar EnSARS a shekarar da ta gabata.

    Ya ƙara da cewa duk da babu wanda ya rasa ransa amma wani ɗan sanda ya ji rauni.

    Ranar Laraba ma wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda huɗu a wani wurin binciken ababen hawa a kusa da Calabar, babban birnin Jihar Cross River da ke kudancin ƙasar.

    Kazalika, maharan sun sace makaman jami'an tsaron.

  2. Iyayen ɗaliban da aka sace a makarantar Jangebe sun bi sawun yaransu cikin daji

    'Yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, AFP

    Iyaye da kuma 'yan uwan ɗaliban da aka sace a makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara sun bi sawun 'yan bindigar cikin daji.

    Wasu daga cikin iyayen sun shaida wa BBC Hausa cewa sun yanke shawarar bin sawun yaran nasu ne da zummar ceto su daga hannun miyagun.

    "Gaba ɗaya garin Jangebe ne muka tasan ma ɓarayin, ko mu dawo da ranmu ko a kashe mu," a cewar wani da aka sace ƙannensa biyu.

    "An ce mana an gan su ('yan bindiga) suna tafiya da yaran a cikin daji, saboda haka mutunen garin Jangebe kusan 3,000 sun fito sun ce za su bi sahunsu."

    • Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 a jihar Zamfara

    A daren Alhamis ne 'yan bindigar suka yi wa makarantar tsinke, wadda ta kwana ce.

    Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

    Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

    Har yanzu rundunar 'yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

    Garin Jangebe wanda ke cikin Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, na da nisan kilomita 89 daga Gusau babban birni jihar ta Zamfara.

  3. 'Yan sandan Najeriya sun kama mutum 48 da zargin aikata fashi

    'Yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, NG Police

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi holen mutum 48 da ta ce ta kama bisa zargin aikata laifukan da suka shafi fashi da garkuwa da mutane da laifuka ta intanet da kuma satar shanu.

    Haka nan, rundunar ta yi nasarar ƙwace bindigar AK-47 guda huɗu daga waɗanda take zargin, a cewar kakakinta Frank Mba.

    Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Abuja babban birnin ƙasar, Mista Mba ya ce an kama mutanen ne a wurare da kuma lokaci daban-daban, waɗanda suka ƙunshi maza 47 da mace guda ɗaya.

    Daga cikinsu akwai wani mai suna Aliyu Suleiman ɗan shekara 26 da kuma shugaban wata ƙungiya da ake zargi da kai hari da kuma ƙwace bindiga daga hannun wani ɗan sanda a kusa da Abuja.

    Kazalika, akwai Yusuf Abubakar wanda ya jagoranci gungun mutanen da suka yi garkuwa da wani ɗan majalisar Jihar Taraba mai suna Mohammed Bashir Bappe, a cewar Mista Mba.

    Frank Mba ya ce za a gurfanar da dukkan mutanen a gaban kotu sannan ya shawarci 'yan Najeriya da su ƙara kula da ayyuykan miyagu sakamakon sabon salon aikata laifuka da suke sake ɓullowa da su.

  4. Assalamu Alaikum

    Umar Mikail ne ke muku maraba da shigowa wannan shafi mai kawo labarai kai-tsaye.

    Za mu fi mayar da hankali a kan Najeriya da Nijar maƙotansu.