Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tura jirage don nemo ƴan matan Jangebe

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku kai tsaye na awasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu za mu kawo muku labaran wainar da za a toya a duniyar.

    Allah Ya ba mu alherinsa.

  2. Gwamnan Zamfara ya ba da umarnin rufe makarantun kwana na jihar

    Bello Matawalle

    Asalin hoton, Bello Matawalle Twitter

    Gwamnan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana sakamakon sace ɗalibai ƴanmata sama da 300 da aka yi a makarantar sakandaren Jangebe a daren Juma'a.

    A wani jawabi da ya gabatar wa al'ummar jihar ranar Juma'a da yamma, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tabbatar da isasshen tsaro a dukkan makarantun jihar.

    Ba a san ranar da za a sake buɗe makarantun ba.

    Gwamna ya yi kira da a kwantar da hankali tare da cewa ana ƙoƙarin ceto ƴan matan da aka sace ɗin.

    Tuni rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta bazama neman ƴan matan.

  3. ‘Yan Algeria sun hallara don gudanar da gagarumar zanga-zangar ƙin jinin gwamnati

    Algeria protest

    Asalin hoton, EPA

    Dubban masu zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati ne suka hallara a Algiers babban birnin kasar, inda suka tattaru a tsakiyar birnin.

    Taruwar na nuni da sake dawowar zanga-zangar mak-mako da suka saba yi a duk ranar Juma’a, da aka dakatar shekara daya da ta gabata saboda annobar cutar korona.

    Zanga-zangar kan titin ace ta yi sanadiyyar sauka daga mulkin Shugaba Abdulaziz Bouteflika a shekarar 2019.

    An ci gaba da yin ta yayin da masu zanga-zanga suka kara yin matsin lambar kakkabe sauran wasu abubuwan da gwamnatin ta bari.

  4. Amurka ta ce Yariman Saudiyya ne ya ba da umarnin kashe Jamal Khashoggi

    Jamal Khashoggi

    Asalin hoton, EPA

    Wani rahoto da Amurka ta saki kan bayanan sirrin da ta tattara kan kisan ɗan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi, ya nuna cewa Yariman ƙasar mai jiran gado Mohammed bin Salman ya amince da wani shiri na kashe ɗan jaridar.

    An kashe Mista Khashoggi a 2018 a ofishin jakandancin Saudiyya a birnin Santambul.

    Rahoton ya ce Yariman na ɗaukar Mista Khashoggi a matsayin barazana, inda ya goyi bayan a ɗauki ko da mummunan mataki ne domin rufe bakinsa.

    Mista Biden na buƙatar masu kare haƙƙin bil adama da su taka muhimmiyar rawa a dangantakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya, kuma ɗaya daga cikin rawar ita ce fallasa wannan rahoton sirrin.

  5. Da gaske DSS ta kama Sunday Igboho?

    Sunday Igboho

    Asalin hoton, Sunday Igboho Facebook

    Wasu rahotanni sun ce an samu ƴar hatsaniya a lokacin da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya DSS suka yi ƙoƙarin kama mai fafutikar kare haƙƙin Yarabawan nan Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho.

    Jami'an sun tare shi ne a babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan a ranar Juma'a, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ganin shugaban ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo.

    Mai taimaka wa Mista Sunday kan harkar watsa labarai ya shaida wa sashen BBC Pidogin cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana, "inda wata tawagar jami'an tsaro suka dakatar da su tare da tambayar ko Sunday na cikin motar, to a lokacin ne hatsaniyar ta kaure."

    Ya ce a cikin jami'an tsaron akwai na hukumar DSS da kuma sojoji amma ba su san dalilin tsare su suna neman Igbohon ba.

    A cikin wani bidiyo da ya yaɗu an ga Igboho matasa na zagaye da shi, sannan ana iya ganin ababen hawan jami'an tsaro

    Sai dai hukumar DSS ta ce ba ta yi ƙoƙarin kama Sunday Igboho a Ibadan ba yau.

    A wata sanarwa da mai magana da aywun hukumar Peter Afunanya ya sanya wa hannu ya ce labarin cewa DSS ta yi ƙoƙarin kama Mista Sunday labarin ƙarya ne, kuma kar al'umma su yarda da shi.

  6. Shugabannin Oman da Qatar sun yi murnar nasarar tiyatar da aka yi wa Yariman Saudiyya

    Yariman Saudiyya

    Asalin hoton, AFP

    Shugabannin kasashen Oman da Qatar sun aike da sakon taya murna ga Sarki Salman na Saudiyya kan nasarar aikin tiyatar da aka yi wa Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, mataimakin firimiya kuma ministan tsaro.

