Ba za a tuhumi ɗan sandan da ake zargi da kashe Jacob Blake ba
Masu gabatar da ƙara a jihar Wisconsin da ke Amurka sun ce ba za a tuhumi ɗan sanda farar fatar nan da ake bincika kan harbin baƙar fata Jacob Blake ba, wanda aka kashe a birnin Kenosha cikin watan Agusta.
Mista Blake ya samu shanyewar jiki sanadiyyar lamarin da ya janyo rikici sosai.
Lauyan Blake ya bayyana rashin jin daɗinsa game da hukuncin, inda ya ce akwai isassun hujjoji da suka isa su sa a tuhumi ɗan sandan.
Masu gabatar da ƙara sun ce Mista Blake yana riƙe da wuƙa a lokacin arangama da ɗan sanda kuma jami'in Rusten Sheskey zai yi iƙirarin cewa ya harbe shi ne don kare kansa.
Wani bidiyo da ya ɓulla a shafukan zumunta ya nuna yadda ɗan sandan ya harbi Blake a baya sau bakwai yayin da yake komawa cikin motarsa bayan 'yan sandan sun tsayar da shi.





