Ɗan Najeriya da ke jagorantar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Liberia ya yi murabus saboda rikicin zama ɗan ƙasa
Shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Liberia, Ndubusi Nwabudike ya yi murabus, a cewar gwamnatin kasar.
Dama dai ana ta ce-ce-ku-ce kan yadda ya samu shaidar zama ɗan kasar. Mista Nwabudike dan asalin Najeriya ne.
Sai dai ya dage kan cewa shi dan Liberia ne kuma ya musanta yin wani laifi, amma ya gaza tabbatar wa wani kwamiti a bara sahihancin shaidar zama ɗan Liberia da har ya samu ikon rike mukamai masu girma a kasar.
Shugaba George Weah ya amince da ajiye aikin nasa ya kuma yi masa godiya bisa hidimar da ya yi wa kasar.