    A sakonsa Sarki Haitan bin Tariq na kasar Oman, ya yi addu’a ga Allah madaukakin Sarki da ya albarkaci Sarkin Saudiyya da dansa Yarima mai jiran gado da koshin lafiya da tsawon rai, don cimma burin abin da ‘yan Saudiyyar ke fata ta fannin ci gaba da bunkasa.

    Haka shi ma, Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya taya Sarki Salman murnar samun nasarar aikin tiyatar da aka yi wa Yerima mai jiran gadon a nasa sakon.

    Sarkin na Qatar ya kuma aike da irin wannan sako ga Yarima mai jiran gadon Muhammad Bin Salman.

    Mukaddashin sarkin na Qatar Sheikh Abdullah bin Hamad Al Thani da kuma Firai ministan Qatar Sheikh Khalid bin Khalifa bin Abdulaziz Al Thani, su ma sun aike da nasu sakonnin tayar murnar ga Sarkin na Saudia da kuma Yerima mai jiran ga

  7. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tura jirage don nemo ƴan matan Jangebe

    Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fara aikin ceto ƴan matan makarantar sakandiren Jangebe ta jihar Zamfara da aka sace.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma’a da yamma ta ce ta tura tawagar da za ta je neman ɗaliban ta sama da ta ƙasa.

    Shugaban rundunar ƴan sandan ta ƙasa Mohammed Adamu, ya bayar da izinin amfani da jirage masu saukar ungulu biyu don gudanar da aikin.

    Wannan tawaga za ta haɗu ne da wacce dama take aiki a jihar ta Operation Puff Adder II, d ke yaƙi da masu satar mutane da fashi da makami.

    Ku karanta ƙarin bayani kan sace ƴan matan ta hanyar latsa nan.

    IG

    Asalin hoton, NG Police

  8. Biden ya yi batun kare hakkin bil adama a hirarsa da Sarki Salman na Saudiyya ta waya

    Salman da Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna ta wayar tarho da Sarki Salman na kasar Saudiyya yayin da yake neman sabunta tsohuwar dangantakar da ƙawancen da ke tsakanin kasashen.

    Ya "jaddada muhimmancin "da Amurka" take bai wa batun kare hakkin bil adama na bai daya da bin doka da oda ", in ji Fadar White House.

    Mista Biden ya yi wannan kira ne bayan karanta rahoton Amurka mai zuwa kan kisan dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Khashoggi.

    Ana sa ran rahoton zai tsunduma hannun dan sarkin, Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman dumu-dumu a batun kisan.

    Ya dai musanta cewa yana da hannu.

    Donald Trump wanda Mista wanda Mr Biden ya karbi mulki daga hannunsa, ya yi ta neman yin alakar kut-da-kut da kasar ta Saudi Arabia.

    Fadar White House ta ce Mista Biden zai "sabunta" dangantakar da kasar ta Saudiyya.

  9. Mummunan hatsarin mota ya hallaka mutum 16 a Ghana

    shugaban Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga kasar Ghana na cewa wani mummunanhatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 yayin da dama suka jikkata a kan babbar hanyar Accra zuwa Kumasi.

    Rahotanni sun ambato ‘yan sanda na cewa lamarin ya auku ne da sanyin safiyar yau, sakamakon kokarin da wasu direbobin motar safa biyu suka yi na wuce wata babbar mota ba bisa ƙa’ida ba.

    Majiyoyi da dama sun ambato ‘yan sanda na cewa hatsarin, ya faru ne da safiyar Juma’ar nan, yayin da direbobin motocin safa biyu ke yunƙurin rige-rigen wuce wata babbar motar dakon kaya.

    Ana haka ne kuma jim kadan a dai-dai mahaɗar Akim Asafo motoci biyun suka yi karo, inda nan take mutum 16 suka mutu.

    Wasu hotunan a shafukan intanet sun nuna irin yadda motocin suka yi kaca-kaca, sannan kayayyakin fasinjojin sun warwatsu a gefen titi.

    Fasinjoji da dama sun ji munanan raunuka inda aka garzaya da su zuwa asibitin gwamnati na yankin Akim Asafo.

    Rahotanni na cewa ‘yan sanda da taimakon wasu jami’an kwana-kwana suka fitar da gawarwakin waɗanda suka mutu daga cikin tarkacen motocin, inda suka kai su asibitin Akim Asafo domin gudanar da gwaje-gwaje ta yadda za a gano ‘yan uwan mamatan.

    Bayanai na cewa ana yawan samun haɗarin motoci a kasar Ghana musamman a kan wasu hanyoyi da ke haɗa sannan kasar daga Accra.

    Ko a makon jiya ma, an samu wani haɗarin mota daga Accra zuwa Cafe coast da kuma daga Tamale zuwa Yandi a arewacin Ghanar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

    Kawo yanzu dai fiye da mutum 30 ne suka mutu cikin kasa da mako biyu, sakamakon irin yadda wasu direbobin ba sa tsayawa su huta idan suna doguwar tafiya da kuma uwa uba rashin hanyoyi masu kyau.

  10. An sake buɗe Kasuwar Shasha ta jihar Oyo

    Bayan sake bude kasuwar Sasha da Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya yi a ranar Talata, harkokin kasuwanci sun fara dawo a tsakanin Yarbawa da Hausawa mazauna yankin.

    Sai dai wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun kafa sabuwar kasuwa ta Iroko nesa da birnin jihar.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko mana da wannan rahoto, ku latsa lasifikar ƙasa don sauraro:

    Bayanan sautiRahoton Umar Elleman kan sake bude Kasuwar Shasha
  11. Shugabannin 'yan adawa a Somaliya sun amince da ɗage zanga-zanga

    zanga-zanga a Somaliya

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Akwai fargabar cewa zanga-zangar ka iya janyo tashin hankali irin wanda aka yi a makon da ya gabata

    Shugabannin 'yan adawa a Somaliya sun amince da bukatar gwamnati ta ɗage zanga-zanga a birnin Mogadishu da aka shirya yi a yau Juma'a.

    Akwai fargabar cewa zanga-zangar ka iya janyo tashin hankali irin wanda aka yi a makon da ya gabata, inda aka yi musayar wuta tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro.

    Shugaba Mohammed Abdullahi Farmajo ya ƙeƙashe ƙasa cewa ba zai miƙa mulki ga gwamnatin riƙon ƙwarya ba, duk da ƙarewar wa'adin mulkinsa a farkon wannan watan.

    Yanzu haka dai an jinkirta zaben da aka saka shirya yi a kasar.

  12. Hare-haren Amurka a Syria sun kashe mayaƙan da Iran ke goyon baya 17

    Biden

    Asalin hoton, AFP

    Sojojin Amurka sun ce sun kai wasu hare-hare ta sama kan wasu wurare da sojojin sa-kai masu goyon bayan Iran suke a gabashin Syria.

    Rahotanni sun ce hare-haren da aka kai da asuba sun yi sanadiyyar mutuwar akalla sojojin mayaƙa 17 duk da cewa ƙungiyoyin sun musanta adadin wadanda aka kashe din.

    Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce hare-haren na ramuwar gayya ne ga wasu hare-haren da sojin sa-kai suka kai wa sansanonin Amurka a baya-bayan nan a Iraƙi.

    Ya ce: "Muna da yakinin cewa mun samu waɗanda muka hara. Mun san su kuma mun hakikance cewa sojojin sa-kai na Shi'a ne suka yi amfani da waɗanda muka kai wa harin wajen kai mana hare-hare."

    Amurka na kokarin tattaunawa da Iran domin ganin ƙasashen sun sake komawa yarjejeniyar nukiliya.

  13. A saka dokoki kan kuɗin intanet a Najeriya maimakon haramta shi - Osinbajo

    Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo

    Asalin hoton, @ProfOsinbajo

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce "ya kamata" Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake duba matsayinsa na haramta amfani da kuɗin intanet a ƙasar wato cryptocurrency.

    A farkon watan Fabarairu ne CBN ya haramta amfani da kuɗaɗen bisa dalilai na tsaro, yana mai cewa "ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta'addanci da kuma halasta kuɗin haramun".

    "Na gane hikimar da ta sa CBN da sauran hukumomi suka haramta kuɗin intanet, amma ina ganin ya kamata a sake dubawa," in ji Osinbajo cikin wani bidiyo da mataimakinsa kan kafafen yaɗa labarai ya wallafa.

    "Akwai rawar da dokoki za su taka a nan. Aikin hukumomi ne su sanya dokokin da za su daƙile waɗannan matsalolin ba lallai sai an salwantar da alganun da ke tattare da shi ba.

    "Nan gaba kuɗin intanet zai kawo ƙalubale game da yadda bankuna ke aiwatar da ayyukansu ta hanyar da ba mu taɓa tunani ba."

    Najeriya na sahun gaba a cikin ƙasashen da aka fi mu'amala da kuɗin intanet a faɗin duniya.

    A jiya Alhamis, masu amfani da shafukan zumunta a Najeriya suka harzuƙa sakamakon kalaman da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi cewa ba za su taɓa amicewa da kuɗin intanet ɗin ba.

    Jerin kuɗin intanet da ake kasuwanci da su

    • Bitcoin
    • Ethereum (ETH)
    • Litecoin (LTC)
    • Cardano (ADA)
    • Polkadot (DOT)
    • Bitcoin Cash (BCH)
    • Stellar (XLM)
    • Chainlink
    • Binance Coin (BNB)
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Tarzomar bayan zaɓe ta kashe mutum biyu a Nijar, an kama mutum 500

    Bayanan sautiDanna hoton sama ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce mutum biyu sun mutu sannan an kama mutum 500 biyo bayan tarzomar da ta ɓarke kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

    Kazalika, madugun adawa Hama Amadou, wanda hukumomin ƙasar suka bayar da umarnin kamawa, ya kai kansa offishin yan sanda na PJ tare da rakiyar lauyansa.

    Ministan Harkokin Cikin Gida Alkash Alhada ne ya bayyana hakan cikin wata hira da manema labarai.

    Daga cikin waɗanda aka kama ɗin akwai 'yan siyasa da kuma masu tarzoma.

  15. HRW ta zargi sojojin Kamaru da yi wa mata 20 fyaɗe da kashe mutum ɗaya

    Sojojin Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch ta zargi sojojin Kamaru da yi wa mata 20 fyaɗe ciki har da masu nakasa a yankin rainon Ingila sannan suka kashe wani matashi.

    Ƙungiyar cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Juma'a, ta ce sojojin sun aikata mummunan aikin ne a shekarar da ta gabata yayin wani samame a ƙauyen Ebam, inda 'yan tawaye ke fafutikar ɓallewa daga ƙasar.

    Sojojin sun tara maza a wuri guda sannan suka yi wa mata 20 fyaɗe, cikinsu har da guda huɗu masu lalurar nakasa, a cewar ƙungiyar bayan ta tattauna da waɗanda abin ya shafa daga watan Janairu zuwa Agusta.

    Ta ƙara da cewa sojojin sun kashe wani mai shekara 34 a dajin da ke kusa da garin.

    An ambato waɗanda suka shaida lamarin na cewa sojoji fiye da 50 ne suka afka wa garin na Ebam ranar 1 ga watan Maris, suna masu zargin mazauna yankin da bai wa 'yan tawaye masu ɗauke da makamai mafaka.

  16. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiSaurari Minti Ɗaya da BBC na Rana 26/02/2021
    • Iyaye da kuma shaidu sun ce ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata fiye da 300 daga makarantar sakandare ta GGSS Jangeɓe a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya. ‘Yan bindigar sun shiga makarantar ce a daren jiya ranar Alhamis. Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa daruruwan mutane ne suka bazama daji domin bin sawun yaran nasu, yayin da iyaye suka rika kwashe daliban da suka tsira zuwa gida tun da asubahin Juma'a.
    • Wasu hare-hare da sojojin Amurka suka kai a Syria sun yi wa kungiyoyi masu samun goyon kasar Iran luguden wuta. Fadar harkokin tsaron Amurka ta Pentagon ta ce harin, wanda shi ne na farko a karkashin gwamnatin Joe Biden, an kai shi ne a matsayin martani ga hare-haren aka kai wa dakarunta da na hadaka a kasar Iraki.
    • Ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Wacht ta zargi sojojin Kamaru da yi wa mata 20 fyaɗe a yankin rainon Ingila tare da kashe wani matashi. Ƙungiyar cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Juma'a, ta ce sojojin sun aikata mummunan aikin ne a shekarar da ta gabata yayin wani samame a ƙauyen Ebam, inda 'yan tawaye ke son ɓallewa daga ƙasar.
  17. UNICEF ya yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Jihar Zamfara

    UNICEF

    Asalin hoton, @UNICEF_Nigeria

    Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana sace ɗaliban makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara da cewa "abin ɓacin rai ne".

    Wakilin UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins, "ya kamata a ce yara na cikin aminci a makaranta da kuma gida" cikin wata sanarwa da asusun ya aike wa BBC.

    "Ranmu ya ɓaci da jin labarin mummunan harin da aka kai wa yara a makarantarsu a Najeriya," in ji shi.

    "Wannan keta haƙƙin yara ne da kuma saka su cikin tashin hankali, wanda ka iya haifar musu da matsala a tsawon rayuwarsu. Muna Allah-wadai da harin sannan muna kira ga masu garkuwa da su sake su nan take.

    "Muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbata ta ɗauki matakin ceto su cikin ƙoshin lafiya da kuma kare sauran ɗalibai a Najeriya."

    A daren Alhamis ne 'yan bindiga suka shiga makarantar sakandaren ta kwana kuma ta mata zalla da ke garin Jangebe mai nisan kilomita kusan 100 daga Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara, inda suka sace ɗaliban fiye da 300.

    Iyaye da kuma 'yan uwan ɗaliban da aka sace sun bi sawun 'yan bindigar cikin daji. "Gaba ɗaya garin Jangebe ne muka tasan ma ɓarayin, ko mu dawo da ranmu ko a kashe mu," a cewar wani da aka sace ƙannensa biyu.

  18. An kai wa ɗakin binciken cutar korona na Jami'ar Oxford hari

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ar Oxford ta ce an yi kutse a ɗaya daga cikin ɗakunan gwajin da take bincike kan cutar korona.

    Wani mai bincike kan harkokin tsaro a Birtaniya, Alex Holden, ya ce masu kutsen sun riƙa magana da Harshen Portuguese, kuma da alama sun aikata hakan ne daga Kudancin Amurka.

    Wani kakakin Jami’ar Oxford ya ce babu wasu bayanan sirri da aka yi wa kutse kuma hukumar leken asiri ta Birtaniya na kan bincike.

    Masana sun ce an samu ƙaruwar leƙen asiri ta internet da ake yi wa masana kimiyyar samar da rigakafi da kamfanonin haɗa magunguna a lokacin wannan annoba ta korona.

  19. Gwamnatin Buhari ba ta tallafa mana wurin ceto ɗaliban Kagara - Gwamnan Neja

    Abubakar Sani Bello

    Asalin hoton, @GovNiger

    Gwamnan Jihar Neja a Najeriya Abubakar Sani Bello ya koka kan abin da ya kira "rashin taimako" daga Gwamnatin Tarayya game da yunƙurin ceto ɗaliban makarantar Kagara da aka sace a jihar.

    Gwamnan ya koka cewa "babu alamun Gwamnatin Tarayya" a jihar domin ceto ɗaliban guda 27 da malamansu da ma'aikata 14 da aka sace ranar Laraba, 17 ga watan Fabarairu.

    Ya bayyana haka ne jiya Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Sanata Orji Kalu, wanda ya kai masa ziyarar jaje.

    "Ya zuwa yanzu dai, ba mu ji wata alamar Gwamnatin Tarayya ba a nan," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa: "Sufeto Janar na 'yan sanda ya turo mana tawaga huɗu ta 'yan sanda amma mu ne za mu ɗauki nauyinsu. Saboda haka ina taimakon? Babu wani taimako daga kowa.

    "E, wakilai (na Gwamnatin Tarayya) sun kawo mana ziyarar jaje, amma maganar kenan. Saboda haka an bar mu mu kaɗai kawai."

    Ya ƙara da cewa duk da halin rashin taimakon da suke ciki, gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin ceto mutanen.

    "Mun dage wurin ceto yaran nan cikin ƙoshin lafiya ko babu taimakon kowa," a cewar gwamnan, wanda tun farko ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba.

  20. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum shida a Najeriya

    Jana'izar korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 634 da suka kamu da cutar korona ranar Alhamis.

    Kazalika, cutar ta sake kashe mutum shida, wanda jumillarsu ta zama 1,891 tun bayan ɓullar cutar a ƙasar a watan Fabarairun 2020.

    Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 22 kuma Legas ce kan gaba da mutum 259, sai Osun mai 45 da Edo mai 38 da kuma Ogun mai 35.

    Saura su ne: Abuja (33) da Anambra (26) da Imo (24) da Ondo (24) da Akwa Ibom (20) da Filato (20) da Abia (19) da Kaduna (19) da Ebonyi (17) da Borno (10) da Rivers (10) da Kano (9) da Delta (8) da Kebbi (7) da Nasarawa (4) da Oyo (3) da Enugu (2) da kuma Ekiti (2).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 154,476 ne suka kamu da cutar a Najeriya, sai kuma 131,699 da aka sallama bayan sun warke.